*BADARIYA*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin rubantar duniya da kuma lahira.}🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇Story and written
By
*AUNTY NICE*😘Wattpad@GaskiyaWritersAsso.
*WANNAN LITTAFI SADAUKARWA NE GA MISS XERKS*
*PAGE* 19
Wannan shafin nabaki shi kyauta *MUMMY* *NA UMMU ASMA'U NOVEL* Allah yabar zumunci.
*___________* 📖Juyawa nayi ina kallin Gidaɗo da yake mani dariya, hararan shi nayi nace "Bakana mun dariya ba kasani tare zamu haɗa komai inji Aunty, ehhhe yaro garama ka kwana da sanin haka", na juya nayi hanyar ɗaki ban saurari dariyan dayake ta mun ba.
Tunda Asuba da nayi sallah ban koma bacci ba, kitchen na shiga na fara haɗa break-fast, alale mai ɗauke da hanta nayi wa Mama, sannan na soya doya da ƙwai na gida, nazo nayi peppesoup ɗin kayan ciki.
Nasan kullum Aunty sai tayi Tea mai kayan ƙamshi, nima ban fasa ba na haɗa hadda shi, sannan na haɗawa Mama kunun alkama.
Bayan naga komai ya kammalu na juya na harari Gidaɗo nace, "sai kaje ka kwanta ae, don duk wanda ya ganka zaiyi tunanin wani abun kirki kake tayani, bayan daga fere doya babu abinda kamun," harara na shima yayi sannan yace, "yarinya ki maida hankalinki fah! bani na tayaki ƙulla alalen ba?" sannan ya ɗauki cooler ya zuba alale guda uku a ciki ya ɗaura a saman fridge, yana hararah na yace, "idan ban adana ba nasani ba zaki ajiye mun ba, bayan na gama shan wahalan yinshi" ya juya ya fita yana mun dariya.
Ɗakin Aunty naje gyara na haɗa turaren wuta ta kowa wuri, daga palor, ɗaki, toilet duk na zuba, idan kaji side ɗin Aunty yadda ya kama ƙamshin turaren borno, ko side ɗin Mama ba yayi.
Wanka na shiga nayi, sannan nayiwa Mujaheed muna shiryawa wurin ƙarfe 8:00 saiga Aunty ta shigo ɗakin.
Da murna Mujah yaje ya rungumeta, ina tahowa wurinta na gaisheta, "Ƴan mata na duk ke kikayi wannan aikin? Gaskiya Babagana zai more da mace mai ƙoƙari ga tsabta," ta faɗa tana duba na da dariya a fuskanta.
Nima dariyan nayi nace, "Aunty yayah jikin Maman? Da sauƙi ta amsa rana ƙarasa bakin gadon, sannan tace, "mai tayata wunin ae har tazo shiyasa na taho, idan yaso keda su Gidaɗo kwaje anjuma ku gaisheta, don na bawa driver abincinta ya tafi mata dashi".
Tana gama faɗi ta wuce toilet don yin wanka, bayan ta fito ne ta samu har na wuce ɗayan ɗakin, zama tayi ta shiryah kaman wata ƴan mata, gown ta saka na wani material, sannan ta fito zuwa dinning.
Muna zaune a dinning sai ga Baba dasu Hammah sun shigo, hannun Abdallah ɗauke da Nabil, wuri kowan su ya zauna, mu kumaa muka gaishe da Baba dasu Hammah.
Aunty ce ta karɓi Nabeel tana tambayan Hammah " ina Maman shi kuma, ko bata tashi bane" bayan ya gaisheta ne yake cemata, "ae bata ma san gari ya waye ba, wanka ma Abdurrahman ne ya mishi".
"Gajjiya ne ya ke damun ta", inji Aunty da ta maida hankalinta kan cin abincinta, kowa ma shiru yayi yana cin abinci.
Baba ne ya tashi yana kallon su Abdallah da su Gidaɗo yace, "Boys ku tashi muje mu duba Maman ku ko"? Duk kansu suka bishi, daga ni sai Aunty da Hammah aka bari a palon.
Aunty ce ta dube ni tace, "Riyyah ki ɗauki doyan ki kaiwa Zainab side ɗin Mama kada ta tashi bata san a nan yake ba"! "Babu inda za a kai mata Aunty, matar da bata san ta tashi ta girka bane za a bata? ae yadda ta nuna mun ban isa da ita ba akn uwata wallahi zata gane ƙuranta, tamanta ko bata aure ni ba Mama ae uwartace" ya faɗa kaman zai yi yayah don haushi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.