🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
*Baya chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P20*
Tafe yake cikin tsananin gudu kaman ze tashi sama kasancewar hanyar ba wasu ababen hawa sbd dare da ya raba har asuba na neman shiga, gudu kawai yake yana duba time ana bukatarshi maiduguri kan karfe 8 na washegarin ranar meeting d'in is so important to him gashi se bayan magrib ya baro Abuja, ko kad'an be tsoron irin hanya haka ya riga ya saba tafiyan dare MAJ Shareef kenan, ko Ina yana iya zuwa cikin dare sbd ya saba kuma bashi da tsoro.
Duba time da yakeyi kuwa sbd matarshine jiddah ya san In har ya hau hanya hk kuma ta sani bata iya bacci sbd rashin tsaron da kasar ke dashi sede shi fa ba ruwanshi In yayi niyyan abu to fah se yayi, tun daga nesa yake hangan kaman mutum ne kan tsakiyar titin kuma kaman mace da ciki, slow down ya fara zuciyarshi cike da zargin anya ba tarko bane aka kafa? Sede Ai bazece daga wasu colleges d'inshi bane tunda ba wadda ya san tahowarshi, kila 'barayi ne kara speed yayi sossai ya nufi kanta kaman ze bugeta da karfi ya taka birki gab da ita har motan na ta'bata ganin ko kallonshi batayi ba hannunta dafe da cikin idanunta na kallon gabanta.
Bindiganshi ya d'auka kan ya bud'e kofan ya fito "baiwar Allah" ya ambata ba tare da ya matsa kusa da ita ba, kallon kafafunta da suka wani irin suntuma yayi Allah kad'ai ya san iya tafiyar da ta sha da wannan kafan, a galabaice ta d'ago manyan idanunta ta kura mishi se ta juya ta fara tafiya kuma a hankali ta nufi kasurgumin dajin dake gabanta hankalinta kwance.
Har ya koma kaman yaja ya tafi yaga inaa baze iya ba kasancewar shi me tsananin tausayi, fitowa ya kuma yi ya nufeta zuciyarshi d'aya ya sa hannu ya rike hannunta, da sauri ta d'ago ta kalleshi tana zare ido tare da kokarin fisge hannunta sede rikon da ya mata ba da wasa ba, motanshi ya nufa da ita ya bud'e ya sanyata tare da zagayawa ya shiga, gangarawa yayi yayi parking dukda ya san hatsarin irin wannan tsayuwa Allah ya taimaka ma ba dajin tsakanin Abuja da kaduna bane sede na kaduna da Abujan ma ba wani tazaran banbanci, "baiwar Allah me ya fito dake cikin wannan tsohon daren da ciki haka?" Ba amsa se kallonshi da takeyi.
Jikinta ya kalla batayi kama da mahaukaciya ko almajira ba ya kuma cewa "bakya magana ne?" Nan ma Shiru dafe kanshi yayi yana kuma duban time, ganin call d'in matarshi masoyiyarshi yasa ya d'auka yana huro iskan da ya cika mishi baki, "Assalamu alaikum ya reef ya hanyan?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "lil hanya Alhamdulillah sede an d'an samu er matsala" rud'ewa tayi ta fara tambayar ko wani abin ne ya sameshi.
Yace "calm down lafiyata kalau, wata baiwar Allah na gamuda cikin dajin Allah ba gida gaba babu baya gata da tsohon ciki duk kafanta ya kumbura ga kayoyi ciki" salati ta d'auka cikin tausayawa tace "daga Ina ta ce maka take ya reef? I pity her" sanin halin matar tashi da tausayi yasa ya murmusa kad'an yace "taki magana lil da alamu bata magana, ban san yadda zanyi ba Lil gashi Ina running out of time, me shawararki?" Cikin kulawa tace "ka taho da ita kawai ya reef, In tayi magana daga baya ta fad'i inda take se a mayar da ita" cikin son tabbatarwa yace "do you really think this is right?" Tace "yes sure bcs we don't have any other option sbd we can't say from where she is kaduna or kano, am quit sure ka baro kaduna yanzu zaka fara shiga wuraren kano ba inda za'a kaita ba tare da tayi magana ba more over ga ciki, did she looks like Muslim?" Yace "eh, she's wearing a long hijab" Tace "Ohk just ka zo da ita I really pity her" yace "Ohk dr jiddah" dariya sukayi kan suka kashe wayan.
Jan motan yayi suka hau hanya karatun dake tashi kasa kasa ya karawa volume nan da nan bacci yayi awon gaba da ita gudunshi ya cigaba da shatatawa gab asuba suka kawo maiduguri, a gate aka dakatar dasu sede ganin wadda ke motan yasa suka daskare hannu kawai ya d'aga musu, aka bud'e mai ya shige ya barsu da gulman yadda yake rayuwarshi shi kad'ai dukda yana da yara escorts kenan dariya wani sojan yayi yace "dama ni aka sa kasanshi kun san wani lokacin gudu yakeyi ya 'bata musu shikenan sede su jishi wani garin?" Dariya duka sukayi imagining yadda ze gudu ya 'bacewa yaran nashi.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰