🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇
*Baya Chanza d'and'anon teku**Fatima Muhammad Gurin*
**Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa
*P33*
Salati ya fara Ai guguwar nan na isa kanshi ya tsala ihu anan take a wurin ya haukace tuburan ya fita da gudu cikin wannan muguwar iskar.
A daidai lokacin da shaati ke kwance tana danna wayar da d'azu ya mujeeb ya sayo Mata shi hira sukeyi da jidda ta chat, a firgice ta mike zaune gabanta na tsananta fad'uwa sunan Allah ta fara ambata tana janyo Shareef jikinta rungumeshi tayi kam tana jin yadda zuciyarta ke luguden bugawa akan lips d'inta ta furta 'Saif'
**********
Zaune yake yana wani aiki a system a yayinda labulayen d'akin da yake yake d'an kad'awa sbd iskar da akeyi gabad'aya duniyar ce, kanshi yaji yayi mugun sarawa a take ya dafe yana ambaton Allah gabanshi ya ci gaba da luguden bugu yayinda hankalinshi gabad'aya ya nemi barin jikinshi, wani bala'e'en sanyi ya fara ji da sauri ya janyo remote d'in Ac ya kashe yana me dukunkunewa a bargo tare da runtse idanu wata zazzafar zazza'bi na saukar mai da kyar yake iya jan numfashi.
******
A daidai lokacin Zuby dake zaune cikin cell ta mike a firgice harshenta taji yana cika bakinta yana neman fitowa waje bata hankara ba tajishi kaman an tsinkashi se lilo yake a waje yana dilalar da miyau, kallon bakin take kokarin yi aiko se taji idanun sun fara ganin duhu bata iya kallon komai alhalin a bud'e suke ihu take kokarin yi se taji maganan ma baya fita a fili ta furta "na shiga uku me nake shirin gani" aiko se taji magan tata ma ba fitowa yake ba magana taci gaba dayi sede baya fita kwatakwata.
Haukacewa tayi ta rasa me zatayi wadda za'a ji a kawo mata d'auki se ta hau jijjiga karafunan cell d'in da iyakar karfinta tana wasu irin abubuwa dukda da hankalinta jikinta ba wai hauka tayi ba sede fa yadda takoma tana wasu irin abubuwa cikin tashin hankali.
*******
A daidai lokacin baba dake cikin tarradaddin kafanshi ya hantsilo ya fad'a kan kafan ba tare da ya sani ba yana shirin tsala ihu yaji ya kasa kaman a wasan koikoyo se ji yai yayi paralyzing a nan ya sheme ya kasa tashi.
A daidai lokacin aka tsuge da Ruwan sama me karfin bala'i wadda shine first Ruwan sama da ya sauko a farkon daminar shekarar, lumshe idanu shaati tayi tana jin ni'imar Allah na ratsata sbd bata rufe windows d'in d'akin ba, karan wayanta ne ya sata bud'e idanun ta zuba mishi gabanta ne ya fad'i welcome back tayi bata da number d'inshi saved one sede daga ganin numbern ta gane shine hawaye ne ya cika mata idanu, yau Saif ne ya d'aga waya ya kirata? Tayiwa kanta tambayar tana kallo har ya katse bata d'aga ba aka sake kira turo kofar da akayi yasa tayi saurin kifa wayar tana share hawayen fuskanta.
Tare da kirkiro murmushi tace "Mama In zo ne?" Mama da ta tsaya kallonta tace "hmm babanki ke kira" ta karasa tana fita, dukda ta tabbatar Mama taga hawayenta ta za'bi ta shareta tunda bata so ta gani ba, kawai se ta mike ta d'auki hijab ta sa ta fito parlor Abba na zaune yana kallon news sbd 9 da tayi ta kalla tace "sannu da gida Abba" yace "Yauwa uwata".
Zama tayi tana wasa da fingers d'inta seda ya gama karanta headline kan yace "Yauwa uwata dama na kiraki ne inji me kike sha'awar yi sbd zama hakan ba wani anfani ze miki ba ya kamata kiyi wani abin na anfanan kai kan ki samu wani mijin" dukar da kanta tayi tare da d'an nazari nan take ta d'ago "Abba makaranta nake so in koma" Shiru yayi cikin nazari shima kan yace "degree ko school of nursing d'in?" Cikin d'an jin daad'i sbd ta san ze barta yasa tace "Abba Ina so a nema min ABU se in karanci BSc Nursing d'in inaga ze fi tunda dama takadduna sunyi kyau" murmushi yayi yace "kin ci sa'a kuwa nan da 2weeks za'ayi jamb se kiyi registration samun admission ba wani abu bane In har kinci jamb a dage da research".
YOU ARE READING
RUWAN SAMA........
General FictionHmmm A very heart touching story.... just add it to your library and thanks me latter🥰🥰