RUWAN SAMA.......

582 56 1
                                    


       🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
   *Baya Chanza d'and'anon teku*

    *Fatima Muhammad Gurin*
  **Gureenjo6763 on Wattpad**

           'Yar Mutan Adamawa

*Wannan page d'in naku ne En Gureenjo novels group comments d'inku na sani nishadi godiya nake🥰*

     *P34*

A yau result d'inshi ya fito, Anty tala da bata jima da sauka ba ta zuba tagumi tana nazarin, yakumbo ta katse mata tunani "tala muje muji me zasu ce tunda naga lokacin da suka ce ze fito d'in yayi ko Ina sulaiman ya tsaya?" Tana rufe baki sulaiman na shigowa se kawai suka mike suka fice a tare zuwa office d'in doctorn da Saif ke hannunshi, zaune suka sameshi yana dubawa suka shiga ya sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah lafiyar shi kalau In Shaa Allahu zamu mishi wata allura yanzu anjima da yamma ze farka da yardar Allah".

Godiya suka mishi kan suka fito yakumbo tace "ko me ya saka shi acting haka?" Sulaiman yace "maybe, maybe fah ya dawo hankalinshi haka nake tunani" Anty tala tace "tabbas ze iya yiwuwa amma na matukar tausaya mishi yadda yake son shaatin nan yanzu ya san ya saketa Ina ze saka rayuwarshi" yakumbo karan kanta damuwar hakan ne dankare a zuciyarta.

Basu jima da komawa ba doctorn ya shigo ya mishi ya fice ya tabbatar musu nan da four hours in shaa Allah ze farka lafiya, aiko dab magrib ya farka a kasalance ya bud'e idanunshi da suka mishi nauyi yana kallon saman d'akin, ya kai 2mins kwance idanunshi a kafe a saman POP d'in d'akin Abubuwan da yayi mata su ke sukar ranshi har gwara mahaifiyarshi ita a kullum Suna tare kuma me yafiya ce a gareshi a ko wani hali amma Aisha!! Sunanta da ya furta cikin zuciyarshi ma seda yaji gabanshi ya fad'i yafi kowa sanin irin zuciyarta.

Runtse idanu yayi se kuwa hawaye suka gangaro mishi tuna randa ya sakata bud'e gate ga tsohon ciki, gorin rashin kawo budurcinta gareshi da yayi alkawari har Abada baze ta'ba nuna mata ko alamun a fuska ba, sakinta cikin dare ga ciki ba imani ya kuma korarta a lokacin, mari... abinda ya san tafi tsana a rayuwarta namiji me duka anya ze iya yafewa kanshi bare har ya iya rokar gafararta? Yaranshi.

Kawai gani sukayi ya mike zaune ya cusa kanshi tsakanin cinyoyinshi abinda ya manta rabon da yayi se gashi yana kuka da hawayenshi kuka me cin rai bakin ciki ya mishi yawa, tsanan kanshi yake ji har kasan ranshi, kau da kai sulaiman yayi hawaye na cika mishi ido yayinda Anty tala kam kukan take tayashi yakumboce ta mike ta dafa bayanshi tana bubbugawa aiko se ya d'ago ya jinginu da ita tare da runtse idanu cikin rawr murya yace "Hajiya taya zata iya yafemin? Ta yaya yarana zasu iya yafemin? Me ya hau kaina har idanu na suka rufe na aikata abinda na aikata ga shaati? Nayi zarginta, I slapped her and then accused her akan abinda batayi ba and divorced her a tsakiyar dare da tsohon ciki hasbunallahu wani'imal wakeel......"

Duk seda suka mishi kuka ba abinda yafi ciwo shine kayi abu ba tare da sanin kayin ba, yayi hurting mace mafi soyuwa a ranshi bayan mahaifiyarshi cikin rashin sani da sharrin mace irin zubaida, sunanta da ya ambata yasa ya tuna ya baro ta asibiti baze ta'ba yafe mata ba sede ba abinda ze mata sede ya saketa ya dankawa mahaifinta taje ita da Allah.

Share fuskanshi yayi yana tunanin wani irin hakuri ze iya ba shaati har ta hakura, yakumbo ta share hawayenta tace "ka yafemin nice sanadiyar duk wani halin da kuka shiga na kasa hakura In yarda kaddarar shaatince haka na ja maka abinda har ka mutu bazaka manta ba" cikin dashewar murya yace "baki da laifi hajiya haka Allah ya kaddara hakan rubutaccene daga rabbissamawati" ajiyar zuciya ya sauke yana mikewa daga jikinta ya furta cikin sanyi "Ina wayata?" Sulaiman ya fiddo daga aljihunshi yace "gashinan" kar'ba yayi ya duba number d'in hospital da zuby take kira yayi cikin sanyin murya suka gaisa ya tambaya Ina patient d'inshi nan sukace sunyi discharging d'inta sun kira wayanshi Baya shiga, suka mishi karya sbd ya kamata yayi suing d'insu taya patient zata bar asibiti ba tare da hospital sunyi noticing ba? Abinda suka sani tunda tana cikin hankalinta zata iya kai kanta gida.

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now