RUWAN SAMA.....

517 55 7
                                    


     🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku*

  *Fatima Muhammad Gurin*
  **Gureenjo6763 In wattpad**

        'Yar Mutan Adamawa

*P29*

A hankali na fara Wara idanuna da suka min matukar nauyi na kurawa pop d'in inda nake idanu chan na juya a hankali se nayi tozali da fuskan Mama akan tebur d'inta sanye da lab-coat idanunta sanye da farin glass na jima sossai Ina kallonta yadda a lokaci kankani ta rame damuwa tsantsa ya bayyana a kan fuskanta tausayinta ne ya ratsa zuciyata ban san sadda na fara yiwa Isma'il Adu'o'i marasa daad'i ba a raina, kaman ance ta juyo se taga idanuna bud'e suna kallonta da sauri ta mike ta nufoni.

Hannuna ta kama tana zubar da hawaye tace "ashe baki da hankali Aisha? Irin tarbiyar da na miki kenan?" Girgiza kai nayi cikin kuka nace "Mama ya kukeso nayi? An saceni an lalatamin rayuwa na samu na tsira da taimakon Allah na dawo gareku sede kunki yarda dani, mama ashe zaki iya yarda yawon karuwanci na tafi?" Na karasa da kuka sharemin hawaye tayi tace "wa yace miki ban yarda dake ba Aisha? Uhmm ko kowa ze ki ki duniya ki cireni ciki, babu uwar da bata san me ta haifa ba da kuma irin tarbiyar da ta bashi na sani sede shedu sun nuna tafiya kikayi hakan ya sa mahaifinki d'aukan zafi har hakan ta shafeni, na yarda kaddararki kenan Aisha sede a yanzu ba yadda na iya dole in taya mahaifinki nufinshi sbd abubuwan dake kuma faruwa tsakaninmu na saka en uwanki tsananki Aisha ban da yadda zanyi dole ke zaki hakura".

Mikewa nayi zaune tace "ko mai tsanani Aisha kika sake yunkurin cutar da kanki bazan ta'ba yafe miki ba" nace "kiyi hakuri bazan sake ba" kaina ta shafa tana me Mikewa se ga hajja ta shigo masifa ta hau ni dashi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ban tankata ba haka kuma banyi kuka ba sbd ni yanzu kuma zuciyata ai ta riga ta bushe, babu d'igon hawaye cikinta.

Bayan mama ta sallameni muka wuce gida da hajja d'akinta ta kaini ta kwantar don har lokacin bani da wani kuzari, chan yamma se ga sallaman yaya mujeeb Saif na biye dashi a Baya, hajja tayi musu maraba ganin shi da bako, zama sukayi ya nuna mata Saif yace "hajja wurin Aisha yazo tun tafiyarta kullum se ya zo Toh shine yau da yazo naga kuma ta dawo be kamata in hanashi ganinta ba" hajja tace "sannu bawan Allah ko lafiya kake zuwa kullum nemanta bayan bamu sanka a matsayin maneminta ba?" Murmushi ya saki yace "hajja sonta nake so na tsakani da Allah kuma auren ta zanyi".

Wara idanu sukayi daga hajja har ya mujeeb sukace "so??" Murmushi yayi ganin yadda suka razana yace "ban sani ba ko an mata miji amma wallahi har kasan zuciyata nake son Aisha zan iya zama da ita ko cikin wani irin hali" hajja tace "amma d'annan ka san abinda ke faruwa kuwa?" Yace "na sani a hakan nake sonta na tabbatar bata da laifi a abinda yake faruwa In har zaku tsaya kuji ta bakinta In har kun yarda da ita kenan, ni na yarda da ita duk abinda ta fad'a hakan ne ko da kuwa karyace bare ma na san bazatayi karya ba".

Ha'ba hajja ta dafe tana furta "ikon Allah, ikon gaske" Mikewa tayi tace "bari In turo maka ita dukda bata da lafiya" tayi maganan tana shiga d'akinta Mikewa ya mujeeb yayi ya fice yana cewa "In kun gama Ina waje" murmushi kawai yayi dukda ya mujeeb ze girme mishi amma shi ya d'auke shi kaman aboki, a hankali nake tafiya kaina kasa tun kan na karaso na san ana kallona jin kaifin idanunshi kaina zama nayi ina me kin kallonshi.

"Wannan yanayi be kamaci kyakyawar fuskan nan ba haba sarauniyar mata ke da na sanki da wasa da dariya da kuma tsokana" d'agowa nayi na kalleshi se kawai na fashe da kuka, Mikewa yayi yazo ya tsuguna gabana nasiha ya fara min akan kaddara da kar'barshi Sannan ya min fad'a kan fiya-fiyan da na sha sossai kan ya bi da lallashin fushin da Abba ke yi.

Nan take naji natsuwa ta saukarmin Saif shine mutum na farko da sam yaki yarda zan aikata duk abinda aka ce nayi, nan ya cigaba da kwantar min da hankali be tafi ba seda yaga murmushi kan fuskata wadda ni karan kaina se da nayi mamaki a tunanina bazan kara murmushi ko dariya ba har Abada, a haka hajja ta ci gaba da kula dani yayinda kullum se Saif yazo su ya mujeeb sun koma school da sati biyu na tashi da zazza'bi.

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now