*BADARIYA*
*1441H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 65---66
*___________*📖Ba tare daya shigo ba ya kira wayana akan yana mota, sallama nayiwa Aunty na ɗauki kayana na fita.
Ina shiga motan naji wani kunyan shi yakama ni, kasa nayi da kaina ina faɗin, "Hammah an tashi lpy"?
Dariya kaɗan yayi bai amsa mun ba ya ja motan muka wuce, har muka isa kofan gidan bai ce mun uffanba, nima bance komai ba har muka isa.
Yana packing ya juyo ya ƙura mun ido, duk sai naji nakasa kallonshi, ƙasa nayi da idona ina wasa da zoben da yake yatsa na.
Shirun naji yana yawa a hankali na ɗago kaina na kalleshi, amma irin kallon da yake mun da sauri na maida kaina ƙasa, ba tare da abinda zan faɗa na iya faɗiba.
Riƙo hannu na yayi har lokacin bai ce komai ba, sai murza mun tafin hannu da yakeyi, lokaci ɗaya naji jikina yana ta ɗan ɓari a hankali.
Jinake kaman na buɗe ƙofan na fita da gudu, don har yanzu murza mun hannu yakeyi batare da ya ce uffanba.
Fitowan mijin Adda Umaimah ne ya dawo dashi kan hanya, ni kuma na samu saukin abinda nakeji, jiki a mace yace.
"idan anyi magarib zanzo ɗaukan ki, sannan ya buɗe ƙofan ya ƙarisa wurin mijin Addan, nima jiki a mace na fito, sama-sama na gaishe shi na wuce cikin gidan.
Ina shiga parlon na haɗu da Ummi nah ta fito daga kitchen, da sauri na ƙarisa na rungumeta, gaisheta nayi, bayan ta amsa tace mun xata tafi gida yanzu, sai yammah ta dawo, saboda mai zama da Adda yau zatazo daga Alkaleri.
Ɗakin na wuce na samu mai jego tasha gayu cikin wata super, Feenah na mata make-up, Adda Hummy na shiryah Babyn da aka saka mishi *MUHAMMAD* ina dariya na ƙarisa gefen maijego ina cewa.
"kyau kenan Adda"? ...."gaskiya Adda kinyi kyau sosai, kaman ba haihuwa kikayi ba? gaskiya ko Feenah ma dani babu abinda muka isa nuna miki", ina faɗa dukkan su suka saka dariya, Feenah tana cewa.
"gaskiya ƙawata ban yadda ba, nifa Adda Umaima 3yrs ta bani hala ma hadda watanni, kinga ko dole na fita ƙira da haɗuwa", ta faɗa tana jijjiga jiki kamar wata tarwaɗa.
Adda Hummy sai dariya take mana tana cewa, "nidai babu wadda ta kai ki a wurina kyau da haɗuwa, don duk kyaun yarinya a bayanki take baby nah"! Kowa dariya yake yi.
Wurin Azahar ƴan alkaleri duk sunzo, Aunty ladidi a gidanta akayi abinci da su coslow, da pappe chicken.
Dama Aunty ta bada aikin Cake a gidan Hajiya Addayo sister Daddy, da sauran kayan snacks, mu kuma kunun aya da kunun gyaɗa, alale, zoɓo muka haɗa nida su Adda da feenah, ana sallan Azahar mukayi wanka muka chakare, kaman wasu amare muka fito.
Da yammah *SHAGARI AUSHER* da *AHMED MISAU* sukazo sukayi ta kashe mana pics.
Gaskiya taro yayi kyau, su Aunty sai yamma suka iso, ana sallah magarib na shiga alwalah naga nayi baƙo, a zuciyata nace, "shiyasa nayita jin ciwon mara, duba pad nayi kawai nayi na saka.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.