20

1.2K 80 4
                                    

*BADARIYA*


☄®
*GASKIYA WRITERS ASSICIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

      🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇

Story and written
          By
*AUNTY NICE* 😘

Wattpad@GaskiyaWritersAsso.


*WANNAN LITTAFI SADAUKARWA NE WA MUSS XERKS*

*PAGE* 20

*SAHIBA* ( *UMMI YAWALE BABA* ) ƴar uwata Aminiyata, wannan lshafin naki ne ke kaɗai na dadaukar miki, Alherin Allah ya isar miki.

*___________*📖 Malali shine sunan unguwan da Yusuf suke zaune da matar shi Aishatu, babu matsalah Yusuf yayi dacen mata mai kirki da sauƙin kai, gashi tana da tsaftah da sauƙin kai.

Duk da ayanzu Yusuf haɗuwar shi da Hammah yayi ƙaranci, amma basu fasa communicating ta waya ba kusan kullum, gashi Yusuf har Abujah ya kai Aisha, amma da yake Zainab bata da kirki kuma bason mutane take da shi ba, sai sabon nasu yaƙiyi yuwa, don tunda suka dawo tace, "My dear gaskiya bazamu sake zuwa wurin wannan mata mai ji da kan nan ba, don wallahi baka ga yadda ta mun ba, ko kaɗan banji daɗi ba".

Dariya Yusuf yayi yace, "kuna da matsalah ko mata wallahi, mudai ba zamu fasa zumuncin mu ba, kodai da yake kuna da jin rai sai ku haƙura", ya faɗa yana kallonta da dariya a fuskanshi.

"Haba my dear! ae bai kamata kamun wannan shaidan ba kuwa, kasan hali na
ni ban iya wulaƙanta ɗan Adam va, da mai kuɗi da talaka duk ɗaya ne a wurinah, kawai dai inaga bata samu home training bane" ta faɗa kaman zatayi kuka.

Sorry my happiness wasa nake miki, ni ko nafi kowa sanin wacece ke? nasan ba halinki bane wulaƙanci shi yasa nake ƙara sonki baby nah, ita ma idan bata gyara ba, nasan Umar zai gyarata very soon.

A haka suka dawo kaduna suka cigaba da rayuwar su, suna six month da aure cikinta ya ɗan fara fitowa, kuma a wannan lokacin Yusuf ya lura da irin cikan da Aisha ta keyi, har ga Allah yaji daɗi cikin zuciyar shi, don shima yanzu ƴar cikakkan mace tana burge shi.




Da gari ya waye Aunty bata wani jira sai Zainab tayi break-fast ba, tashin nah tayi muka shiga kitchen muka haɗa komai, daga na asibiti har na gida, kafin 7:30 mun gama komai.

Bayan driver yakai su Gidaɗo sch ne, Aunty ma tayi shirin fita office tana tsaye a dinning tana mun bayanin abinda zanyi na rana, hannun ta ɗauke da tea cup tana shanye sauran tea ɗinta, bayan mun haɗa komai na asibiti tace, "driver yana dawuwa ki bashi ya kai musu, amma kada kije kinji auta".

Amsa mata da "ehh naji" kawai nayi, muna haka sai mukaji Hammah yana sallama ya shigo.

Aunty ya gayar sannan nima na gaishe shi, Aunty ce ta nuna mishi break-fast ɗin ƴan asibiti, sannan ta nuna mishi na cikin cooler tace ya ɗiba a wurin, su Abdallah kuma nasu yana kitchen dana Baban su.

Kallon Aunty yayi yace, "Hmmm wallahi Aunty da kin barta ta haɗa musu idan yaso suga ranan ku, amma yarinya babu abinda ta iya kaman ba mace ba" ya ja tsaki ya ɗauki basket ɗaya yace, "Aunty bari na kai musu idan na dawo na karya".

Hanyar fita yayi Aunty tace, "na bishi da flask da ɗayan basket ɗin, tunda shi ya ɗauki basket ɗaya da babban flask ɗin.

Har mota naje na saka mishi, ko kallona baiyi ba ya shiga ya fita.

Aunty ma office ta wuce aka barni daga ni sai mai mata sharah da wanke-wanke, ɗaki na wuce don nayi wanka na huta.


Sai wajajen 10:00 su Abdallah suka shigo suna breakfast, inajinsu amma ban fito ba, sai can naji Abdurrahman yana mun sallama.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now