🍇💦RUWAN SAMA...💦🍇
*•Baya Chanza d'and'anon teku•***Fatima Muhammad Gureen**
*Gureenjo6763 on wattpad*'yar Mutan Adamawa
*P4*
Juyi kawai take akan yaloluwar katifarta idanunta na kallon azaran d'akin da ko arzikin silin be samu ba tsaki taja tare da kallon wayan hannunta da ya bani asalin mamaki wadda ya kasance iPhone 11 pro max, ta kuma jan tsaki tare da mikewa daga ita se zani d'aurin kirji yayinda kanta ba d'ankwali kitson attachment d'intan nan har kan d'uwawu fitowa tayi tana fad'a da kofar yaloluwar katako na d'akin tana cewa "ni Wallahi na gaji haba talauci har yayiwa mutum katutu In ba samarina suka bani kud'i ba da se ni ma inci wannan bakar tuwon da inna ke ci, shi baba ba ruwanshi kullum yana yawon cin abinci a waje".
Tsaki ta kuma ja tana cewa "Allah yau se an yi ta ta kare baba se ka san yadda kayi da ni akan wadda nake so" tareta mamanta tayi a kofar zaure ita innan na shigowa yayinda ita kuma take fita "a'a Lafiya zubaida Ina zuwa a haka?" Cewar inna, juya keya tayi tace "wurin baba zani in nima se na biyashi ne kan ya min aiki zan ji haba tun yaushe nake binshi akan wadda nake so na gaji da zaman akwalan gidan nan wallahi".
Ta'be baki inna tayi tace "ku kuka jiyo" tana wucewa taji zubaida na cewa "idan ai na auri me kud'in ku zaku dinga min tururuwa a kofar gida" ta shige zauren, baban na zaune wata mata durkushe gabanshi tana ajiye mishi makudan kud'i tare da mikewa tace "to me yankan wuka dan Allah inga aiki da cikawa na sanka sarai bazaka watsan kasa a ido ba" dariya baba yayi yace "karki damu mune fah zakiga aiki jeki kawai".
Ficewa tayi yayinda baban yayi saurin kwashe kud'ad'en ya turasu cikin babban riganshi ta'be baki zuby tayi tana zama tace "baba ya batun aiki na? Ni fah na gaji wallahi na gaji da rayuwar bakar gidan nan kayi min aiki a kan wadda nake so ko In san matakin da zan d'auka wadda baze muku dad'i ba ehe".Hararanta yayi yana cewa "Toh fitsararriya marar kunya kin san bana aikin banza In har kina son aiki ajiye kud'i" itama rama hararinta tayi kan tace "idan fah kayi aikin nan kune da riba amma ba komai zan biya amma ka tabbatar na shiga gidan nan karku saka ran samun ko biyar" a zuciye ta mike ta koma d'akinta ta d'auki tsadaddiyar handbag d'inta ta bud'e ta d'auko rafar 500 ta juya ta koma zauren ta dangwarar mishi washe baki yayi yana cewa "yanzu kike zance d'iyar nan ya ma kika ce sunanshi?".
"Saif shamsuddeen suraj".*******
"maamah! Mamaah!! Maamah!!" Farar dattijuwar dake zaune saman sofa idanunta sanye da medicated glass tace "oh ni fad'imatu zasu karar da sunan In shigesu" dariya dattijon da shima ya kasance fari sol yayi yace "ah gwara ai ko zasu samu shiga a wurin mijin nasu da kika kwace" ya karasa yana dariya itama dariya tayi a daidai lokacin da Arwa, Yasmin da neeha suka shigo parlorn suka fad'a jikinta suna dariya.
"Kai me haka? Maza ku sauka tunda kuma ba wadda ya karya muku kafata" Shaati da ta shigo hannunta rike dana sameer ta fad'i, sauka sukayi suna turo baki kallon Abba da sukayi yasa suka washe baki Arwa tace "laa Abba yaushe ka dawo?" Yace "d'azunan khadijatul kubra" tana son sunan hakan yasa ta kuma washe baki tace "toh Abba sannu da hanya ina yini?" Yace "Lafiya kalau ya makaranta?" Tace "lafiya Abba" yasmin tace "ni ba'a ganni ba ai" tana turo baki.
Yace "ah na isa? Me sunan uwar muminai, uwata kuma uwar gidata?" Mamah tace "Lallai Alhaji ni kuma fah?" Dariya sukayi a sanda neeha ta koma wurin shaati dake zaune kasa tace "maami Abbanki wai baya so na" ta kare da turo baki, Abba yace "na shigesu fad'imatu sharri zaki min?" Suka kuma yin dariya shaati tace "Abba kyale yaran nan ka biye musu se su saka surutu Ina yini?" Yace "Lafiya kalau uwata ya gidan naki? Tace "Lafiya kalau ashe kuma mun samu karuwa" yace "eh" Tace "Toh Allah ubangiji ya raya" ya amsa da "Ameen thumma Ameen" juyawa tayi ga maamah tace "maamah mun yini Lafiya?" Tace "Alhamdulillah, kai miskili kafi mahaukaci ban haushi baka iya gaisuwa bane?".
Abba yace "ke kuwa wai miskili kina ganin yaro kyakyawa fari sol son kowa kin wadda ya rasa zo nan sameeru" ta'be baki maamah tayi tace "ku kuka jiyo".
Mikewa shaati tayi tace "bari In je wurin me jegon" maamah tace "Toh se kin juyo akwai maganan da nake so muyi kuwa" Tace "Toh" tana fita dayake gidansun katoton family house ne kannen babanta da yayyunsu da matansu da 'ya'yansu Sannan a cikin 'ya'yansun ma akwai wadda sukayi aure aka ware musu part part duk nan cikin gidan sede gini ne irin na zamani ko wanni part da irin colour d'insu ginin wajen gidan ne kawai aka zagaye da color guda wato milk haka gate d'in ma katoton iron get ne milk color.
'Dakinsu ne kawai babu wadda yayi aure a cikin gidan gari suka shiga abinsu, sbd matsalolin gidan yawa ne dashi ga shegen kishi irin na balbali da suka d'aurawa kansu.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰