🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
*Baya chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P15*
YAU NE GOBE NE
Abu de gashinan ga kamanshi zuwa yanzu cikin Aisha ya shiga wata na bakwai kuma har yau bata ga kyallin idanun Saif ba basu kuma waya ba, kud'ad'en gwala gwalanta sun taimaka sossai sede zuwa yanzu komai yayi kasa, har wasu kayayyakin sawanta sabbin supers d'inta ta sayar akan sayan abinda zasu ci a cikinsu da 'ya'yanta.
Har rana yi ta yau bata sanar a gidansu ba se adu'a da take Ta san ko ba jima ko ba d'ad'e Allah ze amsa mata, karan wayanta ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, kallon neeha dake mika mata tayi kan ta kar'ba ganin Abbanta ne yasa ta yi saurin d'agawa da fara'arta "Abba barka da dare" yace "Yauwa Auta ya yaran? Ya kuma karfin jiki?" Tace "Alhamdulillah Abbana, Ina Mama?" Yace "tana nan lafiya, nace Saifullah na lafiya kuwa? Kwana dayawa ya rabu da kiranmu gaisauwan jum'a d'azu nake maganan mamanki ma tace haka itama ta jima rabon da suyi waya".
Gabanta ne ya fad'i ta kirkiri murmushi me sauti tace "Abba yana nan lafiya I guess don muma kwana biyu bamuyi magana ba sbd baya kasan" Shiru Abba yayi yana juya magananta Haka kawai ya kasa yadda da magananta don mutum baya kasa se akace baze kira iyalanshi ba? Gyaran murya yayi yace "Amma kina dae lafiya ko? Mahaifiyarki ta kawo min karanki" da saurin tace "ayi min aikin gafara Abba na dukda ban san laifina ba".
Murmushi Abba yayi yana son diyar nan nashi dukda yana cikin waenda suka kasa yarda da ita a baya sede ya tabbatar bazata fad'a musu abinda ba shine ba, "Tace wani Abu na damunki wadda kika ki fad'a mata Sannan jininki ya hau yadda ba'a so ga me juna biyu" ajiyar zuciya ta sauke tabbas ba abinda ya sauya soyayyar dake tsakaninta da iyayenta da ta zata a baya ya wargaje sbd abinda Isma'il ya aikata ga rayuwarta.
"Abba ba komai" yace "tsakaninki da Allah Uwata In baki fad'a mana matsalanki ba wa zaki gayawa uhmm? Ko de ba Uwata bace da na sani a da wacce bata 'boyemun komai?" Shiru tayi ya kamata ta fitar da abinda ke damunta kar iyayenta suma su shiga tashin hankali In wani abin ya sameta, ta san bata da ya su Sannan binne damuwanta kaman tarama kanta bomb ne wadda ta tabbatar randa ya fashe bazeyi kyau ba sbd tana shanye abubuwa dayawa.
Tuna saura sati guda su Arwa su gama exams in sun gama kuma bata da kadaran sayarwa ta biya musu kud'in wani term d'in tayi, a hankali tace "Abba......." se kuka, da sauri ya mike zaune fuskanshi cike da damuwa tausayin d'iyar tashi itakam daga wannan se wanchan, ta tashi da farin ciki da son en uwanta da faran faran a gidan amma lokaci kalilan ta nemi duk wani farin cikinta ta rasa.
Be katseta ba seda ta fitar da nauyin da ke cikin zuciyarta, kan tayi Shiru tana kallon su Arwa da suka kura mata ido ta kasa controlling ne amma ganin neeha da sameer da yasmin duk suma sun fara kuka yasa ta mike ta koma room d'inta a sanyaye yace "komai ya faru da bawa maganinshi Allah uwata, kiyi hakuri shine ze sa kici ribar kaddararki" share fuskanta tayi tace "Abba rabona da Saif yau wata biyar Abba, be san cinmu ba be san shan mu ba, be san rashin lafiyanmu ba, Abba duk na sayar da komai na har kayan sawana sbd In ciyar damu In kuma biya musu kud'in makaranta" hawaye ya gangaro mata, Shiru Abba yayi cikin mamaki tsantsa mamah ma da ya sa a speaker tana ji seda ta girgiza wani irin juriya ne ga Aisha haka?.
Abba yace "kuma ke kin gwada nemanshi?" Tace "eh Abba In na kira baya d'agawa in ya d'aga kuma fad'a kawai yake hawana dashi, lokacin suna nan kaduna kan su koma Abuja kusan korata yayi" Mamah tace "shi saifullahn? Anya yana cikin hankalinshi kuwa?" Cikin damuwa tace "Mamah banyi zargin kowa ba Adu'a kawai nakeyi Allah ya karkato mana da hankalinshi".
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰