18

1.2K 75 4
                                    

*BADARIYA*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu gaɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

      🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇

Story and written
          By
*AUNTY NICE* 😘

Wattpad@GaskiyaWritersAsso.

*WANNAN LITTAFI SADAUKARWA NE GA MISS XERKS*


*PAGE* 18

Wannnan shafin sadaukar wa gareku, Masoyaana, na hannun dama nah *AISHA ALTO*& *MAI DAMBU*


__________📖Duk da hutawa nake so nayi amma zuciyata taƙi hutawa da tunani, a zuciya na ina ayya na yanzu Mummy dake da yara mata har uku, amma take cikin damuwa da tafiyan su Adda, toh Ummi nah ita yayah zatayi idan nima nayi auren?.

Sake juyawa nayi ɗayan hannu, a zuciyata ina jin ba daɗi yadda Yaya Kamal yake yiwa Fauzy, domin gaskiya idan nice ita bazan iya cigaba da son shi ba.

Toh ni ɗin meye nafi Fauzyn da zai so ni sama da ita?     Bayan ita farace gata ƴar'uwar shi, sake juyawa nayi gefe ɗaya ina jin babu daɗi a raina, saboda yadda take nuna mun tana sona.

Wayata ce ta ɗauki wani sarewan india mai daɗi, ina murmushin jin daɗi na ɗauki wayan don na san mai ƙiran.

"Hello Besty na faɗa ina tashi zaune" can ƙasa-kasa da muryah naji shi yana ce mun, "My dear nikan na gajji da rashin ganinki, nifa gaskiya zaɓ dawo ya faɗa da muryan shagwaɓa".

Ina dariyan shi saboda yadda yake ta mun shagwaɓa kaman ahine macen  nace, "haba Bestyn Beauti! yayah za'ayi ace kadawo kabar aikin da nake alfaharin miji na jarumi ne, ya tafi neman halal ɗin da zai riƙe ni, toh idan kace ka gajji, ni kuma nace meke nan?.

Shiru yayi kaman bazai ce komai ba, can kuma yace,  "Beauty nah!" sannan ya sake shiru yana sauke numfashi kaman bazai sake cewa komai ba, can kuma saaai naji ya sake ajiyan zuciya sannan yace,
"Beauty toh nikan amana auren mana don Allah, nifah gaskiya kisani ina takura sosai".

Ɓoye kaina nayi cikin bargo kaman ana gani nah,  inata dariyan shi ƙasa-ƙasa, ni wallahi mamakin Besty nakeyi na yawan shagwaɓan shin nan.

"Beauty kinyi shiru idan baki ce komai bafa zanyi kuka", ya faɗa yana wani irin murya kaman ɗan 5yrs.

Haƙuri mana Bestyn Beauty, kaga nima zaka sakani kukan kuma babu mai lallashi na, don Ummi nah ta tafi kano, na faɗa nima da muryan kukan.

"Haba Beauty kashe ni zakiyi ne?nikan gaskiya zan ƙira Baba na gaya mishi kawai a mana auren, kinsan sun bani gida mai 2 bedroom ae ya ishe mu ko?"

Haka mukayi ta hiran har zuwa bayan sallan la'asar, sannan mukayi sallama na tashi na yi wanka.

Tunda na shiga haraban gidan na haɗu da Besty zata zo nema na, hararah na take tayi tana cewa, "ke wai ina kikaje ina ta nemanki? Kinsan kuma zamuje gidan Haƙilah ko?.

Hararan ta nayi na buɗe motan bance mata komai ba na zauna, bayan munje gidan Haƙilah wuraren ƙarfe shida mukayi gidan Adda Umaimah, gaskiya gidajen amaren yayi Kyau.

Muna gidan Adda Umaimah har wurin 9:30pm, tukun ango da abokan shi sukazo, muna cikin ɗaki nida Besty Hammah Haidar ya ƙirata akan mu fito, haka muka fita ko sallama bamuyi da Addah ba.

A mota sai hiransu suke kaman zasu lashe kansu don so, har mukaje bauchi clup ya saya mana hanta, bayan mun iso nabar su a motan suna sallama, ni kuma na ɗauki ledan naman nayi cikin gida, a palo na samu Mummy zaune da wasu daga cikin dangi suna ta hira.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now