*BADARIYA*
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga kinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira.}_🎐G•W•A🎐
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•* 🏇🏻_Story and written
By
*AUNTY NICE**_WANNAN BOOK SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~
*PAGE* 36---37
*__________📖* Baba ne ya matso kusa da Abdallah gaba ɗaya illahirin jikin shi rawa yakeyi, riƙo hannun Abdallah yayi yana cewa "me kaji sunce ƴan biyu"?
Rungume Baba Abdallah yayi yana ƙara sautin kukan shi, lokaci ɗaya Baba yaji hankalin shi ya na neman birkicewa, riƙo Abdallah yayi jikin shi sosai, ya rasa kalma ko ɗaya da zai fito a bakin shi.
Abdurrahman na gani mutane sun ɗago shi ana neman motan da za'a saka shi domin daga dukkan alamu suma yayi, hankali a tashe Baba ya dubi Yusuf yace, "wai me yake faruwa ne Yusuf?"
Da sauri Yusuf ya matsa kusa da abokin Abdurrahman yana tambayan shi abin da ya faru?
Daga nesa na hango Abba yana sauri hannun shi rike dana Abban bch suna tahowa inda su Baba suke.
Abba ne ya riƙo hannun Baba yana faɗin "Alhaji kada ka ɗaga hankalinka, dolen mu murungumi abinda Allah ya aiko mana hannu bibbiyu, yayaj zamuyi Babagana lokaci yayi, yanzu sai muyi sauri mu wuce bauchin".
"Bana fahimtan fah abun da kuke faɗa"inji Baba dayake riƙe da Abdallah har lokacin, kuma daga dukkan alamu Baba ya shiga ruɗani ne.
Kafin kace komai jar gurin ya ɗauka da batun hatsarin su Babagana da kuma rasuwar shi.
Babu ɓata lokaci taron ɗaurin auren ƴa fara watsewa, domin dukkan illahirin jama'an wurin mota kawai ake shiga ana komawa bauchi.
Gaba ɗaya haraban specialist hospital bauchi cike yake maƙil da motocin ƴan ɗaurin aure, wanda ya rikeɗe yanzu ya koma na karɓan gawan su Babagana.
Allahu Akbar kullu nafsin zaƙikatul maut, dama duk mai rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, yau kuma an wayi gari da raɗaɗi da ciwon mutuwar Babagana Nuhu Jama'are, wanda ya rasu a tafiya ɗaurin auren shi da Fatima Badariyyah.
Dayake Babagana mutumin mutane ne, wanda zan iya cewa duk gidan su babu wanda ya kai shi yawan jama'a da abokanai, domin kuwa shi koda abokan Baban shi ne sunfi sabawa da shi, ga dayawa kataɓa a garin bauchi zaka samu akwai mu'amalah mai kyau tsakanin su, shidai Babagana mutumin mutane ne.
Babu ɓata lokaci aka wuce dagawan zuwa gidansu dake GRA.
Tunda Besty ya shiga mota suka tafi naji zuciyata kaman zata tarwatse, haka kawai naji zazzaɓi yana shirin kamani, a cikin hankali da nutsuwa na wuce gidan mu, kai tsaye ɗakin Abba nah na buɗe na shiga na kwanta, domin hayanin gidan namu yayi yawa.
Ko minti ashirin banyi da kwanciyaba naji gaba na yana ta faɗuwa, lokaci ɗaya naji babu abinda nake so sai kawai naji muryan Besty na, da sauri na ɗauki wayana da nufin na neme shi, sai naji gabana yana faɗuwa, bazan iya ƙira ba.
Komawa nayi na kwanta, amma sai naji bazan iya hassala komai ba, sake tashi nayi na zauna na zubawa ƙasan ɗakin ido na rasa tunanin me nakeyi.
Ƙaran buɗe ƙofan ɗakin ne yasa na maida ido na bakin ƙofan, Ummi na nagani ta shigo tare da Aunty na, kallona Aunty tayi tace, "auta nan kika dawo?halan hayaniya ya miki yawa ko"? Ta faɗa tana ajiye coolern da ke hannun ta.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.