24

1K 72 5
                                    

*BADARIYA*



☄®
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da kuma lahira.}

 
🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇

Story and written
          By
*AUNTY NICE* 😘

*WANNAN LITTAFI SADAUKAR NE GAREKI MISS XERKS*

*{Ina Gwanar wasu don ni ga tawa Gwanar, Alal haƙiƙa INAWURO, Gaskiya Writers wannan shafin kyauta Aunty Nice ta baki domin jin daɗin irin comment ɗinki, kisani kina cikin ran Aunty Nice dare da rana*}

*PAGE* 24



*___________*📖 Bayan mun fito daga lectures ne Mummy ta ƙira wayan Besty take cemata, "Auta an turo daga gidan su Haidar ranan Friday zasu kawo kayanki fa" Mummy ta faɗa tana dariya.

Bestyn ma dariyan takamayi tana, "kai Mummy ai nasani, tun last week ya gaya mun shine nace ya bari sai ranan Friday, idan yaso saturday sai mu shigo mugani".

Nidai kallon Besty kawai nake ina mamakinta, bayan sun gama wayan ne ta juya tana kallona tace,

"Besty ran Friday fa zasu kai kaya, mukuma saturday sai mu shiga ko?"

"Duk yadda kikace Hakima haka za'ayi"

na faɗa ina dubanta sai wani kauɗi ta keyi tana ta waƙoƙinta.


Ranan Saturday muka shiga gari babu inda muka tsaya sai gidansu Besty, gudu-gudu muka shiga gidan a palo muka haɗu da Mummy zata fita.

Kallonta Besty ta keyi tace,  "Mummy ina zakije kuma? bayan munzo."

"Zanje mu duba Umaimah ne ɗazu wai suka dawo a asibiti, yanzu zamuje nida Ummin ku, ku shiga kawai sai mun dawo ku sai kuje".

Tana fita muka rufe ƙofan gida muka wuce ɗakin Mummy, muna shiga mukaci karo da akwatuna set biyu, ɗaya pink ɗaya kuma wani orange mai kyaun gaske.

Kallon Besty nayi saboda mamakinta nakeyi, duk colours ɗin jakakkunan da take so nagani a kwance, ita kaɗanta ta kwashe da dariya tace, "I Luv U Hammah my Luv".

Ƙiran wayan shi tayi muna buɗe kayan, duk abinda ya mata kyau sai ta bashi labarin abun, nidai sai mamakin shi nakeyi, don jin irin dariyan  da yakeyi kaman bashiba,  ita kuma sai kwaɗa shi takeyi na irin ƙoƙarin daya yi kaman wata tsohuwar mata, shi kuma sai wani wage baki yakeyi.

Nidai rabuwa nayi da ita kawai nake ta kallon kayan, jakan kayan bacci muka buɗe, abin mamaki kawai sai naji muryan Besty tana cewa,

"My luv kaga wannan red nighty dana tura maka? Kaga kyaun da yayi kuwa?"  ta faɗa tana wani rawan jin daɗi.

Biyeta kawai yakeyi suna zuba chaftan su.

Muna gama gani muka hau gadon Mummy muna ta bayanin yadda kayan yayi kyau, Besty tana ta faɗa mun irin ɗinkunan da zamuyi.

Kallona nayi tace, "Besty yanzu yaushe kukayi za'a kawo naki saboda 3month kaman yau ne, gara mu fara maganan ɗinkuna"

Muna cikin hiranmu mukaji tsayuwar motan Mummy, da sauri muka fito Besty ta buɗe ƙofan muka tarye su, Ummi ce a bayan Mummy suka shigo palon.

Hira akayi akan ciwon Adda Umaimah, Mummy tana cewa,

"harda raki fa a ciwon Umaima, don wallahi halinsu ɗaya da Addan su Humairah wurin raki".

Saida akayi sallan magarib tukun nida Ummi muka wuce gidanmu, inda muka samu Hammah Walid da Hammah Bappah sunzo ga Hammah Sadiq ma, gaba ɗaya sai naji daɗi a raina domin rabon danaga Hammah Walid na daɗe.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now