🍇💦RUWAN SAMA...💦🍇
*•Baya chanza d'and'anon teku•***Fatima Muhammad Gurin**
*Gureenjo6763 on wattpad*'Yar Mutan Adamawa
*P2*
Tunda suka fara tafiya ta dukar da kanta kasa gabanta na tsananta fad'uwa yarinya karama er shekaru 9 har ta san wani fad'uwar gaba ganin shirunta yayi yawa ne yasa shi kallon ta ta mirror ya kuma kalli yasmin da itama gabad'aya bata son zuwan nasu gidan en uwansun sbd abinda suke yiwa arwa, cikin sanyi yace "Arwa, Yasmin hope we are safe?" Kallon mamaki suka mishi yace "yes nah.. yadda ake hararanmun nan se kace ba lafiya ba ko Neeha?".
Kai ta gyad'a Arwa ta waro ido yasmin na dariya tace "paapa ni kam dae ban harareka ba sede In Adda arwa" Da sauri arwa tace "Allah nima paapa ban harareka ba" nan fah yace firr sun harareshi suma suka tsaya a sam basu harare shi ba, wannan hirar ce ta ja har suka manta inda zasu sunayi suna dariya yana taka birki neeha ta fita da gudu ta fad'a gidan tana kiran "yakumbooo".
"Eyehh d'iyar arzikice gidana? Kishiya me ban haushi, uwar masu gida da alamu da malam kike ko? Don in ba shi wannan ballagazazziyar uwarkun ba kawo ku zatayi ba".
Itade neeha tayi lub jikinta bata ma san zancen me takeyi ba shigowar Saif da sallamane hannunshi rike da hannun sameer yasa tace "ahappp Ai na fad'a Sannu malam maraba lale sannu da zuwa..."
Kanshi ya dukar yana me tsugunawa kasa yace "Ina yini hajiyata?" Tace "Lafiya klau malam ya wajen aikin?"..
Yace "Lafiya klau mun sameku lafiya?" Zatayi magana kenan ta d'aura idanunta kan Arwa da Yasmin yafito yasmin tayi tana cewa "ke zo nan rabu da wannan 'bara gurbin ki zo nan munafuka me halin uwarta ke kam na kusa yafewa wanchan shegiyar ke daga cikin jikokina".
Yasmin ta matso a hankali idanunta na zub da hawayen tausayin yayarta tazo kusa da yakumbon ta zauna, kwafa taja ta kalli sameer tace "me gida na karfen ina shefane na ne?".
Murmushi ya saki kawai yana kallon Adda arwa da ta duka bakin kofa, cikin sanyin murya saif yace "Arwa karaso mana" cikin karaji yakumbo tace "ta karaso inaa? Bade gidana ba sede naka da ta fi wayau, ke fice min daga gida kar In tashi In karya kafanki da wani fuska kaman na shed'an".
Da sauri Arwa ta fita jikinta na rawa, Yasmin ma ta mike zata fita yakumbo ta jawota "ke wai yaushe nayi sa'a da ubanki ma bare ke da zaki nunamin wai zuciya, daga ke har ita kunci munafukar uwaku fitsararru kin kusa dawowa gabana In har haka zaki ci gaba dayi inga ta karyar soyayya, wawiya kawai".
Saif yace "yakumbo dan Allah ki dena haka ba Don ni ba a dinga abu ana duba gaba ba'a san me ze haifar ba, ba wadda yafi karfin kaddara ba fata ba kina da jikoki k...." katseshi tayi da "Kai dallah rufemin baki mijin tace wato an wanke maka ka shanye kai gaka me zuciyar imani da tausayi, ba laifinka bane, aikin asiri ne tashi ka tafi ka ban wuri" jiki a sanyaye ya mike In har ze zo gidan yakumbo da yaran nan se ranshi yayi mugun 'baci a koyaushe.
Hannu yasa a aljihu ya zaro kud'ad'e masu yawa ya ajiye mata kan ya wuce shiyar kishiyarta innani mata me fara'a da hakuri ta shanye duk wani wulakancin yakumbo tun Alhajinsu na raye tana kuma sha har yanzu da yake kushewa "lale maraba da manyan gari saifullah kaine", yana zama yace "nine innani mun sameku lafiya?" Tace "Lafiya kalau Alhamdulillah ya wurin su shaati? Ina Sauran yaran?".
Yace "suna wurin yakumboo" mikewa tayi tana kwalawa er autanta kira "Sumayyah! Sumayyah" yarinyace ta fito da bazata wuce shekaru goma ba kusan sa'an arwa da gudu ta rungume Saif "Yaya oyoyo" yace "oyoyo sumayyata ya school?" Tace "fine" innani tace "Sumayyah je maza kira Arwa" Da sauri ta fice don Arwa kawartace sossai class d'insu d'aya, ita kuma innani sanin halin yakumboo yasa ta aika a kirata kila tana chan tsugune kofar gida.
Aiko chan ta sameta hannunta ta kama suka shige shiyar yakumbo zuwa na innani a lokacin har innani ta kawowa Saif ruwa da drinks ya kuwa sha yana kallon Arwa da ta zauna Shiru cike da damuwa, mikewa yayi yana ajiyewa innani kud'i daidai yadda ya ajiyewa yakumbo yace "zamu wuce innani, ga wannan ban samu riko muku komai ba" cikin kula tace "Ai da baka wahalar da kanka ba saifullahi me ka ragemu dashi? Tun kan malam ya rasu ka d'auke mana nauyin komai, har bayan rasuwarshi baka fasa ba, Ba abinda muka nema muka rasa da ka ajiye kud'inka kila ya maka wani anfani" cikin ladabi yace "innani munyi waya da Sulaiman yake cemin ya kusa gama service ya rabu da kasar arnan nan" ya karashe yana dariya tuna yadda Sulaiman ke mitar kabilancin arna.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰