*BADARIYA*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻
{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE* 🏇Story and written
By
*AUNTY NICE* 😘Wattpad@GaskiyaWritersAsso.
*WANNAN LITTAFI SADAUKARWA NE, GA MISS XERKS*
*PAGE* 17
Wannan shafi na baki shi kyauta *MAMAN ZAINAB* daga *ZUMUNTA NOVELLAH* inajin daɗin comment ɗinki, nagode sosai😘
Shiru Yayah Kamal yayi yana duba wayanshi, kaman baiji mai Mummy tace ba.
Besty da fuskan shi ɗauke da murmushi, ya dubi Kamal yace "Abokina barka da yau tare da miƙa mishi hannu, domin su gaisa".
Tashi Yayah Kamal yayi kaman bai ganshi ba, yayi hanyar kitchen, duk kanmu saida mukaji kaman mu nitse a ƙasa.
Abin mamaki sai Besty ya dubi Adda Umaimah, still fuskan shi ɗauke da murmushi, yace "Adda inaga wani a waje ya ɓatawa abokina raine, don muma muna da irin shi a gidanmu, ya faɗa yana dariya".
Mummy ce ta fara dariyan yaƙe tace, "shi ae haka yake, wai idan ranshi ya ɓaci sai yaƙi kula mu, yanzu hala shida wacce zai aura ce, haka yake duk ranan da ta ɓata mishi rai, sai ya ɗauka wa shi kaɗai mata sukeyi, gashi yana sonta kaman babu gobe", ta faɗa tana kallon hanyar kitchen ɗin tana dariya.
Gaba ɗayan mu, mun gane Mummy tayi haka ne don kada Besty ya ɗauka da wani abu.
Ko ya gane, ko bai gane ba, sai cewa yayi "Mummy ae haka babban yayanmu yake, idan wani ya ɓata mishi, toh duk gidan ya shafesu har abokanshi, ya faɗa yana dariya".
Dai-dai lokacin Yayah Kamal ya fito a kitchen, hannunshi riƙe da cup ɗin tea, bai kalli kowa ba yayi hanyar waje.
Babu wuya a wurin Allah, ya Mummy da Adda Hummairah suka dawo a Dubai wurin sayayyar kayan ɗakin su Adda Umaimah.
Bauchi suka taho, saboda haka ranan , Ammar kamar zamu lashe shi, daga na gudu da shi gidan mu, can zaka ga Besty taxo, hankalina na tafiya wani wuri zata ɗauke shi tayi gida.
Haka nima zan bita na mata masifah, sannan na ɗauko shi na dawo, Ummi sai masifah take mana, akaan muna wahaladda shi, ita kam Adda Hummy da Mummy ko su kula mu, sai aikin ware kayan sukeyi, wanda Aunty ma tun safe suka zo itada sister Mummy suke tayasu.
Lokacin bikin sauran 3weeks, Adda Hafsat da Adda Umaimah basu wani zama a gida kullum sai sun fita, wannan karon muma zamu haɗa musu ƙauyawa Day.
Ni FATIMA BADARIYYAH kullum mamakin soyayyar Besty da Hammah Haidar nakeyi, yau mabshi yazo ya kaimu gidan ƙawayen mu, da muke kai musu IV da kuma ashobi.
Har gidan Aisha Trouble ya kaaimu wacce take unguwar Railway bauchi, last month akayi bikin Trouble, wato muna gama school da 3weeks.
Ranan monday da muka shiga week ɗin bikin su Adda, Hammah ya kawo mana wasu arnakun material kowa ɗaɗɗaya da kuma lace wanda aka mana gown mai masifar kyau, gaba ɗaya ƙasan ƙace ɗinne aka saka a gaban rigan, sannan aka zuba mishi arnakun stones.
Gashi mummy ta mana ɗinkuna kaman babu gobe, shima ganin haka Hammah walid ya saya mana wasu takalma da jakansu kowan mu kala ɗaɗɗaya, akowanne yakai 15k, a wurin Mummy ya saya.
Week ɗin da za'a fara bikin kuma Besty ya samu appointment letter ɗinshi a inda yayi interview Wato FORTH AUTHORITY branch ɗinsu dake lagos.
Saboda haka ranan saturday yazo ya mana sallama, duk sai naji babu daɗi, don za'ayi bikin baya nan, da zai tafi ya bani mint na 50K yace muyi haƙiri babu yawa, nabawa Besty 20K na ɗauki 30k na liƙi wa amare, kaman zanyi kuka na rakashi jikin motanshi ya tafi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.