*BADARIYYAH*
*1441H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar rayuwar duniya da lahira._ }🎐G•W•A🎐
*GASKIYA DOKIN ƘARFE*🏇🏻Story and written
By
*_AUNTY NICE_**_WANNAN BOOK ƊIN SADAUKARWA NE ZUWA GAREKI MISS XERKS._*
~Whatpad@GaskiyaWritersAsso.~
*page* 97--98
*___________*📖Suna shiga da gudu-gudu sauri-sauri ta ƙarisa bakin gadon, yaye bargon tayi ta ƙurawa mun ido yadda nake ta ɓarin sanyi, ga wani zazzaɓi mai zafi da ya rufe ni, idon ta ne ya sauƙa akan bedsheet ɗin daya gama ɓaci da jini kacha-kacha.
Hannu Aunty ta saka don ta jawoni, bansan lokacin dana kurma wani ihu ba, har saida yayi sanadin shigowan Hammah da gudu, tsayawa yayi daga bakin ƙofah yace, "Aunty yayah take ihu"?.
Mama ce ta juyo cike da masifah tace, "ba dole tayi ihu ba, duk ka yagalgala musu yarinya, Allah dai yasa baka haɗata da yoyon fitsari ba, dubi rashin imanin da kayi akan yarinya Hamman su", ta faɗa tana bin shi da hararah.
Bai sake ce musu komai ba ya juya ya fita ya bar ɗakin, Aunty ce ta taimaka ta kaini toilet ta mun gyara na musamman, bayan ta taimaka mun nayi wanka muka fito ɗakin, inda muka samu Mama ta yaye bedsheet ɗin ta fita da shi, bayan nasaka kaya ne, Aunty ta riƙo hannu na muka fito domin tafiya side ɗinta, sai buɗe ƙafa nakeyi hawaye yana bin fuskana.
A parlour muka haɗu da Mama tana ta yiwa Hammah faɗa, ganin fitowan mune yasaka duk suka juyo suka zuba mana ido, Aunty ce ta dubi Hammah tace.
"Bari muje asibiti zan mata ɗinki", kanshi ya ɗago da sauri ya dube ni, fuskan shi cike da tsoro, Mama ce da sauri ta amsa da.
"Ba dole a mata aiki ba, irin wannan haukan da ya sauƙe kaman a filin daga, kai wallahi kagyara halinka, ce maka akayi abinci ce da ka kusan cinyeta duk"?.
Bayan Aunty ta mun ɗinki ne muka dawo gida, kai tsaye side ɗinta ta wuce dani, inda ta shiga kula dani kaman wacce na haihu, nidai gaskiya ban san meya ke damuna ba, babu hali na tuna abinda Hammah ya mun sai nayi kuka, don wallahi yaci zalina.
Haka Hammah ya dinga jelan zuwa dubani har na warke garau amma Aunty batayi maganan komawa na ba wanda sai naji na samu nitsuwa har hankali na ya kwanta.
Sai da na ƙara sati biyu bayan na warke tukun Baba ya saka baki na koma gidana, don wannan karon Hammah yana ɗauka na mukayu side ɗin Mama, tana ganinmu tace.
"wallahi baka isa ku zauna mun a ɗakina ba, ka wuce da ita gidanka, kalan kaje wannan karon ta yage ka tara mun fitinannun iyayenta? Wancan ma nayita addu'a kada kakanta yaji labari, don ba kai ba hattah ni sai ya lakaɗawa duka, don tsohun soja ne marar imani".
Hammah tunda muka shiga mota yake ta tuntsura dariya wanda bansan dalilin shi ba, nidai banda faɗuwar gaba babu abinda nakeji, sai mamakin abinda yake saka shi dariya kawai nakeyi.
Har muka isa gidan bai daina dariyan shi ba, muna isa naga yadda gidan yasha gyara, ga wani ƙamshin turare da yake ta tashi a kowane side na gidan, kasancewar tun jiya Aunty ta saka masu aikinta suka je suka gyara gidan, yau kuma tun safe suka je suka saka turare suka shimfiɗa bedsheet a ɗakunan, gida dai yayi kyau abin sha'awa.
Nidai gaba ɗaya tunda muka dawo a tsorace nake, amma sai naga Hammah shi ko nuna ya damu da abinda nakeyi baiyi ba, haka dai na shiga ɗakina, amma nakasa taɓuka komai na zauna a bakin gadon nayi tagumi.
YOU ARE READING
BADARIYYA Completed {03/2020}.
RandomLabari mai ƙayatarwa,nishaɗantarwa yare da faɗakarwa.