48-49

1.3K 77 5
                                    

*BADARIYA*
*1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_

       🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_

Story and written
           By
*AUNTY NICE*

*_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*

~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~

(*_MAMAN ABDOUL NA GROUP ƊINA MUYI NISHAƊI, WANNAN PAGE NAKI NE, NAGODE DA KULAWANKI*_)

*page*  49---50

*___________*📖 Ƙura mishi ido nayi zuciyata kaman zata faɗo tsabar razanan da nayi, shima kallo na yakeyi idon shi duk ya canja kala, haka zalika Mama bata fasa buga ƙofan ba.

A hankali ya tashi ya zaunar dani akan kujera, ya ɗauka hijab ɗina ya warr mun ya miƙo mun, nidai kallon shi kawai nakeyi cike da tashin hankali.

Ƙofan ya nufa zai buɗe da sauri na bishi da ido bansan me nakeyi ba kawai naji ni nayi nilldown, hawaye yana ta bin fuskana.

Buɗe ƙofan yayi, kaman an jeho ta kawai sai ganin Mama nayi ta shigo palon bayan ta bangaje shi gefe guda, tsayawa tayi tana kallona, ni kuma sai ji nayi na ƙara sautin kukana, tana harara na tace.

"me kikeyi anan tuɓ ɗazu"?......... Bansan lokacin da naji bakina yana furta,
"Hammah ne na kawo mishi tea ya sakani nilldown".

Dariya Mama tayi tana kallon na tace, "ya mun dai-dai ae, wato ku mayun mazaje, matar shi nacan kwance ke kuma kin ɗebo ƙafa kaman na Ruƙayyan Bangies kin taho wurin miji ko? wato kinga abinda uwarki takeyi kema zaki ɗauka ko? Toh wannan kam ba shanyayye bane kaman ubanshi, ɗana kam namijin gaske ne gara ki sarara mishi, kinji ko bakiji ba"? Ta faɗa tana zaro mun ido.

Da sauri na ɗaga kaina alaman naji abinda tace, tana harara na tace tashi ki bani wuri ki wuce, da shegen tea ɗinku da bansan abinda kuke sakawa ba a ciki na jaraba.

Nazo bakin ƙofan zan wuce amma Hammah ya tare bakin ƙofan ya ƙura mun ido, da kyar na ratsa ta gefen shi na wuce, ina fita naji kuka ya zo mun, ni narasa me nayi wa wannnan matar ta tsaneni.

Ina shiga palo na samu Aunty suna zaune tare dasu Gidaɗo, ko tsayawa banyiba na wuce ɗakinta na kwanta ina kuka.

Dafa ni Aunty tayi tana "me kuna ya faru Riyyah"?  Ina kan kuka na mata bayanin abinda ya faru.

Murmushi tayi tace mun, "kin ban kunya Riyyah, tun daga yanzu har kin fara nuna ragwantanki a fili? Toh gara ma kiyi ɗamara sosai don ban goyi bayanki akan kibari a samu ƙofan tozartaki ba, bance ki raina ta ko matar shi ba, amma babu kukan da zaki sakeyi a kowaye a cikin su, Umar mijinkine bawai farkan ki bane, haka zalika ganinki yayi yace yana so bawai manna mishi ke akayi ba, saboda haka ko da wasa kada na sake ganin kin zubar da hawayenki, da ga yau kuma zaki fara ɗanmarar yaƙin karɓan ƴancinki cikin ruwan sanyi kinji ko"?

Kallon Aunty nakeyi yadda ta zauna take ta mun bayanin yadda zanyi da uwar miji na mu zauna lafiya, ba tare da na sake nuna gazawa naba ko nuna karayana, kuma ba tare dana raina taba.

A can palon Hammah kuma ina fita Hammah ya dube ta yace,

"Mama yanzu tsakani da Allah hakan yayi dai-dai ace kin biyo surakarki har ɗakin mijinta? Don Allah Mama kidinga kwantar da hankalinki akan wannan al'amari, nima fah bawai son yarinyar nan nakeyi ba,kina gani babu yadda na iya ne na karɓi aurenta don kada na kasa farantawa Baba ranshi, ko kina so idan kin matsa ne nima na mutu yadda Babagana ya tafi ya barmu"?

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now