🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
*Baya chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P13*
Zaune tayi a parlorn Bayan ta gama kwad'a sallamanta taji shiru, ta kai kusan mintuna ashirin zaune kan zuby ta fito sanye da wasu kananun kaya earpiece manne a kunnenta duka biyun tana tafiya tana taka rawa irin na wadda ya Samu duniya d'innan.
"Zubaida" yakumbo ta ambata sede bataji ba kila kuma taji iskanci ne kawai irin nata, seda yakumbo tayi motsi da karfi kan ta d'ago ta kalleta a banzance ta cire earpiece d'in kunne d'aya tace "au ashe kece" yakumbo tace "Eh d'iyannan nice nazo ya gidan?" A shekeke tace "klau" ta samu wuri ta zauna ta d'aura d'aya kan d'aya tare da cigaba da bin wakanta, sakaka yakumbo tayi tana kallonta a hankali tace "to kode diyarga bata ganeni bane" gyaran murya tayi tace."Nace ba!!!" Ko sake dubanta zuby batayi ba bare ta san tana magana seda ta d'aga murya tace "zubaida" kallonta tayi tana d'aga gira tace "ya Ina hutawata zaki zo kina min ihu aka Malama me kike bukata ne?" Da mamaki yakumbo tace "yanzu en nan ki dubi tsabar idona kice Ina miki ihu a ka?" Tace "to meye kike min in ba ihu ba mutum na hutawarshi In wurina kikazo na gode se anjima, In kuwa wurin me gidan kikazo wato d'anki to bacci yake In kuma ya tashi Abuja zamu wuce bashi da lokacinki".
Tsabar mamaki yakumbo ta kasa magana se kallo da take binta dashi Anya wannan zubaidace ba chanza ta akayi ba out of words tace "dama haka kike?" Wani irin dariya tayi kan tace "mene? Ai kad'an ma kennan zuby tafi haka yarinya, kinga tashi ki bar min gida ko zaki kwana gidan nan in ban ga dama ba ba ganin babynah zakiyi ba kin gane?".Sallallami yakumbo ta fara "me zan gani ni Hansatu?" Mikewa zuby tayi ta nuna mata kofa "fita kuma karki kara zuwar min gida ba gayyata" sakaka haka yakumbo tayi gwanin tausayi kan ta mike harara zuby ta kuma danna mata tace "Ai In bakayi sharar massallaci ba kya yi na kasuwa fita nace!!!" A sa'bule yakumbo ta fito tana kuka haka ta samu wuri kofan gidan ta zauna taci gaba da kuka kaman karamar yarinya, seda ta fi awa biyu nan kan taji motsin bud'e gate da sauri ta mike.
Aiko zubyce hakimce gefen Saif sanye da rantsatsiyar arab gown shi kuwa kananan kaya ce jikinshi hankalinshi na ga hanya be kula sam da yakumbonba yayinda zuby kuwa sarai ta ganta sede kashe mata ido da tayi suka wuce a guje, hannu biyu yakumbo ta d'aura a kai a fili ta furta "na kashe kaina".
*********
Tayi ma kanta Alkawari In Shaa Allahu ta dena sawa kanta damuwar Saif abinda ta sani shine bazata kashe kanta a banza ba tabbas In ta mutu a yanzu shi bashi da asara dukda dole ya dameta amma ya ta iya? Allah ya riga ya kaddaro mata hakan zata ci gaba da zama a gidanta cikin rufin asiri In har ba sakinta yayi ba.
Zata ci gaba da mishi adu'a har Allah ya ganar dashi In me ganewa ne dukda ta san haka kawai ruwa baya tsami banza, sede dayake ance zato zunubi ko ta fara tunanin wani abin daban zatayi auziyya taci gaba da abinda take, yanzu yaranta sune top priority d'inta, babban matsalanta rashin aikin yi tabbas itama tayi ganganci da ta yarda in sunyi aure ba aiki.
Dole ne ta nemi aikinyi sbd bata ga alamun ze cigaba da yi musu hidiman kud'i kaman da ba and more over ATM card d'inshi da take rikewa ba wani abun kirki a yadda de suka saba rayuwarsu na yau da kullum cikin wadata, Sannan babban damuwanta yaran sun fara damuwa da rashin magana da mahaifin nasu ita kanta dauriya da karfin hali kawai take.
*******
Yakumbo kuwa ganin abunda ya faru yasa ta fara dana sanin abubuwan da tayiwa Aisha sede aka ce dana sani keyace gashi bazata iya fad'in ma kowa ba sbd tsoron kar ayi mata dariya, sede ta tabbatar ko ba jima ko ba dad'e se kowa ya sani tunda shine karfinsu a gidan sulaiman ba aiki ya samu ba bare ya ci gaba da kula dasu Sannan a yadda take kuntatawa mahaifiyarshi tun Suna yara ta san ba lallai ya had'a da ita wurin taimakon ba.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰