*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 45---46
*____________*📖Ina shiga palon Mama na hango Hammah zaune a gefenta yana ta daddanna wayanshi, ita kuma sai masifah take ta zubawa, abin mamaki kaman ba da shi ta keyu ba, gefe ɗaya kuma Zainab ce rungume da Nabeel akan cinyanta sai juka take tayi kaman an aiko mata da mutuwar iyayenta gaba ɗaya.
"shin Umar bada kai nake magana bane? Don tsaban raini ka rike waya kaman mahaukaciya ce tsaye akan ka?"
Ɗagowa yayi yana duban Mama amma abin mamaki idon shi kaman wanda ya shekara yana kuka babu rarrashi, tsabar irin jan da sukayi, buɗan bakinshi yayi da ƙyar yace.
"Mama toh naga kinsani agaba kina ta zagina kaman wanda aka zo akace miki nayi kisan kai ko kuma na aikata shirka, abin takaicin ma agaban wannan yarinyar da ta saka mutane agaba tana ta shirme, kaman wanda aka mata albishir da shiga wutan jahanna ma".
Ya faɗa yana hararan Zainab.
Mama kallon banza ta mishi kaman ta tsinka mishi mari tace,
"Toh meye maraba da kisan kan? Wannna ae kaman ka kasheta da ranta ne Umaru, ballantana ni da na tsuguna na haife ka amma ka watsa mun ƙasa a ido na,
Toh bari kaji idan har ni na haife ka ban yadda ba kuma ban amince ba ka zauna da auren wannan shegeyar baƙar yarinyar, yau ɗin nan kuma yanzun nan nake so ka saketa, ko kuma na tsameka acikin ƴaƴa na" ta faɗa kaman ta tsinka mishi mari.
Kallon idon shi nayi lokaci ɗaya naji gaba ɗaya na tsorata, domin a sani na Hammah Umar manyan ido gareshi, amma abin mamaki idon a buɗe suke amma tsabar ɓacin rai kaman a rufe suke duk sun ƙanƙance wuri guda.
"Mama duk abinda kike so shi zanyi, amma kuma dole ne itama Zainab na gutsire igiyan aure na da ita na kuma yafe mata ɗan data haifah, don ni ma bazan riƙe shi a matsayin ɗa ba,
Mama zan miki biyayyah amma bazai saka na ƙiyiwa mahaifina ba, domin shi ma yana da hakki akaina, don wannan auren nima ba'a son raina nayi shiba, amma saboda kwanciyar hankalin Baba yasa nayi,
Kinga Zainab ma saboda ke nayi saboda haka duk zan iya rabuwa da kowansu, akan na ɓata miki kona ɓata wa Baba".
"Nikan my honey bance dole ka saki matar ka ba, ko nace maka na shiryah rabuwa da kai ne?" Zainab na kuka take faɗin haka, sannan ta juya ta kalli Mama tace.
"Nikan don Allah Mama idan ma don nine kike cewa ya sake, toh gara ma ki bari, don ni kan ban shiryah rasa mijina ba, saidai ki gaya mishi nikan kada ya yadda ya haɗa mu gida ɗaya da ita, don ni gaskiya bazan iya jure ganin yarinya ƙarama ƴar talakawa tana zaune da mijina ba, kuma ta ishe mu da warin miyar daddawa, kuma Mama ki gaya mishi kada ma ya fara haɗa matsayina da nata kawai shine damuwa na"
Hammah hararan ta yayi cikin tsawa kaman zai tashi ya daketa yace,
"Kada ki ƙara saka bakinki kina faɗun duk abinda yazo miki, dan mahaifiyata tana mun magana, kema har wani matsayu kike tunanin kina da shi? Ballantana ita ma yarinya ƙarama wanda bata wuce raino ba".
Ba Zainab da ɗanta da ya fashe da kuka ba, hattah Mama sai da taji ta razana da tsawan shi.
Kallon Zainab da take ta kuka Mama tayi, sannan taja bakinta tayi shiru domin tana da tabbacin ba karamin halin Umar bane ya sauwaƙawa Zainab idan ta sake maganan ya sake ni, tunanin haka da Mama tayi ya saka ta harari Hammah tace.
"Toh uban kowa tunda ka gama kafa mana dokokin naka sai ka tashi ka fita kabani wuri, don yanzu na yadda kai ne Fatima da zuriyarta suka mallake ba Babagana na ba, domin Shi kan kullum cikin lallaɓa ni ya keyi ba irinka ba," lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka tana cewa,
"lallai da gaske nayi rashin ɗana wanda yafi kowa sona a cikin ku, kaidai kawai Allah ya saka mun sonka ne fiye da kowa a acikin su, amma kai kuma kafi kowa ƙin jin magana na, yanxu kam na yadda da maganan Babanah ashe shiɗin mai tsananin ƙauna ne, Allah dai ya jiƙanshi da rahma" ta faɗa tana ta sharen hawayenta.
Tashi Hammah yayi yakama hanyan fita, da sauri Zainab tabi bayan shi da kallo tana share idon ta, sannan ta dawo da kallonta kan Mama tace.
"Don Allah Mama kibar shi da maganan sakin yariyar nan kada nima ya sake ni, jinga wallahi ina son mijina" ta faɗa tana ƙara share hawayenta.
"hmmm, ki barni da shi Zainab insha Allahu ko ba yanzu ba na miki alƙawarin sai ya sake ta, don ni ko kaɗan na tsani zuriyar Fatima, ballantana kuma har aure ya haɗamu da su"
Mama ta faɗa tana jijjiga kanta.
Tunda akayi sallan la'asar Aunty dole ta sakani na shiga kitchen domin nayiwa Hammah girki, ina kallonta nace.
"Aunty toh aini ban san me yake son ci ba?" dariya Aunty tayi sannan tace,
"Hamman ku yawanci abincin gargajiya yafiso, saboda haka sai ki fara duty daga yau, kisan me yaka mata kimishi, ni dai abu ɗaya zan gaya miki shine kullum dare yana shan tea kafin ya kwanta" ta na faɗin haka ta juya tayi hanyan ɗakinta.
Raina duk a jagule natsaya tunanin me zan dafah mishi, can a raina nace bari na mishi gudun kurna ae shima abincin gargajiyane, kuma abincin sarakai ne, don shima bai wuce sarkin ba yanayin shi da tsarin shi, na faɗa ina duba abinda zanyi amfani dasu a kitchen ɗin.
Zoɓo na fara haɗawa wanda yaji kayan ƙamshi zallah ban saka na zamani ba, ina gamawa na saka shi a fridge.
Kaza na ɗauka guda biyu na gyara su na ɗaura su akan wuta bayan na zuba wadataccen albasa da kayan ƙanshi.
Kafin a ƙira sallan magrib na haɗa gudun kurna na, wanda yaji naman kaza da yagama rugurgujewa a ciki, daga kofan palon Baba dake side ɗin Aunty zaka fara jin ƙamshin girki na.
Gidaɗo ne ya leƙo wanda ya yi shirin tafiya mosque yana ta gyara hannun rigan shi da yayi alwala yana cewa "kaaiiii yau zan kwashi gara a gidan nan, lallai na iya zaƙulo Mata inaga abokaina zan gayyato su suzo cin dinner yau a gidannan", ya faɗa ya nabuɗe coolers ɗin dana ke zubawa a lokacin.
Buge hannun shi nayi ina cewa, "kaji rainin sence abincin Hamman ne kake cewa zaka kira friends ɗinka suzo suci? Har ma kake iya saka ƙazamin hannunka kana buɗe mun girki"? Na faɗa ina ƙara make hannun shi daya sake miƙowa zai buɗe yana dariya nah.
Muryan Baba naji yana cewa, "Rabu da shi Fatima zai haɗu da Sojan Hamman shi yau, don nima yanzu dana hango fuskanshi ne yasaka ni canja hanya na dawo sai ya wuce nima na wuce, don naga yau amazan faman yake," ya faɗa shima yana buɗe abincin sannan yace ," uhmmmm gaskiya ƙamshin ne ya jawo ni nima, yakamata a zuba mun nawa ni kaɗai kafin sojan nan ya shigo mukasa zama a palon," yana dariya yake faɗa.
Duk kanmu dariya mukayi don jin abinda Baba yake faɗi, kaman shiɗin ma yana ƙasa da Hamman ne.
Basu suka shigo ba sai da akayi sallan ishaa, lokacin nima na fito a wanka na saka wani Dogon riga Mai irin roban nan, sannan na yafa wani Ƙaramin gyale akai na.
*Don Allah kumun hakuri zuwa dare zakuji ni insha Allahu da wani page ɗin, domin nayi baƙi ne yanzun nan*
*DAN ALLAH KARKU MANTA DA VOTING*
#Vote, Comment, Share, Follow.
*DAGA ALƘAMIN AUNTY NICE* ✍🏻✍🏻✍🏻
VOCÊ ESTÁ LENDO
BADARIYYA Completed {03/2020}.
DiversosLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.