RUWAN SAMA......

496 53 3
                                    


      🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
   *Baya Chanza d'and'anon teku*

       *Fatima Muhammad Gurin*
    **Gureenjo6763 on wattpad**

          'Yar Mutan Adamawa

    *P23*

"Mama dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dena d'aga hankalinki tunda Shaati ta 'bace yau sati guda kenan kinki kwantar da hankalinki bare lafiya ta samu, ita kanta Shaatin bazata so ta dawo ta ganki a wannan hali ba" fadila ke wannan maganan a yayinda yaran suka zagayeta kwance a gadon asibiti Don ciwon yafi karfin gida.

A wahale Mama tace "taya 'yata zata 'bata da ciki ni uwa in kwanta inyi bacci hankali kwance a wannan zamanin na san wani irin hannu take? Sannan me laifinta? Hakuri? Juriya? Ko kuma karfin kaddara da ta fi ku? Ciwon nan ya jima yana damuna sbd hankalina be ta'ba kwanciya ba tun bayan abinda ya sameta, sbd kun d'auki karan tsana kun d'aura mata bayan kokarin da takeyi wurin gani ta koma normal rayuwanta amma hakan ya gagara gareku, kwarai da gaske nayi mamaki sbd ba haka na tashe ku ba, ban gina gidana kaman gidan kafurai ba akwai so, shakuwa da tausayin juna tsakaninku me yasa kuka mata haka? Me yasa kuka banzartar da rayuwanta? Ku tayiwa laifi ko mahaliccinta? Kun ta'ba zama kunce Aisha bamu labarin abunda ya faru tunda tace Isma'il ne kuka karyatata kuka watse......" kuka ne ya ci karfin mama dama damuwan na nan dankare a zuciyarta yanzu ne yake fitowa a hankali.

Duk Shiru sukayi cikin damuwa tabbas In Aisha bata kashe mahaifiyarsu ba abinda suka jima sunayi ba tare da sun san yana damunta sossai ba ze kasheta hameed da yafi kowa d'aukan zafi shide har yanzu be ga aibin abinda yayi ma shaati ba tunda ita ta ja komai, yayinda fadila da meena duk jikinsu yayi sanyi suka fara da na sani majeed kam runtse idanu yayi cikin wasi wasi har ranshi yana kewar kanwartashi dukda sun fi shakuwa da hameed amma ita me sonsu ce tsakani da Allah.

Mujeeb da dama shi be ta'ba tsanan kanwar tashi ba yace "Mama menene takamanmman labarin ne da baku fad'awa kowa ba daga ke har Abba?" Shiru Mama tayi kan tiryan tiryan ta fara basu labarin abinda ya faru da shedar shaati kan ta gama fadila da meena kuka sha'be sha'be yayinda mujeeb da majeed idanunsu suka kad'a suka jajir hameed kam ya rasa me ze d'auka karyace ko gaskiyace shaati ta fad'awa iyayensu dukda shine best friend d'inta kan lalacewan komai.

Sun jima cikin jimami kan Fadeelah Tace "Aisha pls ki yafeni, ban kasance sister da zata yi supporting d'inki a komai da komai ba, hakan nan ban zame miki kafad'a da zaki yi kukan duk wani damuwanki ba se na zama ni ce me saki kukan ni ce nafi kowa uzzura miki a mafi munin lokutan rayuwarki ina ma ina ma, khaih kaicona Allah ubangiji ya bayyanaki karki mutu baki yafemana ba Aisha" ta karasa da kuka sossai, meena ma Hawayenta ta share tace "Mama dan Allah kiyi hakuri zamu gyara In Shaa Allahu kiyi fighting situation d'innan mama sbd ki sake ganin had'in kanmu a rayuwa".

Majeed yace "sorry mamah we are really sorry for letting you all alone in this situation me makon mu tausaya muku se mukayi adding salt into it pls find a place in your heart to forgive us" hameed da har yanzu zuciyarshi be gama aminta ba yace "we are sorry" mujeeb yace "Mama I promise you in har Ismail makes Aisha suffer and go through this hardness all alone court ce zata rabamu I will definitely act as eldest son of this family ki yafe musu ki sa Mana albarka".

Ajiyar zuciya ta sauke tana share fuskan ta tace "Allah yayi muku albarka ya bayyanamin er uwarku, Allah ubangiji ya yafe mana gabad'aya" suka amsa da Ameen. Abba da ya d'an jima jikin kofan ya karaso yana amsawa da "Ameen" shima, Mama ta dubeshi ta tabbatar shima kokari yakeyi amma yana jinya a tsaye cikin sanyi tace "akwai wani labarine?" Yace "babu, sede commissioner of police yace he will put all his effort wurin ganin an bincikota da yardar Allah" wayan Abba ne ya fara kara dubawa yayi se yaga abokinshi malam sulaiman d'agawa yayi suka gaisa inda yake tambayanshi situation na Aisha yanzu.

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now