*BADARIYYAH*
*1441H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira._ }🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇🏻Story and written
By
*_AUNTY NICE_**_WANNAN BOOK ƊIN SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Whatpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 87--88
*_____________*📖A hankali na raba jikina da na shi, ina share hawayen daya zubu mun, shi kuma ya ƙura mun ido yana ta kallona, can yace.
"Baby ina so ki tare kwanan nan", ya faɗa murya ƙasa-ƙasa, kallon shi nayi a tsorace nace, "Hammah sai nagama school ae", harara na yayi ya juya zai fita yana, "kima fara shiri zan yi magana da Aunty".
Har ya daɗe da fita ban iya taɓuka komai ba, duk hankalina saida ya tashi, ni yaya zanyi da Mama ne kam, zama a matsayin surkuwarta ma kaɗai fitina da damuwa ne.
Da daddare muna zaune a parlor muna kallon tarkon ƙauna Hammah ya shigo, bayan sun gaisa da Aunty shima ya maida kanshi kan TV yana kallon.
Muna gamawa yadawo da hankalin shi kan Aunty, ganin haka ta dubi su Khalifah tace subata wuri, ganin zasu tashi ya saka nima miƙewa zan bar wurin, da sauri Hammah yace ni na dawo na zauna.
Duk jikina rawa yakeyi domin bansan me zai ce ba, wurin yayi shiru kaman babu wanda zaiyi magana, sai zuwa can ya fara magana.
"Aunty dama maganan tarewar Fatima nake son sanin yaushe aka tsayar?" sauƙe idona nayi da sauri akan Aunty kaman zanyi kuka ina kallonta, itama kaman ta san ita nake kallo, ta kallo inda nake da saurinta, sannan ta maida kallonta kan Hammah tana ce mishi.
"Hamman su gaskiya ta wurinmu bamu wani tsayar da lokaci ba,don munfi so muji daga gareka tukun, saboda bamu san yayah shirinka yake ba", ta faɗa tana sauƙe idonta a kaina.
Shima cikin nutsuwa yace," Aunty indai shiri ta wurina ne babu matsala, don gaskiya ni nafi son ta tare nan da two weeks, don gidan da zata zauna ya riga da yaza ma ready,shiga ne kawai zasuyi, zan barsu dukkansu anan kowa tana da side ɗinta, amma a Abujazan tafida mace ɗaya, zasuna canji, kaman idan ɗaya ta zo a hutu ɗaya sai tazo daga baya".
Ɗan murmushi Aunty tayi sannan tace hakan ma yayi daidai, amma maganan sati biyu bazance maka ehh ko a'a ba,domin akwai wanda zanyi shawara da su tukunnah ko"? Ta faɗa tana kallonshi.
Bayan 2dys aka tsayar da rana ƙarshen wata, bayan mun gama exams da 1wk, yanzu sauran sati uku kenan.
Haka akayita shiri domin ban fi kwana biyu ba, Baba ya zo ya ɗauke ni akan muje can gida hakanan tukun, muna can Aunty ta ƙaro mun da kayan gyaran jiki masu kyau, haka akayita gurzaki da kayan gyaran, ga kuma haɗin su riɗi da Ummu take bani nasha da nonon raƙumi, ga wataran za ayina kankana da mazarƙwailah. Kai abin dai yayi babu magana sai ido.
Tunda aka fara maganan tarewa nah Mama ta ɗaga hankalinta ta ɗaga hankalin ƴan gidan, ga gefe ɗaya Zainab ma Mama ta zugata itama ta ɓigyare da nata rashin mutuncin, don ana sauran 1week ma ta bar bauchi zuwa maiduguri.
Tana zuwa Mamanta ta tisa ta agaba da kwana biyu suka wuce Dubai, don tace duk laifin Maman Hammah Umar ne, da tana ji tana gani ta bari aka yiwa ƴar ta kishiya, don baƙin cikin ita an mata shiyasa ta saka ɗanta yayi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.