🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇
*•Baya Chanza d'and'anon teku•***Fatima Muhammad Gurin**
*Gureenjo6763 on wattpad*'Yar Mutan Adamawa
*Taa-daaa!!!! Happy Eid el fitr, Allah ubangiji yasa ibadunmu kar'ba'bbu ne yasa muna daga cikin en tattun bayi na wannan wata, rabbi ya gafarta mana dukkannin zunnubanmu ya sa muna daga cikin masu tsawon kwanan ganin wani azumin**innal hamda lillah, Alhamdulillah, bismillah tawakkaltu Alallah wala haula wala quwwata illah billah*
*P1*
Kallon fuskar wayar dake ta kara tayi tare da fad'ad'a fara'arta ganin me kiran, leka fuskata kan wayan nayi naga an saka "ruhool na'im❤️🔐" d'auka tayi cike da murmushi tace.
"hello this is Mrs Saif shamsuddeen Suraj how can I help you?" Dariya yayi daga d'aya bangaren yace "hooo oo my heart ke baki gajiya da zolaya but that name suits you and kin wanke laifinki".
Murmushi tayi tace "am sorry Abban Neeha ban kira ba I was so busy with your kids ne su suka d'auken hankali".
Yace "I'm badly missing them up here" cikin shagwa'ba tace "ni kuma fah?" Dariya yayi yana cewa "mene?" Turo baki gaba tayi tace "nayi fushi" tana shirin kashe wayan kenan taji muryanshi cikin kitchen d'in.
"Surprise"
Wani irin ihu tayi tana juyowa tare da fad'awa jikinshi sossai farin cikin ganinshi ya bayyana a fuskanta."What a surprise!!!" She exclaimed
Yace "I so much miss you sweetheart d'azu da ban fad'a ba har anyi fushi dani right?" d'agowa tayi daga jikinshi ta kalli kanta sanye take da doguwar rigar simple material se hulan dake kanta ko ear rings babu kunneta ta kalleshi yaci wanka cikin sky blue yadi me shara shara ya kafo zanna bukar d'innan yadda take son shi se kamshi yake zubawa.Baki ta tura tace "I'm jealous" lakace mata hanci yayi yace "anty jealousy am hungry of you muje d'aki daga baya kya d'aura daga inda kika tsaya" sossai ta shagwa'be fuska tace "wato kai ko a jikinka?" Kafad'a ya d'aga yana ta'be baki, da sauri yaja baya ganin ta d'aga hannu da niyyan dukanshi gwalo ya mata ya juya da sauri aiko da gudu ta biyoshi be tsaya ba se d'akinshi tana kawo hannu ya chabke ya murd'e.
Ba ta yadda zata ji zafi ba ya mannata da jikinshi ta baya tare da sanya kanshi cikin wuyanta yana shakan daddad'ar kamshinta nan take ya kashe mata jiki da salonshi kan kece me zance ya sauya.Bayan sun samu natsuwa ya kara rungumeta cikin jikinshi yana son matarshi sossai har abada be tunanin za'ayi mace da ta kai mishi ita a komai har kwanciyar aure, ya zurma cikin tunaninta bayan gata a kan jikinshi se ji yayi tana shafa cikinshi tace "na tabbatar bakayi breakfast ba love gashi har to 12, lemme get you something to eat".
Tana kokarin mikewa ya dawo da ita da hannu d'aya d'ayan hannun yasa ya kama fingers d'inta yana wasa dasu yace "In Ina tare dake heart bana jin komai bare wannan abincin da kika ban yafi min ko wani irin abinci" murmushi tayi tace "I have to cook oo bcs kids sun kusa tasowa".
Yace "you don't have to yau gabad'aya ba shiga kitchen hutawa zakiyi".
Tace "then what are we going to eat?" Kissing lips d'inta yayi yace "you" waro ido tayi zata kuma magana yace "Allah d'agani" ya yunkura ya mike da ita zuwa toilet wanketa yayi kan ta tayashi yayi nashi sukayo na tsarki suna fitowa taji ana sallama daga parlor, kallon ta yayi itama shi take kallo sbd ta san In yana gari baya son baki na zuwar mishi gida, cewa yayi "are you expecting someone?" Kai ta girgiza, yace "Ohk lemme check".Jallabiya ya sanya kan towel d'in jikinshi gashin kanshi jike yake da ruwan wankan da sukayi yanzu, seda ya bi corridor d'in d'akunan nasu kan ya fito babban parlorn gidan daga bakin corridorn ya tsaya yana kallonta, ta ci wani irin ado na tashin hankali fuskan nan yasha penti ko ta ina ta saka wata arniyar straight gown na atampha da ya kamata har numfashi da kyar take.
Tsiririyar gyalenta na rike a hannunta da tsinanniyar hill d'inta ta shigo har tsakiyar parlorn ta samu wuri ta zauna, kallon kanta yayi d'aurin da tayi me bayyana rabin kai ne attachment d'in dake sanye a kanta ya bazo har tsakiyar bayanta, murmushi ta sake mishi tace "yaushe a gari?".
Kwa'be fuska yayi yace "mene?" Waskewa tayi tace "Ina yini?" Ba yabo ba fallasa yace "lafiya" ba tare da ya kuma tankawa ba ya juya don komawa tace "erhhmm nace ba, matar gidan fah pls?" Juyowa yayi ya mata kallo d'aya ya juya ya koma room d'inshi.
Tana gyara doguwar rigar atamphar jikinta da aka mishi d'inkin A shape ya tsuke daga sama har kan cikinta daga kasa kuma ya baje, tace "wayene roohul na'im?".
Tsiririyar tsaki ya ja yace "a duniya ban ta'ba ganin abinda na haneki dashi kika cigaba dayi ba se kawance da wannan 'yar iskar yarinyar, I hate her for that me yasa ne ni kam?" Shagwa'bewa tayi tace "haba love ban fa sanka da haka ba, Ina kawance da ita ne sbd watakila In iya zama sanadiyar shiryuwanta kaga dagani har kai zamu samu lada, I'm sorry please".
Hararinta yayi yana zama stool d'in mirror yace "karki yaudareni da wannan puppy face naki" murmushi ta saki sanin ya bar maganan kenan, d'ankwalinta ta d'auka ta kafa d'auri tare da matsawa jikinshi ta d'an kwanto tare da mika hannu kan mirror ta d'auki turarenshi ta feffesa tana ajiyewa tayi pecking cheeks d'inshi tace "am coming" ta fice daga room d'in.
Da kallo ya bita he loves her, he always do be ta'ba ganin simple and caring mutum irinta ba she's always smiling baka ta'ba ganin fushi kan fuskanta ko da kuwa en uwanshi sun bakanta mata yadda suka saba, ajiyar zuciya ya sauke yana huro iskan bakinshi waje yace within his throat "three kids, ko se yaushe zasu dena tsanarki su gane kyawawan halayenki?".
"Oyoyo zuby" murmushi zuby ta sake tace "oyoyo shaaty" bata zauna ba tace "Ina zuwa" kitchen d'inta dake manne da parlorn ta wuce ta d'auki bottle water da maltina ta d'aura kan karamin tray tare da sanya cup ta fito fuskanta cikin murmushi tace "yau kuma kece a gidana zuby yaushe rabon da In ganki?".
Cikin rigima kaman wata er bariki tace "hmmm Ai kun kusa dena ganina shaaty tunda duk randa na sanyo kafata gidanki se mijinki ya min wulakanci". Shaati tace "Eyyah kiyi hakuri ba wulakanci bane kawai dae In yana gari be cika son baki bane ba ke kuma kaman had'in baki se yana gari kike zuwa".
'Daukan malt d'in tayi ta fara sha ba tare da ta damu da cup ba tace "hmmm kede kawai kare mijinki kike son yi, love birds" dariya sukayi a tare shaati na cewa "haka dae kika ce, Ina su malam da inna?" Iyayen zuby kenan.
Cewa tayi "suna gaidake" hira suka ci gaba dayi sama sama, da gudu wata kyakyawar baby ta shigo sanye da uniform yarinyar bazata wuce 3yrs ba lunchbox ne kawai a hannunta se hijab da shima yana rike a hannunta kitson kalabanta ya sauko har kafad'anta "oyoyo maami" bata ma kula da bakuwar ba ta fad'a jikin uwarta cikin shagwa'ba tace "Maami I miss you".
Murmushi shaati ta sake na farin cikin ganin yarinyar tace "miss you too my baby, where are your siblings?" Tana shirin magana wani yaro da ze yi 4yrs ya shigo kyakyawa kaman wannan babyn wadda duk kammannin na mahaifinsu ne goye da karamin school bag d'inshi hannunshi rike da lunchbox daga bayanshi wata yarinyar ce itama sak su a kamanni bazata wuce 6 ba.
Duk da gudu suka rungumeta itama ta amshesu cikin farin ciki, "Assalamu alaikum" wata ta fad'a tana shigowa sanye da uniform irin nasu sede ita she's dark in complexion ita kuma she's 9yrs old nayi mamakin ganin ta daban ko ba abinda ta d'auko na mahaifiyar ko na mahaifin nasu, "wa'alaikissalam warahmatullah an dawo?".
A gajiye tace "eh maami, barka da gida" dukawa tayi tace "Anty zubaidah Ina yini?" Tana murmushi tace "ohhh Lafiya kalau Arwa ya school?" Tace "Lafiya" shaati ne ta kalli sauran yaran tace "Yasmin, Sameer, Neeha baku gaida Anty zubaidah ba" kallonta sukayi a tare sukace "good afternoon Anty zubaidah".
Murmushi tayi tace "how are you guys doing?" Sukace "fine" kallon Arwa Tayi cikin murmushi tace "oya Adda Arwa aje a cire uniform" ta gane da yaran take yi kama hannun sameer da neeha tayi yayinda Yasmin ta bisu a baya suka shige corridor d'in d'akunansu.
Hira suka ci gaba dayi hankalinta na kan saif sede ba daad'i ta bar zuby haka ga kuma tana tunanin yaran sun dawo da yunwa yace kar tayi abinci she knows he mean it ko me zasu ci? Bata gama tunanin ba taji kamshin turarenshi ya bule parlorn lumshe ido tayi ta bud'e su fess kanshi sanye yake da kananan kaya blue jeans da sky blue shirt ya gyara gashin kanshi zuwa sajen nan sun kwanta lublub idanunshi sanye da farin medicated glass d'inshi.
Ba tare da ya kalli inda suke ba ya bud'e kofa ya fita, tana mamakin irin kallon da taga zuby ke mishi, sede bata kawo komai a ranta ba kawai taji ya bud'e kofa ya shigo hannunshi rike da manyan ledoji da sauri ta tashi ta kar'ba.
"Where are my kids?" Ya furta kasa kasa daidai kunnenta bayan ya had'a hannunta da ledan ya rike.
"Suna changing just go back to your room pls I want to surprise them" cikin wani salo yace "really?" Yana wani kashe mata ido murmushi kawai tayi, taune lips d'inshi yayi cikin command sound yace "ki sallami wanchan abar I want to be alone with my family".Fuskan tausayi tayi ya had'e rai ya wuce d'akinshi ajiyar zuciya ta sauke ta juyowa zuby fahimtar abinda yake faruwa yasa ta ta'be baki tace "bari inje zamuyi waya" kan shaati tayi magana ta fice cikin sauri rannan a had'e alamun fushi tayi ajiyar zuciya shaati ta sauke kan tayi kitchen ta ajiye ledojin ta fito zuwa d'akin yaran tana tura kofa taga Sameer da neeha na guje guje sanye da kananan kaya dukkansu girgiza kai tayi tana amsan neeha da ta fad'o jikinta tace "kid's I have a surprise for you".
Duk kanta sukayo har arwa dake sanye da English wear amma riga da skirt, Yasmin dake sanye da riga da wando tace "wow maami what surprise? I know your surprise is very special" Arwa tace cikin sanyinta irin na mahaifiyar tace "maami fad'a da sauri am eager to hear" murmushi tayi tana cewa "ku biyoni" Da sauri suka bita suna dariya.
Direct d'akin babansun tayi dasu tana tura kofan tace "surprise...." ihu sukayi gabad'aya sukayi kanshi suna "oyoyo paapa" mikewa yayi suka rungumeshi gabad'aya cikin farin cikin ya d'aga neeha ya rungume yana jin son yaran nashi har ranshi. Murmushi tayi kawai ta juya kitchen ledan da ya shigo dashi ta duba order ne daga wani elegant restaurant, fried rice with chicken plates da spoons ta d'ibo na mijinta daban daga ka gani zaka san na me gidan ne don kyaunsu a dining ta shirya ta zubawa kowa nashi package d'in a plate ta kawo musu ruwa da drinks.
Seda ta tabbatar komai intact kan ta koma room d'inshi ta samu sun baje suna ta zuba mishi labari tana shiga ta kama kwankwasonta tace "guys food is ready" duk mikewa sukayi suka biyota suna me cigaba da mishi hira yana amsa musu cikin sakin fuska, kowa ya san sit d'inshi a dining so zama duk sukayi suka fara ci Bayan sunyi bismillah a fili.
Tunda suka fara ci ba wadda ya kara magana har suka gama arwa ce ta tattare kwanonin ta kai kitchen tana dawowa paapa yace "oya kuje ku sanyo hijab zamu fita" Da gudu duk sukaje suka d'auko kananun half sunnah d'insu suka sanyo kan su dawo suka samu paapan da maami na hiransu tana tambayar shi Ina tsarabansu, yace "yana car kin san ko akwatin ban fiddo ba".
Tace "Ina kukayi ni ba'a gayyata ta?" Murmushi yayi yace "yi zamanki ki mana gadi gidan yakumbo zamu je Daga nan zamu je gidan Anty tala se ya sukaina duk wai suna son ganina" dammm haka gabanta ya fad'i kallon Arwa tayi se tayi saurin kawar da kanta tausayin yarinyar na kamata ta san bazata dawo cikin farin ciki haka ba, ita karan kanta Arwan seda gabanta ya fad'i Jin sunan mutanen nan amma bazata iya cewa paapa d'insu bazata ba, cikin kawar da damuwanta tace "a gaidamin su sossai" shi karan kanshi ya san bazata ji daad'in hakan ba amma basu da wani option baze watsar da mahaifiyarshi da yayyunshi sbd ita ba.
Sallama ta musu suka fice ita kuma ta zube kujera tana sauke ajiyar zuciya me nauyi a fili tace "Arwa ba laifina bane Ki yafemin" ta jima nan kan ta tashi ta koma d'akinta ta kwanta bayan ta gabatar da sallar azahar ba jimawa bacci ya kwasheta.
*tou fah my readers ganinan Tafe da wata salon ban ce yafi na kowa ba amma believe me salon na daban ne, a sha karatu lafiya*
🖤Gureenjo🖤
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰