🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P24*
"Assalamu Alaikum" ta kutsa kanta cikin gidan bakinta d'auke da sallama zugum zugum ta gansu Anty tala, yakumbo, innani, sulaiman, bappa, Kawu da hajar zaune duk matan sunyi kuka sun gaji, sun buga tagumi har mazan sun rasa abin fad'a, da kyar innani tayi mata bismillah gefen taburman da suke zaune zama tayi tana gaida su, a tare duk suka amsa tace "ko lafiya?" Yakumbo cikin jimami tace "Ina fa lafiya, ni kam ban san wani irin ibtila'i bane ke fad'owa yaran nan abin yayi yawa yanzu wannan tashin hankalin da muka rasa ta Ina zamu fara kamamishi shi yafi komai ciwo da zafi".
Mama tace "subhanallah Allah shine ze mana maganin komai, shi zamu mikawa duk ragamar rayuwarmu sannan bawan da ba'a jarabceshi ba ai be cika me imani ba, kun manta kar'ban kaddara me kyau ko marar kyau yana daga cikin shika shikan imani? Wani abun ne kuma ya kuma faruwa da saifullahi ko yaran?" Innani tace "talatuce....." se kuma tayi shiru, sulaiman ya karasa da "baban su hajar ne aka gano ashe shi ya sace ta ya mata fyad'e sbd bokanshi yace muddin ya sadu da ershi mace to fah se yaci wannan takarar na gomna da ya tsaya".
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun, la haula wala quwwata illa billah, hasbunallahu wani'imal wakeel" Mama ta jerosu a tare hawaye na gangaro mata ganin hajar d'in duk ta firgice tayi wani iri bata magana kwata kwata, wannan duniya ina zaki damu? Ashe Don kawai mulki na duniya mutum ze iya salwantar da rayuwar ershi ta hanyar sa'bawa mahallicinshi ta mummunan hanya? Me yarinya hajar d'innan ta sani da ya za'bi tozartata da rayuwarta, kuka sossai Mama ta saka cikin jimami da tarradaddin abinda duniya ta zama yanzu, ya tala da dama kukan nata be tsaya ba taci gaba da yinshi daga kaji kukan zaka san na tsantsar bakin ciki ne da zallar damuwa da ta rasa yadda zatayi dashi.
Seda Mama tayi kuka sossai kan ta share fuskanta tare da d'agowa tace "to yanzu me aka mishi?" Bappa yace "hmm da matasan unguwan suka so banka mishi wuta amma se hukuma sukayi saurin isowa suka kamashi kan su kamashin ma ya haukace tuburan se fad'e fad'en duk wasu abubuwan da yayi yake tayi" hakuri mama ta ba Anty tala, girgiza kai Anty tala tayi cikin tashin hankali tace "babban abinda yafi damuna shine cikin da yarinyar nan da bata wuce shekara 14 ba ta samu ya zanyi dashi? Me zan ce mata? Me zan cewa mijin da en uwan da zata aura? Ashe duk ka ganka cikin wani rahama na ubangiji ya kamata ka gode mishi ba ka butulce mishi ba? Kenan duk abubuwan da muka yiwa Aisha (shaati) se anyiwa hajar ba tare da anyi la'akari da irin tata kaddarar ba?"
Kuka sossai yaci karfinta danasanin abubuwan da suka dinga yiwa shaati na kamata Lallai duniya kenan, (ashe kenan babu kyau duk wani kaddara da ya fad'arwa mutum ka dinga hantararshi da hakan kana yamad'id'i dashi ba, baka san ta inda naka kaddaran ze zo ba, Allah ya sa kaddararmu ta kasance me kyau) duk jikinsu yayi matukar sanyi musamman yakumbo da ta dinga tayasu Allah ya taimaketa ta nemi yafiyar shaati kan 'bacewarta amma tabbas sun san sunyi matukar kuntatawa rayuwarta.
Mama ne ta yanke shirun da "Ina sauran yaran suke?" Innani tace "suna shiyata da Aisha itace me karfin halin d'auke musu hankali amma Arham kam ya rufe kanshi tuntuni yaki bud'ewa se kuka yakeyi" Mama tace "yana Ina?" Innani tace "yana d'akin sulaiman" Mikewa mama tayi ta karasa inda innani ta nuna mata da hannu a matsayin d'akin sulaiman a kofan ta tsaya ta fara kiran sunanshi shiru tayi ta d'aura da "na san kana jina Arham ka saurara kaji abinda zan fad'a maka.
(Ga masu cewa be kamata komai ya faru ga Aisha ba sbd adu'o'in da takeyi ku saurara kuji da kyau Adu'a baya hana kaddararka afkuwa gareka sede yana iya sassautawa ko ya saukaka maka)
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰