RUWAN SAMA......

490 59 2
                                    


       🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇
    *Baya Chanza d'and'anon teku*

      *Fatima Muhammad Gurin*
   **Gureenjo6763 on wattpad**

         'Yar Mutan Adamawa
  
*Wannan page d'inma naku ne en Gureenjo novels group kuna kasheni da comments d'inku🤣 en team Shaati da team zuby I really appreciate🥰🥰*

     *P12*

Kwance yake rigingine a tsakiyar gadon nata tunani yakeyi amma har zuciyarshi ya rasa tunanin menene yakeyi d'aya, ji yake kaman an sabuntashi nan duniya, ajiyar zuciya ya sauke jin hannunta kan kirjinshi cikin kashe murya tace "baby me kake tunanine haka" kallonta yayi ya rasa me yake ji kanta, tsintar kanshi yayi da cewa "tunaninki nakeyi honey" ajiyar zuciya ta sauke da har tana tunanin aikinsu be ci ba but jin yadda ya mata magana harda honey ta tabbatar komai ya tafi daidai murmushin mugunta ta saki kan ta langwa'be mishi "baby washh zafi muje kamin wanka".

Da sauri ya mike tare da d'agata chak suka nufi toilet se Sannu yake mata alhali chan kasan zuciyarshi ya san ba buduruwa ya sameta ba, haka dae ya mata wankan yace tayi na tsarki nan tace bata iya ba, nuna mata yayi ba tare da damuwan komai ba, tayi yadda yace shima yayi suka fito tana makale dashi.

Alwala yayo yana son yin nafila amma yadda ta narke mai tana kukan shagwa'ba ya hanashi sallahn tare da komawa suka kwanta, ba shi ya farka ba se asuba mikewa yayi yaje yayo alwala ya fito, "honey, honey tashi asuba tayi" cikin bacci tace "kyaleni zanyi anjima" "Toh" shine abinda ya furta kan ya fita zuwa d'akinshi ya chanza zuwa jallabiya kan ya fice masallaci bayan an idar da sallah ya mike ya fito zuwa gida.

Yadda ya barta haka ya dawo ya sameta gefenta ya ra'ba ya kwanta don haka kawai bai son tashinta sbd kar ranta ya 'baci makaleshi ta sake abinda shi bayayi baccin safe haka ya biye mata suka koma bacci se around 10 suka tashi a tare sukayi wanka suka shirya "muje restaurants muci abinci ko? Don gaskiya bazan iya girki ba" Kai ya gyad'a kan yace "Toh muje" suka fice zuwa wani elegant restaurant suka ci abinci sukayi kat kan ta sashi zaga gari kaman yau ta fara fita a garin kaduna.

Se around 12 suka dawo da kaya niki niki Don har shopping seda sukayo, wanka suka sake yi kan suka fito parlor ta kwanta a kan kafanshi tare da kunna kallo shide kallon yake amma hankalinshi na chan wani wurin da baze iya cewa inane ba, ba wai ya manta yana da iyali bane sede baya jinsu a cikin zuciyarshi sam kaman panko Haka yaji ya koma.

*******

Kwance take tunanin abin duniya sun dameta, wai me yake nufi da ita kuma ne? Jiya throughout be je ba ya kira bata kusa da dare ta kira be d'aga ba, ta tabbatar zuwa yanzu kam ya kamata ace yaga miscall d'inta, ko ma be gani ba ai basu ta'ba yini su kwana su kuma wayi gari ba suyi waya da juna ba, wayanta ta janyo tare da danna kiran layinshi.

Seda ya kusa tsinkewa kan aka d'aga to her biggest surprise Zubyce "hello ya akayi" shine abunda ta furta, wani irin fad'uwar gaba taji wadda har kasan mararta tajishi cikin sanyi tace "Assalamu alaiki, me wayan fah?" Murmushi zuby tayi tace "baby kaji abinda take cewa dani da kai ba d'aya bane?" Wani irin mikewa tsaye shaati tayi jin muryan shi yana cewa "d'aya ne mana honey duk abunda za'a fad'amin In ya shiga kunnenki shikenan".

Rasa abin fad'a shaati tayi she is more than shock da abinda take ji, a zuciyarta tace "me ke faruwa?" Daurewa tayi tace "dan Allah bashi ko kice mishi shaati ce" cikin iyayi tace "baby wai shaati ce" tsaki yayi yace "In shaatin ce so what? In bazata fad'amiki abinda take so ba just kashe wayan kizo mu ci gaba da kallonmu" Innalillahi wainna ilaihi rajiun shaati ta furta tana zubewa kan kujera.

"Allahumma ajirni fi musibatin wa aklifnee khairan minha, lahaula wala quwwata illa billah" sune abinda tayi ta maimaitawa bayan tayi disconnecting wayan, ta rasa ma me zatayi anya kuwa ba mafarki takeyi ba? Anya kuwa Roohul na'im ne? Ko de me irin muryan shi ne? Ta rasa me zata kama iyakar rud'ewa ta rud'e duk yadda taso kuka yazo mata yaki ashe hawaye ma rahama ne.

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now