89-90

1.6K 85 21
                                    

*BADARIYYAH*
*1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira._ }

    🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇🏻

Story and written
          By
*_AUNTY NICE_*

*_WANNAN BOOK ƊIN SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*

~Whatpad@GaskiyaWritersAsso.~

*_HUSSAIN 80K, BAKI BAZAI IYA FAƊIN ALKHAIRINKA BA, NAGODE DA SHAWARWARINKA GARENI, WANNAN SHAFI NAKA NE ƘAKINA, AUNTY NICE NA JINJINA MAKA_*


*page* 89--90

*___________* 📖Ranan nayi kwanan baƙin cikin da ban taɓa yin shi ba, nayi kuka har sai da naji hawayena ya kafe, ga zuciyata da take mun wani irin suya kaman zata kama da wuta nake ji.

Bansan wani hali Hammah nah yake ba, amma tausayin shi da nakeji ya ninka wanda nake yiwa kaina, ina jin kiran sallan asubah na tashi da ƙyar naje nayi wanka na ɗauro alwalah, raka'atul fajir nayi, sannan na bishi da aallan asubah, ina zaune ina azkhar naji an buɗe ƙofan ɗakin.

Da ƙyar na ɗaga idona da suka mun nauyi na dubi bakin ƙofan, bansan lokacin dana miƙe da hanzari ba na tsaya na ƙura mishi ido, domin sai da naji wani yankewar zuciya kaman kaina zai fashe naji, domin ba idon Hammah ba hatta fuskan shi a kunbure suke.

Da gudu na ƙarasa na faɗa jikin shi ina kuka nace, "Hammah nah me ya sami fuskan ka? Wani ya dake ka ne Hammah nah?" na ƙara ƙanƙameshi ina fashewa da kuka.

Bai iya ya rungumeni ba yadda ni na mishi, kawai jin muryan shi nayi yace, "Baby ina so ki rufa mun asiri kada wani daga cikin frirnds ɗinki ko ƴan uwanki ya fahimci halin da muke ciki, ki daure idan zakuyi waliman nan kada ki bada ƙofan da wani zai fahimci wani abu kinji my dear!" ya faɗa yana ɗaga ni daga jikinshi.

Kallon shi nakeyi duk hankalina a tashe da yanayin shi, ban iya buɗe baki nayi magana ba saidai ɗaga mishi kai danayi alaman naji, murmushin ƙarfin hali yayi sannan ya juya ya bar ɗakin.



Hawaye naji kaman zai zubo mun amma sai nayi ƙarfin halin mai dasu, jikina a sanyaye na koma kan sallayata na cigaba da miƙawa Allah kuka na, don nasan shi kaɗai ne zai iya yaye mun damuwata.

Ina kan sallayan har ƙarfe tara na safe, duk yadda naso bacci ya ɗauke ni abun ya gagara, sai wani masifaffen ciwon kai da nakeji kaman kan zai rabe gida biyu.

ina kan jan casbi naji kiran Aunty ya shigo wayana, da sauri na ɗaga na kai kunne na ina. "Assalamu alaikum. Aunty an tashi lafiya"?

cikin nuna kulawa ta amsa mun da lafiya sannan take ce mun na tashi nayi wanka yandu mai mun make-up tana hanya, da kayan da zan saka gaba ɗaya, cikin nutsuwa na amsa mata.

Ina tashi nayi hanyar toilet, na fi minti ashirin ina wanka, wai duk don idona ya koma dai dai, sai wanke shi nakeyi, ina fitowa naji sallaman matar tare da Mujaheed.

Har parlour na kaisu sannan na dawo nayi sallan walaha na fita zuwa wurinta, bamufi minti arba'in ba ta gama mun kwalliyata ba mai yawa ba, amma nayi kyau, gashi abinda nake tsoron bai faru ba, domin idona yayi kyau yayihaske kaman banyi kuka ba kwanan jiya gaba ɗaya.

Wani dogon riga ta saka mun na material piech sannan ta ɗaura mun Laffaya akai, nayi masifar kyau sai ƙanshin matan borna kawai nakeyi, a haka ta fito dani har waje, mota muka shiga sai gidan su Hammah, wanda duk hankalina yana kan ko zan ganshi amma shiru.

Muna isa naga canofy har uku, kuma kowanne cike    yake da mutane daga ƴan office ɗinsu har ƴan kafin-madaki, Alƙaleri, Jama'are duk suna cike a wurin, ga ƙawayena maƙil a wajen har da su Ai Troble da take riƙe da ɗanta ɗan wajen six month.

Har wajen zamana Aunty ta kaini, lokacin kuma malama Juwairah ta fara buɗe taro da addu'a, sannan ta cigaba da sauƙe mana wa'azi mai taɓa zuciya.

Duk nasihanta akan biyayyan aure ne, da kuma kyautatawa ƴan'uwan miji, especially akan iyayen miji, kaman daga sama sai ga Hajiya Mama tinkis-tinkis ta shigo cikin fili kai tsaye wurin malamar ta wuce.

Karɓan micraphone tayi a wurin malamar, dai-dai malamar tana cewa, "toh jama'a ga mahaifiyar ango ko zata mana wani ɗan nasiha ne, toh Mama bismillah", ta faɗa tana miƙa mata.


Karɓa Mama tayi sannan tayi gyaran muryah ta fara faɗin, "Toh jama'a kundai ji abinda Malama tace ni mahaifiyar ango ce, toh Alhamdulillahi haka maganar take nice nan wacce ta haifeshi ta kuma fi kowa sanin ciwon shi da darajan shi, toh naji tana bayani akan biyayyan aure da kuma kyautatawa iyayen miji, wanda shine dadalin abinda ya tasoni na fito don nayi magana," sai tuja ta dubi inda nake, ta cigaba dacewa.

"Toh ƴan mata ko nace amaryah, naji daɗin yadda kina wurin kikaji ance ayi biyayyah wa miji da iyayenshi, wanda abin baƙin cikin shi ɗana bai dace da mace mai tarbiya ba da kamun kai, don da ina damuwan na haɗa zuriya da masu shegen asiri da mugun kissa ashe duk abin ya wuce nan, abin baƙin ciki jiya bayan an kai amaryah bai daɗe ba sai naji wayan ɗana ango, bayan na ɗauka sai naji shi yana ta kuka yana cemun shikan an cuce shi ashe matar da aka liƙa mishi yayi biyayyah ya karɓa sauran wani ne, don shidai bata kawo mishi budurci gidan shi ba, da ƙyar na hana shi sakinta a daren jiyan nace ya bari yau yazo iyaye suyi zama akanshi, idan kuma baku yadda ba ku shiga side ɗinshi na gidan nan ku duba shi, tun asuba yazo yake ta mun kuka, da ƙyar na lallaɓa shi ya shiga ya kwanta, toh jama'a ku tayi ni roƙon uwar goyonta data karyah asirin da tayiwa mahaifin yaron idon shi ya rufe ya haɗa wannan auren da ya raba baki alaikum, ko kuma na kai kara ga hukuma don a raba ɗana da raƙai".

Juyowa tayi kan Aunty tana riƙe da abin maganan ta cigaba da faɗin, "na haɗaki da Allah ki raba ɗana da muguwar ƴarki mai mugun ɗabi'a, ɗana yana da matar shi ƴar asali masu tarbiya da arziki bama su kwaɗayin abin duniya ba" ta faɗa tana kuka.

Da ƙyar nake jan numfashi na don lokaci ɗaya naji ta mun ƙaranci, ina cikin haka naga Aunty ta taso ta riƙo ni na miƙe tsaye, sannan ta dubi Mama tace, "idan ɗanki wani abu ne kije kijiƙa shi ki shanye, insha Allahu Riyyah tabar zuriyar ki har abada, shi kuma idan ɗan halak ne acikin ki ki saka shi yazo ya sake ta", sannan taja hannuna muka shige cikin gidan muka bar jama'a da suke ta hayyah hayyah.

Mama tana juya wa fuskanta ɗauke da murmushi kawai taji sauƙan mari a fuskarta, da sauri ta ɗago kanta kawai saitayi arba da Ummanta gefenta kuma Aunty Fannah ce itama ranta a ɓace, Ummah na kallonta tace.


"idan Umar ya saki Fatima, ke kuma kije na yafeki duniya da lahira, kuma nono na da kika sha ban yafe miki ba" sannan ta juya ta fita a gidan Aunty Fannanh na binta a baya.

Hammah nagani kan varandan su ya ƙura wa su Mama ido, sai hawaye ne yake zubo mishi, da kyar ya ɗaga ƙafan shi yabi bayan su Ummah.




#Vote
Comment
Share.

*KU KASANCE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE* ✍🏻✍🏻✍🏻

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now