*BADARIYYAH*
*1441H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira._ }🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇🏻Story and written
By
*_AUNTY NICE_**_WANNAN BOOK ƊIN SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Whatpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 95--96
*_________*📖Suna shiga wurin Baban su suka shige, bayan sun gaisa ne dukkan su sukayi shiru kowa kanshi a sunkuye a ƙasa, har zuwa wani lokaci tukun Baba ya ɗauki wayan shi ya ƙira Hammah akan ya same su a parlour shi.
Kafin Hammah ya shigo Baba ya ƙira Aunty, tana shigowa Hammah ya shigo fuskan nan na shi a murtuƙe kaman a filin yaƙi, gashi duk ya rame kaman ba shiba.
Dukkan su gaishe da Aunty sukayi sannan parlour ya koma yayi shiru kaman babu wani halittah aciki, zuwa wani lokaci Baba yayi gyaran murya, sannan ya sanar musu abin da ya faru tsakanin shi da Mama har akaje batun saki, sannan ya sanar dasu yadda jiya sukayi da Abbah da kuma Aunty.
Baba kallon su yakeyi yana jiran abinda zasu ce, zuwa can Abdallah ya gyara zama ya fara magana kaman haka.
"Baba Allah ya ƙara maka lafiya da juriya akan iyalanka gaskiya alal haƙiƙa kai mai haƙuri ne da kuma hangen nesa, kuma kai ɗin har ilah yau mai adalcine cikin iyalanka, domin kuwa abinda ya ke faruwa tsakanin ka da Mama tun tashin mu da kai ba mai haƙuri da adalci bane da ko saki ɗari ne idan ya halattah toh da kayi, Mama mahaifiyata ce amma na sani abubuwa da yawa bata kyautawa expecially tsakaninku da abokiyar zamanta, har ilah yau ya fara dawowa kanmu ɗaya bayan ɗaya."
Ajiyan zuciya yayi tukun ya cigaba, "Baba amadadina da sauran ƴaƴanta muna mai baka haƙuri da abinda Maman mu ta maka, ko ince ta muku kaida Aunty da kuma Hamman mu gaba ɗaya".
"Domin bawai wa Riyyah kaɗai Mama ta ciwa mutunci ba, maganan gaskiya wa Baba damu kanmu ƴaƴanta ta ciwa mutunci, domin martabar gidanmu ta taɓa, Baba don Allah ba don halin Mama ba kayi haƙuri ka maidata matsayin ta na matar ka, haka kema Aunty don Allah kiyi haƙuri ki yafe mata".
Shiru wurin ya sake ɗauka babu wanda yace uffan, zuwa can kuma sai Abdoulrahman ya buɗi baki yace.
"Baba da Aunty don Allah kuyi haƙuri ku yafewa Mama," sannan ya maida kanshi gefen da Hammah yake yace, "Hammah don Allah kayi aure ka yafewa Mama, domin kaima an maka ba dai-dai ba", ya faɗa yana share hawayenshi, domin shi mai rauni ne.
Hammah dai zuwa lokacin bai ko ɗago kanshi ba.
Aunty ce ta gyara muryanta sannan ta ce, "Allah ya gafarta mana gaba ɗaya, sannan kuma nidai a gefe nah nayafe mata, amma kuma maganan data faɗa akan Riyyah shikam maganar gaskiya bazan iya cewa ya yafu ba, har sai shi ɗanta wanda yace mata Riyyah bata kai mutuncinta gidan shiba tayi proving hakan tukun zamu yafe, domin gaskiya duk abinda Mama zatayi mun taci darajan mijinta da nake aure, da kuma ku ƴaƴanta da kuke yayun nawa yaran, kuma wallahi da tasan yadda nake so mu zauna lafiya mu rungume yaranmu, da wallahi sai tafi ko wacce mace samun zaman lafiya da zuciyarta, amma kuma gaskiya bazan bari ta saka baiwar Allah a gaba ba, don bazai yiwuba".
"Toh Alhamdulillahi mungode Allah tunda kin yafe mata, sai magana na gaba shine maganan ita Riyyah, shi kuma wannan nasan matsalanku kuna tunanin Baba nane ya zo ya ɓata ta a wurin mamanshi ko? Toh wallahi sam kada ku saka a ranku, domin nayi imani da Allah koda Riyyah bata kai budurcinta gidanta ba toh Baba nah bazai tona sirrin gidan shi ba, kawai ta faɗa ne don ranku ya ɓaci, kuma yau zan ɗauki Baba nah muje har gaban Abba ya basu haƙuri, kuma tare da Mama zamuje domin ta nemi yafiyar su, Allah kuma ya magance mana wannan masifah".
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.