RUWAN SAMA.....

520 58 6
                                    


      🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
  *Baya Chanza d'and'anon teku*

     *Fatima Muhammad Gurin*
   **Gureenjo6763 on Wattpad**

           'Yar Mutan Adamawa

     *P22*

Abinci ta kawo mata pepper soup na kan sa da bread se kayan tea, da ruwan zafi da kanta ta jere mata su ta had'a mata tea ta mika mata a zaune haka ta ci abincin akan gado, tana yaba mutuncin jidda yanzu duk girman gidan nan bata da girman kan neman me aiki tazo tayi ta mata komai da komai, minti minti take sake murmushi In taga yadda jidda da zaheedan suka zuba tagumi suna kallonta ko er tari tayi za'ayi saurin tambayarta, a haka ta gama breakfast d'in.

"In baki koshi ba an kusa gama abincin rana se a zubo miki" Kai ta girgiza tana shafa cikinta alamun ta koshi, Tray d'in ta d'auka ta fice, yayinda zaheeda ta bud'e babin surutu dukda ba amsa mata shaati ke yi ba se murmushi, a bangaren jidda kuwa Bayan ta mayar da trays d'in kitchen ta nufi d'akinshi ta duba har yanzu be tashi ba kila se asr, komawa d'akin ta tayi ta za'bowa shaati wasu kayan bubu atampha da gyale Don jikinsu ze yi d'aya da shaatin In ma Shaatin zata nuna mata wani abu se hips, d'akin shaati tayi ta ajiye mata kayan tana cewa "Aunty Aisha kiyi wanka ki sanya se muje asibiti In duba lafiyan babynmu kar a shiga hakkinshi".

Memo da biro da jidda ta ajiye gefen gadonta ta d'auko tayi rubutu ta mikawa jidda "ki taimaka pls dama duk banji motsinshi ba" waro ido jidda tayi tace "shine kikayi shiru? Maza tashi kiyi wanka mu tafi Allah dae ya sa lafiya har kika ci abinci be motsa ba?" Gyad'a kai shaati tayi tana Mikewa da dabara don kafanta dake tsananin ciwo wanka tayi ta sanya kayan ya kuwa zauna mata gwanin kyau ta yafa gyalen Bayan ta d'aura d'an kwali.

Ta samu wuri ta zauna tana jiran jidda chan se gata sanye da Italian gown coffee color tayi wrapping gyalen ta makala pin hannunta rike da wata moshiano toy brown bag, kafanta sanye da snickers black, farin glass sanye a idanunta "muje ko na gama" Mikewa shaati tayi suka fito zuwa kasa inda anan taga zaheeda na kallon cartoon a Nickledion neeha ce ta fad'o mata rai tuna yadda suke fad'a da sauran yayyunta akan tashan.

To Ina ta baro 'ya'yan nata tunda bata manta Sunansu ba? Tambayar da tayiwa kanta kenan wadda ta rasa amsa, "taso muje In saukeki gidan yaaya don na barki nan kya iya hana Abieynki bacci" Mikewa tayi da tsallenta suka fito wata Elantra blue ta janyo suka shige, fitansu kan kwaltan da ya kasance shiruu se polisawa da sojoji da zaka dinga hange gida na d'aya na biyu na uku by there left tayi parking tace "oya bye bye" sauka zaheeda tayi tana d'aga musu hannu da gudu ta karasa tayi knocking seda suka ga shiganta kan jidda taja tana cewa shaati "gidan iyayena kenan mahaifinshi wa ne ga mahaifiyata".

Kinga nan ta nuna mata gida na hud'u by right "nan ne gidanmu" murmushi shaati tayi tana gyad'a kai, nuna garin tayi ta juya hannunta jidda tace "wai nan wani gari ne?" Gyad'a kai shaati tayi jidda Tace "borno kenan" murmushi shaati tayi haka jidda taci gaba da mata bayani duk inda zasu wuce ita dae sede ta murmusa ba laifi bane don zaheeda na surutu ga inda ta gado ko shi Shareef d'in na da wannan surutun? Ta tambayi kanta a haka suka karasa asibiti.

Duk inda zasu wuce se anyiwa jidda magana tsabar yawan mutanenta kuma ko yaya se tayi surutu harda masu jinyar patients, nurses da colleagues d'inta doctors kowa dr jiddah, a haka suka karasa office d'inta kwanciya tasa shaati tayi ta mata scanning cikin taka tsantsan anan ta gano yaron be da lafiya, da kyar yake motsi kad'an wadda ba lallai har uwar taji ba, paper ta samu tayi rubuce rubucenta kan suka fito.

Daga asibitin chemist babba sukaje ta shiga ta sayo magunguna daga nan suka wuce wani katon mall, gowns tayi ta jidarwa shaati masu tsada, ta sayi atamphopi kala biyar laces biyar shadda uku kampala biyu, ta sayin gyalulluka, ta saya mata takalma da jaka kaya kam kaman ba gobe garda en kunnaye da sarkoki, man shafawa da gel na wanka su shampoo da turaruka, itade shaati binta kawai take a baya tana kallon ikon Allah.

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now