9-13

2.9K 99 0
                                    

[10/29, 16:09] Anty Nice: *BADARIYA*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya d'aya ce daga kinta sai b'ata, burinmu mu fadakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

       🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN KARFE* 🏇

Story and written
           By
*AUNTY NICE* 😘

*PAGE* 9⃣

    Duk abinda sukeyi idon Hammah nakansu, baza a jima ba sai kaji yayi tsaki shi kad'ai shi.

MC ne yayi sanarwan ana so aga dangin ango a fili, kafin kace wani abu sai ga Family an fito filin rawa, harda cousins d'insu y'an jama'are, zuka ga zuk'a-zuk'an kyawawan mata a familyn, ba jama'are ba, ba Maiduguri ba.

Besty ne yace "kutashi muje fili".

kallon shi nayi nace "Nikan bana rawa besty".
Sai naji yace  ehh ko bakya yi fito muje kiyi mun liki".Besty Feenah ke kam zamuyi rawa ko?"  Tana dariya tace rawa kai besty, sanann ta mik'e tana kallona.

Babu yadda na'iya na mik'e, shi kuma ya bud'e purse d'in hannu na ya zuba mun kudin liki a ciki, sannan muka wuce filin rawan.

Wata cousin d'in suce tazo kusa da Besty tana wani rawa a gaban shi tana zolayan shi kanin ango, amana lik'i, tana nan kaman zata b'alle don sirintaka, yake kawai yamata ya shareta, haka ta cigaba da rawanta, shi kuma yafara bin bayan besty suna rawa.
A haka suna rawa nafara mishi lik'i face d'ina d'auke da smiling, shima haka ya zuba mun ido kaman zai janyeni ya keji, abun sha'awan kuma ina lik'i amma bansan ina juya jikina ba a hankali kaman ina rawan y'an shuwaa, Wanda ya burge mutane dayawa a wurin.

Duk inda nayi idon Aunty nah dasu Ummah na kaina, Aunty nah fuskarta d'auke da murmushi, ita kuma Goggon Bauchi zuciyarta yana mata fari duk lokacin data ganni, a ranta tace Allah yasa burinta ya cika, mu had'a kanmu da HAIDAR.

Da sauri Gidado yazo yana ta d'aukan mu photo da wayanshi, itama Aunty Fanna haka kawai taji ranta na kauna na, kuma haka kawai take jin dad'in a ranta na alaman da take gani kaman d'an ta m sona yakeyi, da  sauri ta tashi tazo tana mana lik'i, ko takan sauran bata bi ba, hankalinta yana kaina da besty, ganin haka yasa Auntyn mu ma fitowa tana mana lik'i babu k'ak'kautawa, gaba d'aya sai filin ya kachame, kud'in hannu nane ya kare, najuya zan koma na zauna, charaff sai naji hannun besty ya rik'o nawa, zuciya na naji ya yanke amma shi ko a jikin shi, sai murmushi dayake mun, tsorona kada mutane su ganmu, amma dana ga kowa hidimanshi yakeyi babu Wanda ya lura damu, sai mutsu-mutsu nakeyi akan ya sakeni amma fir yak'i.

Kaman ance na daga kaina na dubi Hammah Umar, sai ganin wani banzan kallo yake mun kaman idon shi zasu fad'o k'asa, bansan wani irin k'arfi bane yazo mun, a d'ari na k'wace hannu na, na juya wurin zaman mu kaman zan fad'i k'asa, numfashi na da sauri yake tahowa.

Besty ce ta biyoni inda nake sai haki takeyi, tana murna tace "Besty kid'an yamun dad'i, kaman kada a daina".

   Hammah Umar yayi tsaki yafi sau ba iyaka, har saida Zainab ta maida hankali kan shi tace "Honey me ya faru?".

Ko kallonta bai yiba shid'ai kawai ji yakeyi kaman ya tashi ya bar taron, a zuciyan shi yana fad'in.

"in banda sakarci, ina Babagana ina mace  at this age? Yaron da ko karatu baigama ba, meyake nufi?".

Mtsss ya sake Jan tsaki.

Da sauri Yusuf ya juyo ya kalle shi, yana mamakin dalilin d'aure fuskan abokinshin, shida ake auren shi ae ya kamata yafi kowa farin ciki a wurin.
Amma saboda sanin halin abokin shi sai baiche komai ba, ya maida hankalin shi inda y'an matan keta rawa, yana harin wacce zai zab'a shidai yana son fara mai tsayin gashi.

Ba' a tashi taron ba har wurin karfe 11:00 sannan aka koma gida, kowa jikinshi ya gajji, banda bacci babu abinda nake so, a haka mukayi wanka babu wani hira kowa ta nemi wurin kwanciya ta kwanta, Aunty ne kawai da Goggon Bauchi suke taba hiransu.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now