23

1K 95 4
                                    

*BADARIYA*


☄®
*GASKIYA WRITERS ASSOCIARION*✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da kuma lahira.}

    🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇

Story and written
          By
*AUNTY NICE*😘

Wattpad@GaskiyaWritersAsso.


*WANNAN LITTAFI SADAUKARWA NE GAREKI MISS XERKS*



*PAGE* 23

  
*___________*📖 Tun ranan da Hammah ya kirani bai sake ƙirana ba, amma duk da rashin kiran shi sai na maida hankali na akan karatuna, kuma kullum sau babu adadi muna waya da Besty nah.

Akwana a tashi babu wuya wurin Allah yau saura 1week mu fara jarabawa, gaba ɗaya hankalinmu ya koma kan karatu, don hatta su Hammah Haidar da Besty sun sarara mana da yawan ƙira, sudai burinsu mu fito da sakamako mai kyau.

Ranan wednesday muka gama jarabawar mu, kowanmu kagani ya faɗa saboda damuwan karatu.

Da wurin ƙarfe ɗaya drivern Mummy yazo ɗaukan mu, muna ta ɗauki da murna muka isa gida.

Ranan kam munyi barcin huce gajjiya, don nidai da ƙyar da akayi sallan la'asar na tashi nayi sallah, kuma sai zuwa lokacin naci abinci.

Bayan nagama cin abincin ina zaune a gefen Ummi na ina yanke farce take ce mun,

"Auta kinga irin kayan abincin da Yayan Babagana ya kawo mana kuwa? lokacin da zai tafi wancan ƙasan, ga kuma kuɗi har million ɗaya yabawa Abbanki yace baya so ko iyayen shi suji, wai Abbanki ya saya miki gado da shi, kai mutumin nan ɗan albarka ne sam baiyi halin uwarshi ba".

Tsayawa nayi da cin abinci ina kallon Ummin mu, fuskana ɗauke da mamaki sannan nace, "Ummi ni dama yana zuwa wurin Abba ne? Wancan karon ma kunce mun shi yayi gyaran side ɗinki".

"Zuwa kai" inji Ummi sannan ta cigaba da mun bayani,  "auta ai yafi mai neman naki zuwa gidan nan, mutumin da idan yazo sai su wuce awa biyu zuwa uku shida Abbanki, gashi duk yanda Abbanki yayi yaron nan sai ya taimaka mishi, don yanzu gaba ɗaya karatun Sadiq shi yake biya".

Ummi tana gama mun wannan bayanin ta tashi ta shige kitchen domin ɗaura abincin dare, don tace yau na huta zatayi.

Duk jikina a sanyaye dajin bayanin da Ummi ta mun, ɗaukan wayana nayi na ƙurawa number shi ido ina mamakin abinda ya hana shi ƙirana.

Can na ce, " Ummi to da yatafi kuma suna waya da Abban"?

Fitowa tayi daga kitchen ɗin hannunta ɗauke da rober ta miƙo mun kuɓewa na yanka mata, ta nemi wuri a gefe tana gyaran kifi tace mun,

"Jiya ma ai ya kira Abbanki sun daɗe suna magana, har maganan dawowan ki yau naji suna yi, ai yaron ɗan albarka ne sose"

Satinmu uku da dawowa gida hutu wanda yayi dai-dai da saura sati ɗaya mu koma school, da yamma Mummy da Adda Hummy suka shigo garin Bauchi wanda suka taho da sayayyan da sukayi na auren mu, kuma da kayan auren Yaya Kamal da aka haɗo a can.

Washe gari da safe Adda ta ƙirani akan mu harhaɗa kayan a jakakkunan su, kusan set biyu ko wanne mai biyar, wayyo kaya kam ba'a maganan yawansu da kyaunsu.

Da yake Adda Hafsat ma ta biyo su da suka sauƙa a kanon, acan kuma Adda Umaimah ma tazo, saidai tunda ta zo take kwance a ɗakin Mummy babu abinda ta ke iya tsinanawa saboda wani irin laulayi mai wahala ta keyi, Adda Hafsat ce ba za kace ma tana da wani ciki ba, kuma a lokacin ma ya kai 4month zuwa 5, amma kaman babu komai, haka mukai ta shirya kayan.

A store kuma Mummy ce da masu aiki taje nuna musu inda zasu sauƙe  namu sayayyan.

Bayan mungama saka kayan ne muna ta hiran kyan kayan saiga Yayah Kamal ya shigo palon, wanda ban taɓa tunanin yazo garin ba, ashe tare da su Mummy yazo.

Adda Hummy ce ta kalle shi tana dariya tace, "ango zo kaga irin bajintar da Mummyn ka ta maka, don alama ya nuna Mummy ashe rufah-rufah take mana, yanzu ne na fahimci tafi ƙaunar ka akan mu, don komai ta ɗaga sai tace zaiyi kyau da matar ɗana"

ta faɗa tana dariya wanda dukkansu palon dariya sukeyi.

Shima cikin takun shi na barazana ya shigo ya zauna face ɗinshi ɗauke da murmushi yana duban Mummy yace,

"Mummy ai nasan bata da wanda ya wani cikin ƴaƴanta tun ba yau ba, kallon ku kawai na keyi ana wani cewa wai Umaima da Hafsat ne gwanayenta, ni kuma nasan ba haka bane ko Mummy nah" Ya faɗa yana dafa kafaɗanta.

Dariya tayi tace, " hakane yaro na, don nafi gadara da kai, sukuma na gidan wasu ne, kai kuma da kai da matar ka da yaranka duk iko nane, sai yadda nayi da ku" ta faɗa tana buɗe mishi kayan.

Kallo yakeyi yana murmushi ya dubi Adda yace,  "kaman kinsan yanzu daga wurin Fauzy nake, tana gaya mun wai best colour ɗinta Blue ne, gashi ko duk yawancin kayan mai Blue kuka saka, nasan zataji daɗi wallahi, Adda mun goggode fa da ɗawainiya".

_Hmmm ko kallona fa baiyi ba_, na faɗa a zuciyana Lokaci guda sai naji abin bai mun daɗi ba, tashi nayi nace, "Mummy bari naje gida zan taya Ummi aiki".

"Okay Auta sannunku da aiki" Mummy ta faɗa fuskan ta ɗauke da farin ciki, haka na fita ko jiran Besty banyi ta mun rakiya ba na fita na bar gidan.

*****

Ranan saturday aka kai kayan Fauzy Alkaleri, mu kuma sunday muka koma school, duk yadda naga Yayah Kamal yana so ya ritsani sai na kauce wa wurin don bazan iya ɗaukan raini ba.

Bayan mun koma ne muna kwance nida Besty take cemun,  " ashe Besty ya tambayeki best colour ɗinki dasu size ɗinki ki kaƙi gaya mishi? amma kin ban kunya har saida ya tambayeni? Kenan inaga idan anyi auren ni zan dinga gaya mishi irin cefanen da kike so ko?" ta faɗa tana harara na.

Tashi nayi na zauna ina dubanta nace, "Besty fa bayida kunya ne, cemun fa yayi wai gaya mun size ɗin bra ɗinki dasu pant, ni kuma na kashe wayan, to ke idan Hammah ya tambayeki zaki iya faɗa mishi ne"?

Kallo na takeyi sheƙeƙe sannan tace, "na yaushe? Ni ai har mun wuce wurin domin Aunty har ta fara haɗa kayan, colours ɗin dana keso na gaya mishi, ni hatta irin night wears dana keso na tura mishi, ke har turo mun yake yi ina zaɓa".

Ta sake kallo na dana buɗe baki ina kallon ta tace, "idan ma zaki ɗame to ki ɗame, don namiji duk yadda ka mayar mishi da kanka haka zai bika, idan kika maida kanki local haka zai ɗauke ki, idan kika nuna mishi ke mace ce haka zai ɗauke ki, ni yanzu hatta kayan daya ke sakawa ni nake zaɓa mishi bari kiji bayani yarinya."

Haka na bita da kallo ina mamakin wayewa irin na Besty, tana hararana tace, "gara ma ki gyara don wannan surakarkin idan baki riƙe mijinki ba tun yanzu, zuwa zatai tana miki chefane naga alama"

Nima Aunty nice nace, " Hakane fa rayuwan da gaske, don mazan yanzu duk yadda kike haka zasu biki, Mata gara mu gyara don shi rayuwa da miji ɗan kissa ne, bawai ki cuce shi shine kissa ba, a'a wannan mugunta ne da zalunci, amma kisan right ɗinki da Kuma yadda zaki zauna dashi lafiya shawaranku ɗaya ai shine jin daɗin"





*DAN ALLAH KARKU MANTA DA DANNA VOTE.*



*KU KASANCE TARE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE A SHAFI NA GABA* ✍🏻✍🏻✍🏻
2019.

BADARIYYA Completed {03/2020}.Where stories live. Discover now