*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
(Jama'a ga dama ta samu, domin wannan haxiƙar Marubuciyar nan
HAFSAT A GARKUWA wanda tayi suna a cikin littatafanta masu matuƙar daɗi da faɗakarwa wato*KUNCIN RAYUWA*
*ZAMANTAKEWA*
*GIDAN MIJINA*
*DR HISHAM*
Yanzu kuma ta taho muku da sabon novel ɗinta mai taken *TSANTSAR BUTULCI* Wanda zai zo acikin sabon shekara a farashin ₦100 kacal, game so ya tuntuɓeta a wannan number 09038178773, kada kubari a baku labari*page* 55---56
*___________*📖Dariya nayi ina kallon Adda nace, "haba ma Adda kawai don kaina nayi wanka bawai don Hammah ba, nida ko tarewa banyi ba wani rawankai wa miji zanyi? a haka ma yayan besty nane fah".
"Hmmm ke kika sani lokacin da zaki manta yayan Besty ne, ni ina wurin ne?"
Dai-dai lokacin wayata ta fara ringing, ina dubawa naga number Hammah ne, share wayan nayi har saida ta tsinke aka sake ƙira shima kaman zai tsinke tukun na ɗauka.
A hankali na ɗauki wayan nayi sallama, daga ɗayan gefen yace mun yana waje ya iso, kashe wayan nayi batare da na ce uffan ba.
Ɗaukan gyale nayi na fita xuwa inda yake, ina zuwa na buɗe mishi ƙofan inda yake batare dana sake fuskana ba na mishi sannu da zuwa.
Ƙura mun ido yayi yana kallon yanayin fuskana, hannu ya miƙo zai riƙe nawa nayi saurin janyewa na juya ina cewa, "mushiga ciki Hammah".
Har parlon na kai shi, saida naga ya nemi wuri ya zauna tukun na wuce ɗakin Adda na gaya mata Hammah yana parlor.
Tare muka shigo parlon nida Adda, ni ina riƙe da boy ɗin a hannu na, ita kuma tana bina a baya, waje ta saku ta zauna suna gaisawa, ni kuma na miƙa mishi babyn.
Da sauri ya saka hannu ya karɓi ɗan bakin shi ɗauke da murmushi, yana faɗin "masha Allah", yana cigaba da murmushin ya dinga jero addu'o'i wa babyn.
Nidai kallon shi nakeyi ina mamakin yadda yake addu'o'in cikin ƙwarewa, wato shi Hammah komai ma ya haɗa ne?.
Ɗago idon shi yana duban Adda yace, "yayah jikin ki, bawani matsalah dai ko"?
Tana sunkuyar da kanta tace, "babu komai Hammah mungode sosai".
Tana tashi ta wuce ɗakinta shi kuma ya ƙora mun ido yana tambayana, "madam akwai wani matsalah ne"?
Murguɗa baki nayi batare dana kalle shiba nace, "babu komai nikan".
Dariya yayi yace "toh zoki maida shi kizo mu wuce ko".
Miƙa hannu nayi zan ɗauki babyn yayi sauri ya ɗaura mata bunch na ƴan 200 a kan cikin babyn, kallon shi nayi ina zunɓura baki nace, "baby da mamanta sun gode".
Ina zuwa naje na ajiye babyn da kuɗin akan gadonta, Ummi tana kallona nace, "Ummi nah zamu tafi" sannan Adda Umaimah ta ɗauki kuɗin kan babyn tana, "kai Hammah ango haddah ɗawainiya daga zuwa? gaskiya mungode Riyyah kimana godiya don Allah".
Haka na musu sallama na fito, a mota na same shi yana zaune, buɗewa nayi na zauna batare dana ce mishi uffan ba.
Jan motan yayi muka kama hanya batare da yace mun uffan ba, haka muka yita tafiya shiru babu wanda ya kula wani har muka zo kwanan gidan su da yake GRA makurɗi road.
Gefen titin yaja ya tsaya, dayake layin bai cika hayani ba, shiyasa banga mota ko ɗaya ba a kan titin, da sauri na juyo na kalleshi, idona ɗauke da alaman tambaya.
Batare daya kalle niba yace, "ina alƙawarin mu"?
Juyowa nayi kaɗan na kalleshi nace, "Alƙawari kuma? Ni ae babu wani alƙawari a tsakanunmu da ya wuce ka kawo ni gidan haihuwa".
Shiru yayi kaman bazai ce komai ba, har zuwa wani lokaci sannan yace, "abinda kika ce kenan ko"?
"Hammah da gaske nifah na manta" na faɗa mishi kaman babu wani abu dana tuna.
Jawo ni yayi zuwa ƙirjinshi yana faɗin, "bari na tuna miki da alƙawarin mu" lokaci ɗaya na buɗe baki cikin razana zanyi magana, kawai naji bakinshi cikin nawa.
Duk yadda naso na ƙwaci kaina amma gaba ɗaya na kasa, saboda wani irin kiss na fitan hankali da yake mun, lokaci ɗaya naji numfashina na shirin ɗaukewa, ina jin shi sai laluɓan riga na yakeyi amma ya rasa inda zai buɗe rigan haka ya gama laluɓen shi jikin shi sai rawa yakeyi amma yakasa samun kan rigan.
Da yarasa yadda zaiyi kawai sai ya matseni da ƙarfi acikin jikinshi, yana ta ajiyan zuciya, a hankali ya sake ni ya kifa kanshi akan sitiyarin motan, duk yadda naso na mishi magana akan mu wucce gida amma nakasa saboda har lokacin jikina rawa yakeyi.
Ɗagowa yayi yana kallona batare da yace mun komai ba.
Tsarguwa nayi da kallon, na juyo na harare shi a hankali nace, "nidai kada ka ƙara mun haka, kasan ae ni matar ƙaninka ne amma kake raruma na" na faɗa raina a jagule don wani iri nakeji har zuwa lokacin.
Tada motan yayi muka wuce gida ba tare da yace mun uffan ba.
Muna isa ya juyo ya kalleni, lokacin ina ƙoƙarin buɗe marfin motan yace, "nine nake rarumar ki a matsayinki na matana amma kike cemun matar ƙani na ko"?
Kallon shi nayi kaman zan fasa ihu don ganin lokaci ɗaya duk ya koma Hamman shi na da, sunkuyar da kaina ƙasa nayi ban iya na bashi amsa ba.
"Good hakan yana da kyau, gara da kika nuna mun ni amatsayin danake a wurinki, fita kije Allah ya bada sa'a".
Yana faɗa ya maida hankalinshi yana kallon gaban motan, buɗe baki nayi zan mishi magana, amma yadaka mun wani mummunan tsawan da sai danaji hanta na yana neman kaɗawa.
Ban san lokacin da na buɗe motan na fita da gudu ba nayi cikin gidan.
Harara yabini da shi, yana cewa "inbanda yarinta har nine zata kalleni tace wai ina dadumanta"? Yaja tsaki yace "ashe mata duk halinsu ɗayane"?
Ina kallonshi nafaɗa a hankali dai-dai zai shiga side ɗin shi nace, "wallahi Hamman jarirai ba ɗaya sukeba, itama razana tayi da kai, amma idan kana son wata ina da mai hankali zan haɗaku da ita, besty nah zan baka" na juya da gudu nabi bayan Riyyah don ganin halin da take ciki.
#Vote
Comment
Share
Follow.*KUKASANCE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE* ✍🏻✍🏻✍🏻
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.