🍇💦RUWAN SAMA.....💦🍇
*Baya chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*Gureenjo novels group bani da kamarku ina matukar kaunanku har raina🥰 kuyi hakuri kwana biyu bana samun yi ma kowa reply d'in comment d'inshi sbd halin da nake ciki ku cigaba da tayani da adu'a kaman yadda kukeyi yanzu Ina ganin each and every comments d'inku and wallahi I really appreciate shi kuma ke sa min kwarin gwiwan yi muku ko da kad'an ne na gode❤️❤️ Son so🥰🥰*
*P14*
Ta samu ta sayar da golds d'in cikin sa'a sbd gold da suka hau, kayan abinci ta kara musu sossai kan ta wuce direct bank taje ta biya kud'in makarantar su na term d'in da suke cikin tana fata Allah ubangiji ya mata hanya ta biya sauran kan next term a kuma koransu, bayan ta biya ta wuto gida tana jin daad'i har cikin ranta.
Tana parking taji wayanta na ringing da sauri ta duba a zatonta Saif ne se taga mamah, d'agawa tayi da murnanta ta d'aga tabbas ajiye kadara daad'ine da shi, "Assalamu Alaikum mamah" Tace "Wa'alaikissalam warahmatullah sannu madam kila gida zan biyoki Awo ko?" Wara idanunta tayi tace "laaa wallahi shap na mance da wani awo, gobe in Allah ya kaimu in yaran sun wuce school zan zo" Mamah tace "Toh shikenan ki gaidasu" Tace "zasuji bye".
Da murna suka tare ta ganin ta shigo tana dariya rungumesu tayi gabad'aya tace "gobe se school na biya ga taller d'inku" murna suka fara yasmin tace "maami paapa ne ya turo?" Fara'arta ne ya d'an disashe se kuma ta saki murmushi tana gyad'a kai, tace "guess what are we going to eat today?" Neeha tace "spaghetti" sameer yace "rice and beans" Yasmin Tace "as usual" wato rice and beans d'in, Arwa tace "jollof rice" duk girgiza kai tayi suka had'a baki wurin cewa "what then!!!" Cikin tunani, tace "rice and stew" waro idanu sukayi neeha tace "with meat?" Ta gyad'a kai se gasu suna murna har seda hawaye ya gangaro mata da ubanku da arzikinshi amma ace rabon da su ci abinci me ma'ana me suna abinci yadda suka saba ci daa ta manta.
A 'boye ta goge hawayen nata tana cire hijab d'inta ta nufi kitchen yasmin da Arwa suka bi ta yayinda sameer da neeha suka ci gaba da kallonsu da ta samesu sunayi, 'bare maggi, daka garlic, miko mai miko kaza da haka suka taimaka mata wurin girkin nata nan da nan suka gama, sunayi suna hira daga kitchen mota suka koma suka tattaro sayayyan da tayo suka shirya a store Arwa ta share kitchen da store d'in.
Wanka duk sukayi suka sa kayan shan iska kan Arwa ta zubo musu abincin dukkansu a tray guda da spoons a parlor suka baje sukaci a natse yasmin ta tattara sun d'an huta kan aka kira sallah suka gabatar ta kwanta abinta ta barsu suna kallo, bata tashi ba se la'asar ta kuma watsa ruwa sbd wutan da aka d'auke gashi ana zuba zafi bayan tayi sallah ta fito basa nan alamu sun nuna sun wuce islamiya da 2 yayi dama ta sabarwa Arwa yi musu shirin islamiya da sa su a gaba su tafi tunda ba wani nisa ne da shi ba, ammafa da ubansu na nan a mota ake kaisu a d'auko su.
***********
"Wallahi gaskiyace dae bazan dena fad'a maka ba Saif wai kana cikin hankalinka kuwa? Shaatin kake cewa baka da lokacinta?" Cikin masifa yassar ke wannan masifan zaune a office d'in Saif, kuma had'a rai Saif yayi yace "wai Ina ruwanka da rayuwata ne? Matarkace ko matata? Me naka a ciki? bani da lokacin zuwa kaduna Sannan bani da time d'insu se me? Me ka isa yi Min?" Shima ya mayar cikin masifa.
Yassar yace "ko don su yakumbo bazaka iya zuwa kaduna ba? Wai anya kuwa Saif? su neeha yaushe rabon da ka kira kaji lafiyansu? Anya kuwa kana son gamawa da duniya lafiya? Ina zaka kai hakkin yakumbo da na Yaran nan In ka cigaba da musu haka? Sannan Aisha....." katseshi Saif yayi cikin d'aga murya "Ba ruwanka it's my life I have the right to live yadda na so, me naka? Uhmm I hate hearing everything about kaduna so please spare my life and get the hell outta my office and life".
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰