26

1.1K 96 4
                                    

*typing✍🏻°•°*

*BADARIYA*



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da kuma lahira.}_

    🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE*_ 🏇

Story and written
           By
*AUNTY NICE* 😘

_*WANNAN LITTAFI GABA ƊAYA SADAUKARWA NE WA MISS XERKS.*_


*PAGE* 26--27




*__________📖*  Tunda garin Allah ya waye Mama take ta musu hali amma daga Aunty Fannah har Baba babu wanda ya kula ta, gara ma Aunty Falmata tace,

"Yaya abinda kike mana fa tun zuwan mu jiya kinga babu dole ni sai nai wucewata , dama lagos zanje duba kaya na da suka iso, saboda kai kayan nan ne yasa ka na haƙura, amma tun jiya sai gaya mana magana kikeyi, gaskiya ni babu dole a wurina idan baki bar ɗan naki yayi aure da wanda yake so ba, ke zaki zauna da shi?"

ta faɗa tana hararan Mama.

Umma ce ta dube su tace, "kada na sake jin muryan ɗaya daga cikin ku idan ba alkhairi zaku faɗa ba".

ta juya ta cigaba da wuridinta inda Nabeel da yake kwance kan cinyar Aunty Fannah.

Aunty tun wurin ƙarfe takwas na safe ta taho gidanmu domin su haɗu akan aikin taryen baƙin, duk da komai ma sun bayar ne ayi musu, samosa ne da cake Besty da Adda Umaima da Aunty Ladidi sukeyi a gidan su Besty, wanda nima tun safe na shiga gidan.

Ƙarfe ɗaya na azahar su Hajiya Addayo ƙanwar Baba suka iso daga Jama'are su uku, ita da babbar ƴarta da kuma wata cousin ɗinsu matar chairman ɗin jama'are, babu wani karɓa na arziki da Mama ta musu sai wani sauƙe musu baƙar magana da takeyi.

Ganin haka Baba yasaka Aunty Fannah ta rakasu side ɗin Aunty inda su Gidaɗo suke zaune shida Khalifah suna ta kallo a palon Auntyn.

Da murna Gidaɗo ya karɓe su ya wuce dasu can palon Aunty, ita kuma Aunty Fannah ta koma ta haɗo musu abinci ta kawo musu side ɗin, inda ta samu Baba yana zaune cikin su sai hira sukeyi.

yana tambayan su yaya jikin babbar Addan su wanda take fama da diabities.

Ana sallan la'asar ƴan gidan wazirin jama'are su biyu suka iso a wata arniyan mota kaman wani jirgin ƙasa, sai sauƙe ƙamshin turare kawai sukeyi, ko gefen Mama basuje ba saboda sunyi waya da Hajiya Addayo ta gaya musu inda suke, bayan sun gama gaisuwan yaushe gamo n Aunty Fannah tace,

"su fito su wuce kai kayan"

inda babu ɓata lokaci suka wuce.

Duk yadda nayi da Besty akan mu zauna nida ita agidan amma firrr taƙi tayi wuce wanta gidanmu ita dasu Adda, babu yadda na iya dole muka cigaba da wayanmu nida Besty kaman zamu lashe junan mu don so.

Tunda aka shiga gidanmu Zainab take ta wani yatsine-yatsine irin gidan bai mata ba, babu wanda ya damu da ita, dama suma ƴan'uwan Baba ko gaishe su batayi ba haka suma ko cikanki babu wanda yace mata.

Bayan an gama buɗe kaya ne sai Aunty kece mata, "Zainab ina kika baro mana maigidan namu? Ko dan yau yaga mata iri-iri ne ya hanashi zuwa inda nake?".

Aunty ta faɗa tana dariya.

Ita dai Zainab ɗan yamutsa fuska tayi kaman mai jin warin kashi tace, "yayi bacci ne shiyasa na bar shi wurin Mama".

Ganin abinda tayi sai Hajiya Addayo tacewa Aunty, "ai kawai Fatima wannan mijin ki barshi wa Zahra, ke kuma kiyi fatan matar Babagana tana shiga ta sulluɓo mana namu maigidan wanda ya iya gaisuwa da cefane, don nasan zai iya damu dukanmu, ba irin wanan da bai iya gaisuwa bama ballantana aje ga maganan chefane ba".

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now