RUWAN SAMA.......

579 61 9
                                    


     🍇💦RUWAN SAMA........💦🍇
  *Baya Chanza d'and'anon teku*

      *Fatima Muhammad Gurin*
   **Gureenjo6763 on Wattpad**

      'Yar Mutan Adamawa

    *P31*

Kwanan su Mama biyu maiduguri kan suka juya da shaati da kusan akwatunanta set bayan bata zo da ko kaya d'aya ba, ta tafi ta bar su jidda da kewa haka suma sun tafi da kewansu sossai suna masu yabon karamci da mutunci irin na su baba, bayan haka baba ya basu duk wasu adu'o'i ya kuma tabbatar kar shaati ta dena anfani da magungunan da ya bata.

Hajja da yaya suka had'a su da turaruka na d'aki, na jiki, na tsugunu, humras masu bala'in kamshi, da lafayas, shaati seda tayi kukan rabuwa dasu sbd bazata ta'ba mantawa da su ba adu'arta baze ta'ba katsewa daga kansu ba se ta dena numfashi mamaki take yadda tun ranar suna har yau bata kuma ganin Shareef ba sede taji suna waya da jidda, ta so su ke'be ko yaya  ne ta mishi godiya sede hakan be samu ba tunda be dawo ba kuma bata da waya.

Ko su Abba da suka so ganin shi hakan be yiwu ba sbd daga yobe gaba yayi yace kuma it was urgent ba yadda za'ayi ya juyo sede sukayi waya da Abban ya kuma kar'bi contact d'inshi, suna sauka Airport ta bud'e baki cike da tsantsar mamaki take kallon wai waenda suka zo tarbansu Ya hameed, ya mujeeb, ya majeed, ya meena da ya fadeela se Anty tala da namesake d'inta, se ma ta rasa wa za ta fara runguma ganin dukkansu fuskokinsu kwance da murmushin farin cikin ganinta.

Kawai se ta tsaya chak ta fara hawaye ya majeed da ya mujeeb ne suka nufota tare da rike hannayenta suna kallon irin kyau da yalkin da jikinta ke zubawa dukda ta d'anyi duhun jego amma tayi matukar kyau, kawai se ta rungumesu su biyun tana kara sautin kukanta ya majeed yace cikin sanyin murya "is Ohk sis" ya mujeeb yace "welcome home dear" kai kawai take gyad'amusu tana murmushi da hawaye har suka saketa ya meena da ya fadeela da suka karaso suka rungumeta.

Se suma suka saka kuka sossai suke kuka seda mama ta ce "a Airport fa kuke hankalin mutane na dawowa kanku" saketa sukayi suka had'a bakin cewa "we are sorry lil, we are so sorry" murmushi ta musu tace "thank you for being your real self's I missed you two so badly, I missed everything about us da har na fara mantawa almost 9yrs" girgiza mata kai sukayi ta saki hannunsu tana murmushi ta kalli ya tala da namesake cikin fara'a da Hawaye suka rungumeta se taji Saif a zuciyarta ji take kewarshi na taso mata, da sauri ta kawar da wannan tunanin ta d'ago tana murmushi ta kalli hameed tace "hey bro" murmushi kawai yayi.

Kallon ya fadeela da ta kar'bi Shareef daga hannun hajja da ta kumbura fuska tana jiran ace mata kyat ta fashe tace "masha Allah lil wannan kyakyawar babyn" meena tace "photocopy d'in Saif wallahi" namesake ta leka fuskanshi tana cewa "ya sunanshi?" Mama tace "Shareef her life savior" ras haka gabanta ya fad'i jin abinda mama tace, se tayi saurin sakan murmushi ta kalli hajja da bata motsa ba Bayan sun fara tafiya tace "hajja kalau kuwa naga ki......" bata karasa ba hajja ta cha'be "an tsaya d'in nace an tsaya d'in, dukkanku zaku lalla'bo ku sameni lullu'be kan gadona ne wallahi se nayi maganinku d'aid'ai ni zaku mayar saniyar Ware?".

Abba da tuni yana jikin motan mujeeb yana waya da baba, ya juya yana kallonsu jin da karfi hajja tayi maganan murmushi yayi yayinda su kuwa suka saki dariya majeed yace "kajimin tsohuwa yanzu fisabilillahi waya mai dake saniyar Ware?" Dakuwa ta mishi tana nuna Abba tace "ka ga chan tsohon ba de ni ba, ko wannan ta gabanka a gabana kuka nuna kunfi son er uwarku a kaina na hau wannan karfen ta bature na sauka lafiya ba wadda ya iya ce min barka, Ai wandon roba nake daidai nake da kugun kowa" (@hauwa Ibrahim bahaushiya manya to an gode da wannan hausan) ta fad'a tana kwafa.

Dafe baki sukayi shaati tana dariya tace "to kuwa in har Abba tsoho ne kenan ke kuwa tsohuwar tsohuwa za'a ce miki" binta tayi da sauri ta zagaya ta fad'a motar ya mujeeb tana locking duk dariya suka fashe dashi har Mama murmushi take yayinda Abba ya d'an sha kunu dukda dariyar dake son kwace mishi shima ganin ta zage tana ta masifa don an ce mata tsohuwa da kyar Abba ya lalla'bata ta shiga motar hameed kan shaati ta bud'ewa mujeeb motan tana kan dariya har lokacin.

RUWAN SAMA........Where stories live. Discover now