🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*'Yar Mutan Adamawa
*Wannan page d'in naku ne masoyana musamman Gureenjoh Novels group, godiya ba adadi da kulawarku gareni Son so❤️*
*28*
Ban san iya adadin lokutan da na d'auka a sume ba na de farka na ganni kan wata taburma a kwance wata tsohuwa na zaune gefena tana min fifita, a razane na mike zaune ina kiran sunan Allah sbd duk a tunanina zan farka na ganni hanun Isma'il, "sannu baiwar Allah, Sannu Allah ya sakamiki" kuka na fashe dashi Ina jin duniyan na min baki Kirin seda nayi kuka me isata kan ta fara bani baki da kyar nayi shiru tace "ga chan ruwan zafi muje In gasaki ko zaki iya?" A lokacin jikina yayi tsananin tsami ko tsayuwa seda ta dafani nayi mukaje toilet d'inta dukda de gidan kam akwai kazanta haka na daure ta min wankan ta gasani ba laifi naji dama dama sede ko ni na san ina bukatan ganin Doctor.
Wani d'aki ta buge yankwanannen kofar katakon ta shige tana cewa "biyoni nan d'akin 'yatace Bari In nema miki kaya cikin nata" haka ta bincika duk kayan banzan da suke wurin da kyar ta samu jallabiya guda ta bani na saka, tace "na san kina jin yunwa amma wallahi baiwar Allah banda kwandala......" shigowa d'akin da akayi ne ya sasu duk mai da hankali bakin kofan d'akin wata buduruwace ta shigo cikin shigar banza ko arzikin d'ankwali babu da farko nayi tunanin kafurace sbd ba abinda ya banbantata dasu se kuma naji mahaifiyarta tace "zubaidah" suna na biyu da ya gama tarwatsamin rayuwa.
"Inna wace kuma wannan da har zaki bata kayana ta saka ba tare da an tambayeni ba?" Inna cikin lallami tace "wallahi taimakonta nayi fyad'e aka mata inaga ta samu ta tsira daga garesu ne muka gamu kan tayi magana ta fad'i sumammiya kinga yanzu farkawarta wanka kawai tayi shine na nemamata nan kin san bazata iya saka kayana ba".
Shiru zuby tayi tana kallona se kuma ta saki murmushi ban sani ba ko Don taji tausayina ko kuma kyauna ne ya ringayeta don se kallona takeyi tace "sannu" nace "Yauwa" inna tace "zubaidah nace don Allah in da wani abin hannunki ki d'an bamu In sarrafa mata abinci, kin san wanchan bokan uban naki ba bayarwa ze yi ba seda muka kwashi bala'i ma kan farkawar baiwar Allah".
Cikin tsananin mamaki nake kallon wannan family me kenan? Haka wai suke ko kuwa yau ne kad'ai? Haka zubaidah ta bud'e jakanta ta bawa inna kudad'e nan ta fita Don aike, ba zan ta'ba manta karamcin inna a gareni ba dukda abinda 'yarta tayi min wadda har In mutu bazan manta ba, dukda su sun kasancene masu rayuwa kaman dabbobi sbd rashin ilimi da jahilci da ya musu yawa, rayuwa sukeyi kaman tun kan shigowar musulunci.
Kwana na biyu a gidan nan na fahimci mahaifin ma malamin tsubbu ne Sannan tana da yaya wadda be da aiki se shaye shaye ya shigo su d'ibewa juna albarka da mahaifin da mahaifiyar, ganin nan ba gidan zama bane yasa na cewa innar zan tafi sbd na san duk inda iyayena suke hankalinsu a tashe yake, taso rakani sede naki sam don Mama kusan yankani zatayi ta ganni da waennan familyn da jahilci ya musu yawa dukda sun taimaki rayuwata a lokacin da nake cikin halin mutuwa ko rayuwa.
Zuby da take shishigemin lura da ilimi da kuma natsuwa irin ta masu ilimi ga kyau da wayewa da suke tare dani yasa ta kasa barin kusa dani har seda na bata lambar wayana nace In na isa gida zamuyi magana, sallama mukayi ta ban kud'in napep, har bakin titi suka rakoni na Sami abin hawa kan suka koma gida suna me jaddada min In dawo fah, kar In manta dasu.
Ta 'bangaren Saif kuwa ashe tun daga yammacin ranar da ya kira yaji wayana kashe hankalinshi ya d'an fara tashi be shiga damuwa ba se ganin har washegari da safe kuma har yammaci, cikin rashin kuzari da karfin jiki ya nufi kwatancen gidanmu da na mishi, yana isa da Isma'il ya fara had'uwa sukayi musabaha daga bakin gate se yace "pls Aisha nake nema" ya fad'a yana kallon isama'il d'in kai tsaye sbd be saba wata kwana kwana ba.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰