RUWAN SAMA.......

701 61 5
                                    


         🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇
      *•Baya chanza d'and'anon teku•*

    **Fatima Muhammad Gurin**
       *Gureenjo6763 on wattpad*

   'Yar Mutan Adamawa


           *P3*

Weekend me daad'i suka gudanar kaman yadda suka saba In har ya zo weekends be cika zuwa ba shiyasa idan ya zo haka yaran suke matukar jin daad'i, sun ziyarci wurare daban daban a kaduna cikin so da kaunar junansu yau Monday, Bayan ta gama shirya yaran sun wuce makaranta suna me jin kewar baban Don sun san baza su dawo su sameshi ba neeha kam har da kukanta da kyar suka lalla'bata ta tafi.

Suna shiga parlorn ta rungumeshi tace "ni ma kaman in taya neeha kuka zamuyi kewarka" murmushi ya sake yana kissing forehead d'inta yace "yi hakuri kar kiyi In ba so kike in kasa tafiyar ba" tura baki tayi tace "Toh In ka tafi sai yaushe zaka samu shigowa?" Yace "ba rana" trolley d'inshi ta nufa ba tare da tace komai ba ta fara gyarawa duk abinda ta san ze bukata ta had'a mishi tsab ga kayanshi a shirye a goge gwanin ban sha'awa.

Wanka ya shige bayan ya fito ta taimaka mishi ya shirya ganin taki mishi magana alamun fushi take yasa tana gama gyara mishi zaman necktie ta juya kenan ya janyota jikinshi a kunne ya rad'a mata "tuba nake sarauniyata nan ba da jimawa ba zan zo In aiki ya min sauki ma next week se ki ganni kiyi hakuri kinji?" Murmushi ta saki tace "Yauwa hoorul Na'im ko kaifa da fa cemin kayi ba rana" yace "to yanzu akwai shikenan?" Kai ta gyad'a tana me mika mishi dark blue suit d'inshi kar'ba yayi ta sako gyale akan doguwar rigar atamphar jikinta tare da d'ago trolley d'in suka nufi waje.

Har jikin mota seda ya bud'e boot ya saka trolley d'in ya juyo da nufin shiga mota ta fad'a jikinshi ta kankameshi tare da cewa "zanyi kewarka rabin raina ka kula min da kanka please, karka manta da adu'ar matafiya Allah ya tsare min kai da tsarewarshi ya kare min kai daga dukkan wani abin cutarwa" yace "Ameen my dear, take good care of yourself and the kids I love you" ya saketa tare da fad'awa motar ya kunna ja baya tayi tana d'aga mishi hannu cikin kasa da murya tace "love you too".
Hannu shima ya d'aga mata kan ya ja motar kirar GLK 350 ya fice daga gidan ajiyar zuciya ta sauke kan ta koma cikin gidan zuciyarta na cike da kewar mijinta abin alfaharinta.
       Seda ya biya gidan yakumbo yayi mata sallama daga ita har innani kan ya wuce ya kama hanyar Abuja yana juya maganganun yakumbo akan karin aure, shi gaskiya baze iya ba, ba abinda shaati ta rage shi dashi ba ta inda ta Gaza ga kulawar ta gareshi da kuma yaranshi toh me laifinta a abinda Allah ya riga ya rubutashi tun daga randa aka halliceta? Yana sonta ba abinda ze iya ruguza wannan soyayyar da yake mata ba irin ruwan da Za'a kara akan kogin son da yake mata da ze iya chanza d'and'anon sonta a cikin ranshi, gaskiya baze iya yi mata Kishiya ba dama cewa yakumbo yayi ze yi tunani a kai toh da haka ze waske mata.

Tana shiga d'aki taga wayanta na ta aikin haske alamun ana kiranta da sauri ta karasa tana dubawa taga "Ya Meenah" seda gabanta ya fad'i dukda zuwa yanzu komai ya wuce amma fah alakarsu da en uwan nata be koma daidai ba kaman da, receiving tayi tare da sallama ta d'aura da "ya meena ina kwana?" Daga d'aya 'bangaren tace "lafiya kalau ya yaran?" Tana d'an murmushi tace "suna lafiya sun tafi school" ya meena tace "yayi kyau amm wai kinji matar ya hameed ta haihu?" Ido ta d'an waro "ta haihu??? Wallahi banji ba yaushe?".
    Ya meena tace "har jibi suna ban san ai bakiji ba, an samu d'a namiji" jikintane taji yayi sanyi idanunta suka cika da hawaye wai se yaushe en uwanta zasu mance da abinda ya riga ya faru? Ta san bata da laifi tunda duk abinda ya faru ba da son ranta bane ba itama ba yadda ta iya ne sbd bata da wani wayau da dabara, ya meena ce ta katseta da cewa "hello" jin shirun yayi yawa cewa tayi "arhmm inaji Masha Allahu, Allah ubangiji ya raya bisa sunnah bazan samu zuwa barka ba tunda se yanzu nakeji gashi yau babansu neeha ya koma wurin aiki, zan tambayeshi zuwa sunan In shaa Allah" ya meena ta d'anyi jimm kan ta ta'be baki tace "Toh Allah ya kaimu a unguwan rimi za'ayi bukin sunan, Se anjima" bata jira cewarta ba ta katse kiran.
Rike wayan tayi a hannunta hawaye na gangaro mata bata san sadda kuka ya kwace mata ba sossai take kuka tana tsinewa wanzuwarshi a duniya adu'a take yi kullum ba dare ba rana akan Allah ubangiji ya saka mata ya bi mata hakkinta na tarwatsa rayuwarta da yayi, vibration d'in da phone d'inta ya d'auka ne yasa ta goge fuskanta tana kallon fuskan wayan "Maamah" ta gani rubuce fuskan wayan da sauri ta d'aga da sallama.
      Amsata mama tayi daga d'ayan 'bangaren kan ta d'aura "Lafiya naji muryanki haka?" Tana gyaran murya tace "Lafiya kalau Mama Mura nake, Mama ya gidan?" Mama tace "Lafiya kalau, Aisha me ya faru baki kira yayanku hameed kin mishi murnan haihuwa ba ya zo nan ya isheni da mita? Sannan har cikin gida naji ana cewa kinki zuwa barka?" Wasu hawayen ne suka gangaro mata kowa laifinta yake jira a gidan cikin muryan kuka tace "ban sani bane Mama yanzu Ya meena ta kirani take fad'amin wallahi ban sani ba" Shiru Mama tayi na d'an mintuna kan cikin sanyin murya tace "Toh me na kukan kuma?" Shesheka ta fara cikin rawar murya tace "wai se yaushe zasu gane bani da laifi a duk abinda ya faru da rayuwa na?" Ta karasa da kuka sossai tana d'aurawa "kowa fah Mama jira yake nayi wani abu da za'a samu na jifana dashi a cikin family yau na godewa Allah ba don ya turomin saif a rayuwana ba da ban san halin da zan shiga ba, na sani Mama kema har yanzu baki d'aukeni shaatinki na da ba...." katseta Mama tayi "kayya Aisha komai ya riga da ya wuce, yanzu ki dena kukan nan ki kira hameed ki mishi murnan samun karuwan da yayi in da hali kije musu barka ko gobe ne inde mijinki ya barki kenan In kuwa be bari ba ku had'u anan suna jibi kinji?" Kai ta gyad'a sukayi sallama.

Seda taci kukanta kan ta fara neman numbern yayan nata tayi dialing seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga sallama tayi ya amsa mata ta gaidashi ya amsa a dakile tace "ashe kuma mun samu karuwa?" Yace "eh" Tace "Toh Allah ya raya bisa sunnah yasa me taimakon addini ne" yace "Ameen" daga haka ya kashe wayanshi wayan tabi da kallo wasu hawayen suka kuma zubo mata tabi wayan da kallo kaman ba favorite yayanta ba, kaman ba sune sukayi wani shakuwar da zaka d'auka bazasu ta'ba samun sa'bani ba har duniya ta nad'e tana kewarshi tana kewar dukkanin shakuwarsu da en uwanta da yanzu babushi.

Bata san iya adadin lokutan da ta d'auka zaune a wurin ba seda taji wayanta na kara dubawa tayi se taga video call daga habeebinta mikewa tayi da sauri ta shiga toilet ta wanke fuskanta sossai ta fito ta sa kwalli tare da shafa powder kad'an yadda ze 'boye kukan da taci kan ta d'auki wayan lokacin har ya mata two missed calls.
Kiranshi tayi itama video call ringing biyu ya d'aga tar yake kallonta itama haka yana zaune cikin mota juya idanunta tayi tace "yalla'bai barka da hanya" yace "Yauwa yalla'biya" dariya tayi idanu ya kura mata a zuciyarshi yace tayi kuka, katseshi tayi da cewa "sorry kayi two missed calls bana kusa" yace "naga baki kira lokacin da kika saba kira kiji ya hanya ba In har na bar gida shiyasa na kira inji ko Lafiya?" Murmushi ta sake tana cewa.
"I'm so sorry wani d'an aiki ne ya rikeni" ta'be baki yayi yana d'age bakin girarshi me cika yace "aikin har ya Fini ko?" Tace "a'a ya ma isa? Yanzu de ayi hakuri please Sannan a maida hankali kan hanya Allah ya tsare bye" bata jira cewarshi ba ta kashe ta san In ta biye mishi Haka zasuyi ta waya ita kuma tana tsoron kar wani abu ya sameshi tunda ba parking yayi ba yana tafiya ne kuma yake wayan da ita.

Ajiyar zuciya ta sauke tana jinta wasai sbd ganinshi kawai da tayi yasa duk damuwarta sun yaye mikewa tayi ta nufi kitchen da shirin sama musu abinda zasu ci na rana don en school sun kusa dawowa. Jollof rice ta musu na manja da wake Don ta san duk suna so yaji kifi ta juye a food flask babba ta kai dining tana ajiyewa suna shigowa da murnanta ta tarbesu itama kaman yarinya a cikinsu da kanta ta kaisu d'aki ta chanzawa neeha da sameer kaya neeha na ta damunta da surutun abinda ya faru a makaranta tana amsawa bata gajiya da magana da yaran nata Don In har mijinta baya nan Toh fah sune abokanta bata zuwa ko Ina koyaushe suna tare shiyasa sukayi muguwar shakuwa.

Suna fitowa Arwa da yasmin na fitowa suma sun chanza zuwa kananan kaya dining suka wuce arwa tayi serving d'in kowa suka fara cin abinci Bayan sun gama yasmin ta tattare kwanukan ta kai kitchen da gudu neeha ta koma d'aki ta d'auko tab d'inta ta kira paapa d'insu video call aiko ya d'auka gashi zaune a parlornsu na Abuja har yayi wanka ya sauya kaya da murna suka fara mishi surutu wannan ta fad'a wanchan ta fad'a wannan ya fad'a.
      Murmushi kawai shaati ke yi tana kallonsu dukansu basa gajiya da juna basa ta'ba gundurar juna In har ba abinda yakeyi zama yake ya ta zuba surutu da su kaman ba mahaifinsu ba dukda idan ya juya duk tsoronshi suke amma sun shaku matuka dukda ba kasafai suke zama gabad'aya ba idan ba anyi hutu sunje Abuja gabad'aya ba ko ya samu saukin aiki ya taho gida ba, hannu ya d'aga mata yace "wato baza'a min magana ba ko?".
         Murmushi tayi tace "ruhool na'im fah magana kake da sarakan surutun nan Ina naga sararin maka magana?" Kallon yaran yayi yace "Toh fah kunji malamai ku kyale mata zatayi waya da mijinta" dariya sukayi duka har neeha kaman ta san wani me mata da mijin ke nufi Arwa kaucewa tayi ta kama hannun neeha tace "baby zo muje kiga abinda na sayo miki a section d'inmu" da sauri ta mike ta bita sameer da yasmin ma suka mike suka bisu da sauri yasmin na cewa "Ai yau Allah Adda baku isa ba kullum neeha kawai kike sayowa abu In har baki sayo mana ba nata zamu kwace ko sameer?" Yace "yes Adda yasmin" suka shige.

Kallon da yake jefanta dashi ta kawar da "ka isa Lafiya?" Yace "Alhamdulillah me akayi ne?" Ta san abinda yake nufi da hakan, ba wadda ya fishi saninta nan duniya a yanzu ko maamah kuwa so yake yaji dalilin kukan nata da sauyin yanayinta Don har lokacin bata dawo daidai ba duk ta sawa kanta damuwa sbd tunanin abinda zata fuskanta In taje suna amma ya ta iya? Dole taje In ba haka ba ta shiga bakin duniya.

"Babu" ta amsa tana murmushi yace "ban yarda ba" Tace "Yauwa matar ya hameed ta haihu ya samu d'a namiji jibi suna" a zuciyarshi yace so that is it, cewa yayi "Allah ya raya da dare se kuje da yaran kiyi mata barka habu ya kaiku kin san ban son driving d'inki da dare" Tace "Ameen" tana murmushi ta d'aura da "roohul na'im ka kuwa ci abinci?" Shafa cikinshi yayi tare da karkata kai yace "inafa na ci ni da banda wadda ze bani" murmushi tayi tace "please ka fita ka ci kar a bar min ciki da yunwa" jiyo ihun neeha da kukanta yasa tace "uhm toh an ta'ba min d'iya bari naje naji ita da waye, please ka fita kaci kaji love?" Kai ya gyad'a yace "se munyi magana" ya kashe wayan da sauri ta mike tayi d'akinsu Arwa da ipad d'in neehan hannunta.




                     🖤Gureenjo🖤

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now