22

1.2K 67 18
                                    

*BADARIYA*


☄®
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

    🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇

Story and written
          By
*AUNTY NICE* 😘

*WANNAN LITTAFI SADAUKARWA NE GAREKI MISS XERKS*




_Haƙika anyi rashin Babban mutum, mai haƙuri, son mutane da cigabansu. *BAPPAH HAKIMI* ina ta'aziya wa masaratan Misau da dukkan legal community, Allah ya  masa Rahama ya gafarta masa zunubansa._


*PAGE* 22

*__________📖* Gaba ɗaya ji nayi ƙafana kaman baza su iya ɗauka na ba, muryan Mummy Boo naji tana ce mun,

"ki ƙara so mana, ba Yayan ki bane ba?"

Dole na jawo ƙafana na ƙaraso cikin office ɗin, har ƙasa na sunkuya na gaisheta, sannan na gaisheda Hammah Umar wanda duk naji muryana yana rawa.

Mummy Boo ce ta tashi tace, "Toh Sojaa bari na barku ku gaisa, amma kada ya wuce 30mnt, ina jiranka a wajen can"

ta fita tana cewa na zauna akan kujeran.

Juyowa yayi ya kafa mun mayun idanun shi wanda bansan lokacin da na buɗe baki na sake gaishe shi ba.

Batare da ya amsa mun ba ya jeho mun tambaya, " baki da number nane a wayanki? baki damu da kiji Yayah muke ciki ba ko?"

Jijjiga mishi kaina nayi alaman ba haka bane, harara na yayi yace, " hala bakinki yana ciwo ko?"

buɗe baki nayi nace, "bani da number ne Hammah".

Miƙo hannu yayi ya karɓi wayana ya saka number shi, sannan yace,

" daga yau ina samun ƙiran ki na gaisuwa, sannan duk wani abu da kike buƙata ban ɗauke miki ba, ki kira ki gaya mun"

shiru yayi yana ta dube-dube cikin wayan har zuwa wani lokaci sanann ya ɗago ido ya dube ni yace,

"Fatimah! Naso ace kiyi karatunki ki gama successefully kafin ki shigo da maganan aure, amma sai kika watsa mun ƙasa a ido kika biyewa wannan yaron mai rawan kan, wai kema aure kike so, bakiga kinyi ƙarama ba? Me zaki ɗauka a rayuwar aure?"

Ban iya ba shi amsa ba sai sunkuyar da kaina ƙasa da nayi ina wasa da hannu na, shima ƙura mun ido yayi wanda har jikina sai da naji yana rawa, shi ɗaya naji yayi a jiyar zuciya sannan yace,

"Fatima bana so kibiye wa soyayyah ki kasa maida hankali a karatu, don ke har yanzu bakiyi wayon da zaki fahimci so na gaskiya ba, kuma zaiyi wuya a age ɗinki ganzu ki gane menene soyayya" ,

"Amma da zaki mun alfarma ɗaya ki dakatar da maganan auren nan sai kin gama karatunki, da ni kuma zan miki alƙawarin wani muhimmin abu mai daraja a rayuwarki, wanda har ki ƙarasa rayuwarki a cikin farin-ciki"

ya faɗa yana ƙura mun ido.

Ɗaguwa nayi ina son satan kallon shi, amma cikin tsautsayi sai idon mu ya haɗu wuri guda, da sauri na sun kuyar da kaina kasa, ban iya bashi amsan komai ba.

"ki buɗe baki kimun magana, saboda akwai abu masu muhimmanci da suka sa ni shigowa cikin school ɗinku, kuma ya kamata kibani haɗin kai mutattauna kinji"

Batare dana shirya ba nasamu bakina da furta,

"amm..umm Hammah...."

sai kuma naji na kasa iya cewa komai, nidai wallahi da yasan yadda yake mun kwarjini da bai zo inda nake ba.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now