🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P39*
"Assalamu alaikum" ta furta tana me lumshe idanu, wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke da har seda taji, muryanta yake ji yana ratsa mishi zuciya he missed her like crazy, kuma sallaman tayi tana me sauraren jiran amsa a hankali ya amsa mata "wa'alaikissalam warahmatullah" jin muryanshi ne yasa cikin azama ta cire wayan zata kashe yayi saurin cewa "In kina yiwa Allah da manzonsa karki kashe wayan nan" mayarwa kunnenta tayi, cikin karyayyiyar murya yace "how have you been?" Shiru ta mishi.
Yace "Aisha na san bani da bakin da zan iya baki hakuri sede ki sani wallahil azeem cikin hankalina dae bazan ta'ba iya aikata rabin abinda na aikata ba, I didn't know what came over me, ban ta'ba yarda asiri ana iya samunshi na gaskiya yanzu a wannan zamanin ba se gashi ya hau kaina har na wulakanta mace mafi soyuwa a raina, duk abinda nayi miki na san ke a wurinki ya riga ya wuce but ni har yanzu zafinsu nake ji har cikin raina kaman ni akayiwa, Aisha I loved you, I love you and I will keep loving you to eternity, Ina so ki san RUWAN SAMA Baya Chanza wa ruwan kogi d'and'ano, kaman yadda babu abinda ya isa ya Chanza d'and'anon sonki a cikin zuciyata, za'ayi RUWAN SAMA da na tabbatar se ya wanke duk wani ta'bon bakina a zuciyarki In Shaa Allahu" ajiyar zuciya ta sauke kan tace "excuse me!!" Ta kashe wayanta.
Lumshe idanunshi da sukayi ja yayi yana tunani wani wahalan kuma ta sha a randa ya saketa sbd tsanan nata gareshi yayi yawa ya dae san ta 'bata tunda har gidanshi aka zo nemanta, be san yadda ta haihu ba, be san me ta samu ba d'anshi guda be san ko da sunanshi ba, da karfi ya runtse idanunshi yana me d'aura hannayenshi saman kanshi abin da ciwo sede hakuri shine magani se adu'a mikewa yayi ya d'auro alwala ya fara nafilfili yana rokon Allah ya sassauta mata.
Ta 'bangarenta kuwa sossai maganganunshi suka tsaya mata a rai sede a lokacin tayi iya yinta ta ciresu ta watsar ta gyara kwanciyarta se bacci hankalinta kwance.
Ta 'bangaren Shareef yana isa jidda na farkawa a matukar tsorace take kallon jikinta ganin ba inda ta kone yasa ta sauke wani wawan ajiyar zuciya tana furta "Alhamdulillah" yaya dake zaune ta kalleta tana murmushi tace "Allah shine abin godiya kin tashi?" Kai kawai ta gyad'a tana tuna yadda wutan nan ya tashi, a daidai lokacin ya turo kofar wadda yana shigowa yaya ta mike ta fice, tana bada baya ya karaso cikin sassarfa ya rungumeta cikin jikinshi kaman wani ze kwaceta har seda ta d'anyi kara kan ya sassauta ajiyar zuciya kuwa ya sauke sunfi goma idanunshi a lumshe ya samu kunnenta "thanks for being Alive lil".
Murmushi ta saki tana d'agowa tace "Da na mutu fah?" Yace "I would have regretted not showing you how much I love you, I would have regretted duk wasu laifi da na miki duniya, oh Allah I can't even imagine you dying now" kissing lips d'inshi tayi tace "Alhamdulillah" Ai kallon kinyi kad'an ya mata kan ya chabke Lips d'in nata ya fara mata wata kalar mahaukaciyar kiss🚶♀️🚶♀️🚶♀️
***********
Washegari da safe Shaati na tashi kawai taga an turo mata sako, bata duba ba sbd ta bada saif ne, ta cigaba da abinda take bayan ta gama musu breakfast kaman yadda ta saba tayi wanka ta shirya kan ta d'auki wayan, miss calls hud'u ta gani na wannan numbern da Saif ya kirata jiya bata bi ta kai ba don ba kira zatayi ba ya ci sa'a ma da batayi blocking contact d'in ba.
Abinda taga an turo mata yasa ta mikewa tsaye fuskanta na cika da farin ciki ba kaman a da da ta cunne ba, da gudu ta fita kaman yarinya tana kiran "Abba! Abba!! Abba!!" Fitowanshi kenan ze zauna dining yace "uwata are we safe irin wannan kira?" Tace "Abba admission na samu" shi da mama sukace "Alhamdulillah congratulations dear" cikin farin ciki tace "thank you" Abba yace "to zo zauna ki ci abinci kar farin ciki ya sa cikin naki cika" Tace "Ai ma ya sa Abba Ina zuwa" ta ruga d'aki mama tana girgiza kai Tace "Allah ya shirya mutum da 'ya'ya amma har yanzu ya gaza hankali?" Abba na dariya yace "ke kyaleta ko ke aka ajiyeki gaban umma haka zakiyi ehe" dariya tayi kawai tana cigaba da serving d'insu.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰