*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
(Aunty faraa na Badariyyah fans wannan shafin nakine kyauta, domin nuna mun ƙauna da kikeyi.)
*page* 47---48
*__________*📖Inagama shafa turare na, na wuce palon domin jan kunnen da Aunty ta mun akan kada ta yadda ta jirani nazo nayi saving mijina, faɗa sosai ta mun ta wuce.
Ina shiga shima yana shigowa, lokacin Aunty da su Baba da yaran gaba ɗaya suna kan dinning, Aunty ce tacewa Hammah.
"Hamman su ka wuce palona Riyyah ta ajiye maka dinner ka a can".........ba tare da yace komai ba yayi murmushi ya wuce palon Aunty.
Nima bin bayanshi nayi kaman zanyi kuka saboda ƙasa-ƙasa Gidaɗo dariya yake mun.
Ina tsaye na ɗauki pilet na zuba mishi gudun-kurnan da ƙanshin shi lokaci guda ya cika wurin, miƙa mishi nayi zuwa gaban shi, sannan na zuba zoɓo ɗin cikin cup na ajiye mishi, kaman an dasa ni a wurin naja na tsaya.
Ni ban tafi ba shi kuma bai ci ba, ina kallonshi nace "Hammah kada yayi sanyi fah".
Ɗago idon shi yayi ya sauƙe su a kaina, bansan lokacin da baki na ya furta, "ya rabbi" da sauri na sunkuyar da nawa idon ƙasa.
Murmushi yayi sannan yace, "idon mugu ko"? Da sauri nace, "a'a kayi haƙuri ni tsoron idon kawai na keji".
"Zaki mun bayani," sannan ya kalli pilet ɗin ya ce, "baki iya sannu da zuwa ba, ballantana ki gaisheni, kuma Aunty tayiwa mijinta abinci kin ɗauko kin kawo mun".
Turo bakina gaba nayi nace, "ahhh Hammah ni nayi fah, ka tambayi Auntyn".
Zaro ido yayi yana kallo na yace, " jagwalgwalen jaririya zanci"?
Bansan na harare shi ba nace, "nifa na girma".
Jan pilet ɗin yayi yana murmushi ya fara cin abincin ba tare daya sake kallona ba, ganin haka na juya zan shige ɗakin Aunty.
Hannuna naji ya kamo ya dawo dani, ƙasa-ƙasa naji yana cemun, "haka ake kula da miji"?
Kujeran da ke kusa da shi naja na zauna da ɗayan hannun, domin yaƙi sake mun hannu na.
Ina zama ya ajiye spoon ɗin hannun shi yace, "bani zoɓon" ......zaro ido nayi ina kallon shi.
"ina wasa da ke ko?" naji ya faɗa.
Da ƙyar na ɗaga cup ɗin na kai bakinshi, yana buɗe bakin nayi sauri na rufe ido na, amma don neman fitina sqi naji yaƙi yasha.
Buɗe idona nayi ina dubanshi, Harara na yayi ganin haka da sauri na sake miƙa mishi, a haka babu yadda na iya na bashi yasha.
Yana ta murza mun hannu wanda lokaci ɗaya naji hannayenmu suna zufa, amma bai fasa murzawa ba yana cin abincin shi hankali kwance.
Yana gamawa nayi saurin miƙewa zan kwashe kwanikan, ƙura mun ido yayi da sauri na koma na zauna.
Dai-dai lokacin wayanshi ta farq ringing, ɗauka yayi naji yana, "hello aboki yaya kake"? Yana wani ɓata rai naji yace, "kamai da ni irin kane? Yayah zanyi da jaririya Baba ya maƙala mun ya haɗani da raino".
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.