*BADARIYYAH*
*1441H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira._ }🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇🏻Story and written
By
*_AUNTY NICE_**_WANNAN BOOK ƊIN SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Whatpad@GaskiyaWritersAsso.~
*_Gaskiya writers wannan shafin kyautane na bawa duk wata member dake gidan, sannan ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman wa ɗiyata Neat lady da innaro, gaisuwan ku da bance na muku_*
*page* 91---92
*_____________*📖Duk yadda yaso ya tsayar da hawayen shi abun ya gagare shi, har inda su Ummah suke tsaye ya ƙarasa, bai iya ya furta musu komai ba sai hannun shi da yasaka ya riƙo na Ummah yana ta sheshsheƙan kuka, ɗayan hannun kuma ya rufe fuskan shi da shi.
Aunty Fannah da ta kira number driven ta akan ya fito su tafi, itama hawayen take zubarwa, haka zalika Umma ma kukan takeyi, babu wanda yace uffan har drivern ya ƙara so inda suke yayi parcking.
Aunty Fanna ce ta saka hannu ta riƙo na Umma akan su shiga mota su tafi, wanda ko kayan su ba suyi tunanin ɗauka ba, jiki na rawa Hammah ya sake damƙe hannun Umma idon shi yana kallon Aunty Fannah yana ta girgizama ta kai alaman kada su tafi.
Share hawayenta tayi ta juya wurin shi tace, "Umar kada ka hana mu tafiya, tafiyan ne kawai zai saka zuciyar mu ta sanyayah, sannan ina mai kara tabbatar maka da kada ka sake matar ka, kajira zuwan Babanka tukun duk abinda ya ce maka akai sai kayi aiki da shi, sannan ta saka hannu ta jawo na Umma suka shiga motan.
Da ƙyar yaja ƙafan shi ya koma cikin gidan, bai tsaya komai ba ya ɗauki motan shi ya fita ya bar gidan, kai tsaye gidan shi ya wuce inda kai tsaye ya wuce toilet don wani irin zafi da ɗaukewan numfashi ya keji, haka yaje ya sake ruwa mai sanyi akanshi.
Muna shiga ɗakin Aunty ta kwantar dani akan gado sannan ta juya ta rufe ɗakin ta fita, babu ɓata lokaci ta sallami dukkan bakin da ta gayyata, sai da taga kowa ta tafi gidan daga ita sai Goggon mu da Mummy tukun ta shigo ta buɗe ɗakin da nake suka shigo, kuma har zuwa lokacin da ake ƙiran sallan azahar ban bar kuka ba, ga wani numfashi na da nake ji kaman zai ɗauke.
Kowar su wuri ta samu ta zauna fuska a murtuke, Aunty naji ta fara magana tana, "Riyyah don Allah zuwa yanzu kukan naki ya isa haka, ki bar ta da sharrinta ni dai nasani kuma kema kinsani babu abinda muka koya miki sai tarbiya, saboda haka sharrinta akan ta zai tsaya".
Shiru nayi da kuka na sai ajiyan zuciya kawai da nake tayi, sannan na maida hankalina inda naji Goggo tana cewa Aunty zata wuce dani gidanta, duk wani shirgina ta aiko mun daga baya.
Mummy tana amsawa da, "wallahi wannan shawarah yayi dai-dai, kuma Abba ya kawo shawarah mai kyau, insha Allahu sai ta zubar da hawayen abinda tayiwa baiwar Allah, an gaya mata ita kaɗai ne ta fara haihuwa? Idan da badan iko na ubangiji bama da kuma kowa da irin rabonshi ae da yanzu Riyyah tana gidan Kamal inda babu wanda ya isa ya takurata ko yagaya mata banzan magana" Mummy na magana tana miƙewa ranta a matuƙar ɓace da niyyan tafiya.
Ina ji ina gani Goggo ta riƙoni muka fita, inda Aunty ke binmu a baya ranta a ɓace ko magana ba ta iyayi, har inda motar Mummy yake ta raka mu, muna shiga babu ɓata lokaci muka fita a gidan, har kofar gidan Goggon mu Mummy ta kaimu, sannan ta dubi Goggo tace.
"Goggo duk yadda Alhaji Nuhu zaiyi ya lallaɓeku kada a baru Riyyah ta koma har sai yayi kyakkyawan tsakani wa Mama da ita", Goggo na girgiza kai alaman haka za ayi sannan tace.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.