14-15

1.5K 72 0
                                    

[11/1, 00:53] Bestie Sady: *BADARIYA*


☄®
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin riban duniya da kuma lahira.}

        🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇

Story and written
           By
*AUNTY NICE* 😘

*WANNAN LITTAFI GABA ƊAƳAN SHI SADAUKARWA NE GAREKI MISS ZERKS, ALHERI ALLAH YA KAI MIKI*

{ *MUM SAYYEED WANNAN SHAFIN NAKINE, AUNTY NICE NAJIN DAƊIN YABAWAN KI, ALLAH YA BAR ƘAUNA*}

*PAGE* 1⃣5⃣

   

Da safe Yaya Kamal ya tafi Abuja,mu kuma bamu tafi ba sai da yamma, Mummy ce da Adda Umaimah suka mai da mu.

A kwana a tashi babu wuya a wurin ubangiji, yau saura kwana uku mu fara weac, gaba ɗaya hankalinmu ba a kwance yake ba, hatta Trouble da bata da burin cigaba da karatu, itama ta dage, duk da a lokacin har ankawo sadakinta, muna gamawa za'ayi aurenta.

Yauce ranan da zamuyi final paper mu na NECO domin tunin mun gama WEAC, ranan murna kaman zai mana yaya,bayan munfito daga Hall ne muka ɗunguma Hostel.

Allah sarki sabo turken wawa, wato wasu an rabu dasu kenan har abada, wata kuma baka san ta ina zaku haɗu ba?, abin tausayi dayawa sai kuka akeyi.

Akwai wasu suna SS 2 class, ana ƙiransu,
Umma Saleh Jos
Lami Garba (Pulako)
Azumi Tanko Bauchi
Tine Turaki,
Ranan nayi kukan rabuwa dasu, wanda har gobe idan na tuna su nakanji wani iri, gara Tine Turaki ina haɗuwa dasu, amma saauran har yau, duk inda suke ina musu fatan alkhairi.

Driver ne yazo ɗaukan mu, ido na yadawo kaman jan gauta haka muka shiga motan muna jin wani iri a ran mu.

Muna tsayawa na wuce gidan mu, Ummi ce ta tsaya kallona wani iri, can tace "Ke kuma me ya faru naga idonki wani iri?, bakida lafiyane?".

Hawaye naji ya zubo mun, sannn na ƙarasa kusa da ita nace" Ummi na mundawo".  Idona yana kan zubar da hawayen,tsaki tayi tace "amma kinji haushi wallahi, keda zakiyi murna kingama lafiya, sannan kiyi fatan sakamako mai kyau, amma sai kina kuka".

"Ummi wasu ƙawayenmu fa an rabu kenan har abada".shine kawai nake kuka sabon da akayi.

Abba ne ya fito daga ɗakin shi yace "Fatima an dawo lafiya?". Sannan ya dubi Ummi yace "haba ae sabo ake kokawa ba mutuwa ba, yanzu rayuwa da sukayi ɗaki ɗaya, wurin karatu tare, wurin cin abinci tare, lokaci ɗaya a rabu ae ko zaka koka mana".

Haka dai Abbah nah yayi ta rarrashi na, har na shiga nayi wanka, nazo na sake gaishe su, kallon Ummi nayi nace "Ummi ina Hammah Sadiq?".

"Yana school, tun last week ya tafi shida Bappah". cigaba da hiranmu mukayi.

Satin mu ɗaya da dawowa aka saka date ɗin auren su Adda, nan da sati shidda, a nan muka samu labarin Hammah Haidar ya turo an nema mishi izinin zuwa wurin Besty.

A ɗayan gefen ma, Daddy ya nemawa YayaKamal auren Fauzy kuma an bashi, Mummy babu yaddah ta iya, haka tayi ta lallaɓin Yayah,  ƙaarshe yace mataa shi ni yakeso, hankalin ta ya tashi, domin tasan Baba ya nema wa Babagana aure nah a wurin Bappah daga can kafi, kuma ance mishi an bashi.

Da wannan dalilin ta kwantar wa Yayah Kamal da hankali, sannaan ta nuna mishi babu komai ya nemi Fauzyn ita ma ba laifi, gashi ta samu tarbiya, a haka rai babu daɗi ya koma Abuja ba tare da yaje inda Fauzyn ta ke ba.

Da dare muna palon Abba muna cin abinci muna kallo, daga ni sai Ummi nah da Abba nah.

Hammah Haidar ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, bayan sun gaisaa ne, Ummi tace na kawo mishi abinci, da sauri yace "abarshi kawai ya ƙoshi".

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now