Introduction

746 48 6
                                    

Wacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban mamakin gaske ne! Ko wani dalili yana sa uwa ta tsani ýarta? Wanne dalili ne wannan da zai iya juya matsananciyar soyayyar da uwa ta ke yi wa ýarta ta koma kiyayya zalla? Ita kuma ýar wacce irin rayuwa zata yi? Wanne irin kalubale zata fuskanta? Wanne irin hali zata shiga kuma ya za'ai ta warware wannan kullin? Wa zai bata amsar wannan tambayar mai nauyi?

Duka amsoshin ku suna cikin labarin WACECE NI wanda zai zo muku nan ba da daďewa ba. Ku biyo ni cikin labarin Ihman ku karkaďe kunnuwanku kuji dalilin da ya sanya Inna take wa Ihman kiyayya mai ban mamaki da halin da Ihman zata shiga da kuma yanda za'ai ta warware kullin da yake cikin rayuwar ta ta gane WACECE ita?

Littafin kyauta ne votes ďinku da comment kawai nake bukata.

Sai mun haďu!

Ma'assalam
Cutyfantasia

wacece ni?Where stories live. Discover now