🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
*Baya chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar mutan Adamawa
*P16*
Numbern innani ta kira Bayan sun gaisa take gayamata yakumbo na asibiti ba lafiya, salati ta d'auka kan ta tambayi asibitin, gayamata tayi a sanyaye tace yanzu sulaiman ze kawoni, ta kashe wayan anan tayi zaune tana tunanin ta kira Saif ko kar ta kira har akayi kiran magrib ta mike taje tayo alwala sallayar da ta taho dashi ta shimfid'a ta tada sallah Bayan ta idar tana zaune nan tana azkar taji wayanta na kara "uncle lesu" shi ta gani d'auka tayi tace "uncle sule kun iso?" Yace mata "eh gamu a reception" Tace "Ohk ku taho amenity room 16" ta kashe wayan.
Mintuna kad'an se gasu da sallama, mikewa take kokarin yi innani tace "a kul Aisha yi zamanki Sannu" murmushi tayi tana zaman kuwa dama taji daad'in zaman "sannu da zuwa innani" Tace "Yauwa Aisha me ya faru haka?" Tace "wallahi taje chan gida muna magana kawai naga alamun tana shirin fita hayyacinta shine muka rugo asibiti" kallonta kawai Uncle sulaiman yakeyi cike da tausayawa rashin d'a babban abu ne amma ya suka iya ya rasa sau nawa yake kiran yayan nashi baya d'agawa In kuwa ya d'aga sede yaji muryan zuby ta kuma karta mishi rashin mutunci.
Da kyar ya samu aiki a wani private school na teaching ana biyanshi 33k duk wata sbd kasancewarshi me degree da kud'in makarantar sumayya ya kare ma mijin Aisha ne ya biya er dubu talatin da ukun nan akan kananan bukatun gida yake karewa baya saving ko biyar, maganan Shaati ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi "uncle sulaiman lafiya kuwa Ina ta magana shiru" yace "sorry Inlaw wallahi na tafi wata duniyar ne daban ya nauyin jiki?".
Ta amsa da "Alhamdulillah wurin hajar kuka fito ne?" Cikin damuwa yace "Eh baki gani ba abin tausayi itama har yanzu bata farka ba kuma mahaifinta na kan bincike" cikin tausayawa da sanin hali makamancin haka da ta shiga tace "Allah ya tona asirinshi ya bi mata hakkinta" suka amsa gabad'aya da Ameen kan sule yace "me sukace yake damunta ne?" Tace "wallahi bp ne se low sugar" yace "Allah ya bata lafiya bills d'infah? Nawa sukace?" Murmushi tayi tace "na riga na bada karka damu" Albarka innani tayi ta saka mata tana fata Allah ya ba sulaiman mata irinta.
Yanzu In ba macen arziki ba waye yakumbo Zata yiwa wannan cin kashi ta dawo kuma tana jinyarta a yanayi na ciki? Ai se me karfin imani, innani tace "Toh Allah ya saka miki da gidan aljannah Aisha, ya karkato miki da hankalin mijinki gareki, yanzu kije gida sbd yara ni se in kwana nan" a zuciyarta ta amsa da Ameen thumma Ameen, kan ta d'aura da "innani kema kina bukatar hutu kije kawai zan kwana nan da ita yara kuma suna chan gida unguwan rimi" innani ta matsa Aisha ma ta nace hakan ya sa ta kyaleta sun d'an jima nan kan aka kira wayan Aisha tana dubawa taga driver d'in gidan su ne d'auka tayi suka gaisa kan yace yana waje ya kawo abinci.
Sulaiman ta tura ya kar'bo, bismillahn abincin tayi musu sede sunki su ci ba jimawa sukayi mata sallama suka tafi kuma har lokacin yakumbo bata farka ba, bayan tafiyansu ta d'an d'ibi abincin tuwon shinkafa da miyar zogale se er pepper soup na naman kai, zama tayi taci sossai Don ta manta rabonta da tuwo yaran ba so suke ba se in tayi sha'awa tayi d'an daidai cikinta taci.
Se chan cikin dare yakumbo ta farka zuwa lokacin Aisha ta d'an sa pillow ta kishingid'a kan sallayar abinka da mai tsohon ciki motsi kad'an ya farkar da ita mikewa tayi ta karasa jikin gadon tace "sannu yakumbo" kallonta tayi kan ta kalli d'akin a sanyaye tace "sannu d'iyarnan, wai asibiti nake?" Aisha tace "Eh bari In kira likita" fita tayi ta gayawa nurses ta farka wata nurse ta mike ta biyota zuwa d'akin ruwan ta cire mata tare da duba file d'inta za'a kuma kara mata wani ruwan.
"Mama kiyi abinda zakiyi ki d'an huta zan kuma sa miki wani ruwan" 'bata fuska yakumbo tayi tace "kayya diyarnan baza'a barshi ba kawai" murmushi nurse d'in tayi tace "a'a Mama bakiga halin da kike ciki ba har yanzu? Kiyi hakuri a karasa ku tafi gida gabad'aya" gyad'a kai yakumbo tayi, nurse d'in ta fice Aisha ce tazo Don taimaka mata da sauri tace "a'a Aisha kina fama da nauyin jiki kuma In kara miki wannan bari zan lalla'ba" murmushi Aisha tayi Lallai yanzu yakumbo ta gane gaskiya wai har ita takeyiwa magana cikin sanyi da kulawa? Lallai za'ayi ruwa yau harda kankara.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰