🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P26*
A hankali soyayya me karfi ta shiga tsakaninmu da ya Isma'il wani irin so da bazan iya misaltashi ba, ya min sabo da kanshi ko wani lokaci muna tare a chat, WhatsApp call ko video call, komai d'inmu ya zama d'aya har su ya fadila Suna jin haushin irin wannan soyayyar da mukeyi, Mama bata ta'ba nuna min tana so ko bata so ba tunda a lokacin nayi nisa ko ta fad'a ba ji zanyi ba mutumin da muka tashi tare dashi nayi wayau.
Wata hutu da suka ta'ba dawowa wadda bazan ta'ba mantawa dashi ba, randa akace yau suna hanya ban samu kaina ba abinci nayi musu ko ince sbd shi nayi abinci kusan kala biyar da drinks homemade da na kampani, duk a side d'in Hajja na zage na sha wannan uban aiki tana kara min karfin gwiwa don tafi kowa jin daad'in tarrayarmu, bayan na gama na shiga toilet d'inta na tsala wanka da na kusan awa, na fito Shiri ma zama na musamman na mishi na tsala kwalliya ta da sabuwar material da mama ta mana, duk abinda yasa nake hakan sbd wannan ne had'uwanmu na farko tunda muka fara soyayya.
Na kasa zaune na kasa tsaye tsabagen zumud'i ban huta ba seda naji karan shigowan motocin da suka je tarbarsu, zama kawai nayi kan kujeran hajja hannuna dafe da kirji sbd tsananin bugu, chan bayan kusan mintuna 15 da isowarsu naji sakon shigowar massage wayata dubawa nayi se naga shine, murmushi na saki ganin ya rubuto "where are yhu?" Ba 'bata lokaci na tura mishi "side d'in hajja" beyi reply ba, kaman 5mins naji an turo kofa da sauri na mike Ina kallonshi bakina ya Gaza Rufuwa dukda kunyanshi da ya kusa nitsar dani.
Ban hankara ba se ji nayi ya rungumeni, cike da zullumi na zame Ina dukar da kaina yace "come on babe, menene haka? Shekara nawa rabon da na ganki shine zaki hanani pleasuren rungumarki?" Murmushi na saki nace "welcome home, ba wai na zame bane sbd wani abu na zame ne sbd be dace ka rungumeni ba a musulunce if you wanna have me all for yourself then marry me" na karasa Ina sakar mishi murmushi, 'bata fuska ya d'anyi kan yace "not now yanzu me kika tanadarmin?" Kallon dining nayi nace "abinci gasu chan all your favorites" ido d'aya ya kashe yace "only food?" Kau da kaina nayi ina nufan dining nace "lemme call su ya hameed suzo kar su ce ma zasu ci abincin Mama".
Kiransu nayi ina kallon Isma'il da ko kuma glancing inda nake be yi ba, he was busy taping his phone, har su ya hameed suka shigo be kara cemin komai ba dukda son ya fara min magana da nake ji amma aji irin na mace irina a lokacin da nake ji da kyau samari goma se sunyi sallama dani biyu basuyi da ya fadila ba bare ya meena, da kaina nayi serving kowa muka fara ci ba muyi nisa ba su sadiya da su ya fadila suka shigo sukayi joining nan hira ya 'barke sede ni na kasa maida hankali kan hirar sbd ganin gabad'aya hankalin Isma'il be kaina kaman da se kan waya.
Da gayya na fara tari kaman na kware duk yayyuna suka fara min sannu ya meena na zuba min ruwa a cup kurba nayi ina kallonshi sau d'aya ya kalleni ya d'auke kai ajiyar xuciya na sauke a raina na furta 'to kode fushi yakeyi dani don ban rungumeshi bane?' A sanyaye ta karasa cin abincin, bayan mun kammalla muka dawo parlorn hajja aka bud'e wani sabon hirar su ya fadila se tambayansu yadda kasan waje yake suke su kuma suna basu amsa cike da kewa yayinda ni kuma nayi Shiru na shiga duniyar tunani.
Tunani nake ko ya Isma'il yayi wata budurwarne yasa yake shareni gabad'aya ya addabeni, ko ya dena sona ne? Ko laifi na mishi ne? Duk ni kad'ai baby" naji ya ambata da sauri na kalleshi yace "zo ki kar'bi tsarabarki" ya mike ya hameed yace "ba wani tsaraba kace kana bukatar space da masoyiyarka mu kuma munzo mun takura maka" duk dariya aka d'auka banda Ismail da tuni ya fice da sauri na bishi cike sa kunya.
Tafiya muke side to side sede ba abinda ya ce min gajiya nayi da shirun nace "bae me nayi maka ne?" Yace "me kika gani?" Nace "naga tunda naki ka rungumeni kake fushi baka sake kulani ba after all ba haka muke da ba, ko kayi wata buduruwa ne ka dena sona?" Wani irin murmushi ya saki muna shiga room d'inshi dake side d'insu ya riko hannuna duk yadda nake so in kwace tunanin kar ya kuma fushi dani ya hana, yana kallon tsakiyar idona yace.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰