🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P37*
Wani kasalallen murmushi ta saki tare da kallon ya reef kaman bata ga wani Saif ba tace "ya reef gyalena gyalena ze fad'i" shi kuwa da azama ya sa hannu a kan gyalen yana gyaramata daidai lokacin ta cewa suhail "sorry suhail Ina zuwa I will get back to you" ganin tana kokarin fitowa ga waya a kunne ga kuma Shareef a hannu yasa ya saka hannunshi ya kar'bi lil Shareef d'in dake bacci ya makalashi kafad'a yana cewa "ke ma dai da rigima kike taya ga baby a hannu kina kokarin saukowa kuma kina amsa call. Yanzu In shareef ne ya fad'i ba gyale ba fa?" Shagwa'bewa tayi tana murmushi tace "sorry baza'a sake ba" shagala yayi da kallonta.
Aiko a kasan zuciyarta kuwa tunani take me ya kawo Saif kuma kofar gidansu? In har yana cikin hankalinshi ta tabbatar yanzu ya gama kuluwa sbd ya tsani wani namijin yaga shagwa'barta bayan shi, aiko kaman ta sani a lokacin da takeyiwa Shareef dramar ta Saif ji yayi kaman zuciyarshi zata fad'o kasa a take idanunshi suka kad'a sukayi jajir jijiyon kanshi suka mimmike, tabbas In tace zata auri wani bayan shi ya san wallahi mutuwa ze yi baze iya d'auka ba bare kuma irin Shareef da shima namijin gaske ne wadda In yace a yanzu ze baje mata kolin soyayyarshi wallahi se ta manta da wani Saif rayuwarta.
Da idanu ya bi su har suka shige shi Shareef be lura ba yayinda ita kuwa sarai ta san kallonsu yake se kara sakewa shareef murmushi take, Yasmin ce karshen fita sbd neman murfin ice cream d'inta da take kan ta fito kowa ya shige, a hankali ya tako zuwa jikin motan cikin sanyin murya yace "Yasmin" da sauri ta d'ago ta kalleshi ganin yadda idanunshi suka kad'a sukayi ja ba abinda ya fad'o mata se ranar da ya mari neeha har ta kusa suma cikin razana kar itama ya maretan sbd ranar ma haka idanunshi sukayi tayi saurin jan baya ze yi magana ina ta kwasa da gudu ta nufi gate.
Daidai lokacin Shareef ya kuma fitowa da sauri ya riketa yana cewa "lafiya yasmin?" Kuka ta fara tana nuna mishi Saif "papi ze d'auke ni ya kaini wurin Anty zubaidah and she's evil" kallon Saif yayi tabbas shine mahaifinsu sbd kammani a ranshi yace "ashe shima namiji ne" murmushi ya saki yace "karki damu ina nan ba inda ze kaiki kinji? Oya shiga gida" Da gudu ta shige gida shi kuwa Saif In aka ce a wurin hawaye ya fara to baze musa ba sbd reaction d'in yarinyar ya mugun firgitashi banda ma maganan shaati da ya gani da wani saurayi.
"Assalamu alaikum" Shareef ya furta yana mika mishi hannu a kasalance ya d'aga nashi sukayi musabaha, kan ya bud'e motanshi ya d'au abinda ze d'auka ya koma ciki ya bar Saif tsaye nan kaman an dasa shi har ga Allah yayi matukar bashi tausayi sede yanzu shaati ta zama allura cikin ruwa se me rabo ze iya d'auka, ko ma ta ganshi? Ya tambayi kanshi se kuma ya ta'be baki tare da d'aga kafad'a yana furta Ina ma ruwana.
Tana shiga gidan d'akinta ta wuce rike da shareef da shareef babba ya mika mata a kofar parlorn, a gado kawai ta ajiye yaron tana me fisge gyalen kanta safa da marwa ta fara tare da dunkule hannunta d'aya tana dukan tafin d'ayar, abubuwan da suka faru ne suke dawo mata bata san sadda kuka ya kwace mata ba tare da zamewa ta saka kanta tsakanin cinyoyinta tare da kara sautin kukanta.
Mama da taga wucewarta kuma taga kaman tana cikin tashin hankali se ta biyo bayanta dukda bata san me ya faru ba bata son katsalandan cikin al'amuran yarinyar tunda yanzu tayi girman da ta san fari da baki, ajiyar zuciya ta sauke ta fita tare da jan kofan a hankali.
Seda tayi kukanta ma'ishi kan ta mike ta shiga toilet ta wanke fuskanta, zuciyarta tunani daban daban, wanka kawai tayi ta fito ta shafa mai tare da zura material ta saka turban kanta, ba ita Zata yiwa Shareef abincin dare ba mama da lantanace so sai kawai ta kwanta ta d'auki wayanta ta danna kiran suhail gaisawa sukayi nan ya fara janta da hira cikin son sanin wacece ita, bata 'boye mishi ba ita bazawara ce me 'ya'ya har biyar, yayi matukar mamaki sbd jikinta be nuna hakan ba sam.
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰