*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 51---52
*___________*📖Yana shigowa palo suka haɗu da Aunty da ta fito ɗauke da tray ɗin kayan tea ɗin Baba daga kitchen, kallon mamaki ta bishida shi tana tambayanshi.
"Kada dai yarinyar nan bata kai maka tea ɗinba"?
Cikin inda-inda yake amsa mata, "takaimun Aunty, dama tambayanta zanyi ko akwaizuma ne dama dashi nake son sha", ya faɗa yana dafa kan kujeran kusada shi.
"Bari na miƙo maka ae bamu rabuwa da zuma ko dan Baban ku da khalifah da suke son shi",ta faɗa tana ajiye tray ɗin ta wuce kitchen ɗin ta ɗebo mishi a cikin wani container mai kyau.
Karɓa yayi da sauri yana mata godiya, sannan ya wuce yafita, haryaje bakin ƙofan kaman munafuki ya juyo da sauri yana kallon ƙofan ɗakin kawai sai suka haɗa idoda Aunty, da sauri yafita bai sake juyowa ba.
Itama dariya tayi tace, "kaji dai dashi idanma matarka kabiyo na koraka ae, kayi haƙuri har akai maka ita mana".Taje ta rufe ƙofan ta shige parlon Baba tana dariya.
Kallon ta Baba yayi yana tambayan, "Lafiya ƴan mata", dariya ta cigaba dayi tana cewa."ina fa lafiya, yaran yanzu kunya ta musu ƙaranci, wai Hamman sune fah zai raina mun hankali, ya shigo inaga matat shi yake nema sai ya ganni, shine ya wayance da cewa zuma yake nema", ta faɗa tana dariya.
Shima Baban dariya yayi yana cewa, "amma kema ƴar sa ido ce, mutum da matar shi don ya miki kara ya nuna kunyan shi ae sai ki kau da ido kiyi kaman baki gani ba, toh ina kin nuna mishi matat shi"?
"haba ma na nuna mishi ita? Zuman na ɗauko na bashi, yana fita kuma na rufe ƙofan".
"Amma baki kyauta ba Fatima, ina ke yanzu wurin tsohon mijinki kika taho?toh ae shima da sai ki bashi matar shi su wuce side ɗinshi".
Hararan wasa Aunty take bin Baba da shi tace, "chabb ya zuƙe zaƙin amarcin tun a gida basu wuce na su gidan ba, gaskiya bazai yiwuba, da safe ma zan ƙara mata bayani duk yadda za ayi tafa kiyaye", ta faɗa tana matsuwa kusa da Baba.
"kudai mata kuna da matsala kawai ki bashi matar shi zaifi ganewa, bawai ace sai ta tare ba, tarewan da sai ya dawo nan da kusan wata shida".
Tana dariya tace, "kasan yaran yanzu bazasu rasa ɗan ƙananun abubuwa ba ,amma ma'in ɗin yayi hakuri sai an kaita".
Baba ma hararanta yakeyi cikin tsokana yace, "amma ƙananun ina cewa bazaki hana shi ba ko"?
"na isa na hana shi? Wannan ko na hana ae bazan san lokacin da zasu saci ido na ba, kuma ma namata lecture akan ta dinga shige mishi saboda shaƙuwa, da kuma samun fahimtan juna", ta faɗa tana matsawa kusa da Baban.
Dariya mai ɗan sauti yayi yana binta da kallo yace, "amma ƙwaƙwalwar ku mata kaɗan ne take aiki, ta yayah ma za'ace mace ta dinga shigewa namiji batare da ya aiwatar da abinda yayi niyyah ba? ae wannan mannuwan ƙara ɗaga mishi hankali zaiyi, kuma yadda nasan ɗana bazai baku sararin ja mishi rai ba,
kawao dai ki koma ki bawa ɗiyarki wani lecture akan ta dinga kulle kanta a ɗaki kawai shi zaifi sauƙi".
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.