*HUDAH Y'AR KARYA*....1-10

2.8K 157 5
                                    

☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
         🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
  🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛


_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_

         Wattpad@asykhaleel
          Facebook Group
           Asy khaleel nvls grp
               IG @asykhaleel


                  1️⃣-1️⃣0️⃣

Wata hadaddiyar motace ta paka a haraban wani shahararran hotel da ya amsa suna, (Hamdala hotel.)
    Take kallo ya koma a kan masu fita cikin  wannan motor, cikin nutsuwa Hudah ta bude murfin gaban motar tafito, yayinda classic Feedoh ta biyo bayanta sa'annan ta maida kofar ta datse hannunta rike da key car dinta,
Sannu a hankali suke takawa kai daka gansu kaga mata masu aji, ahaka suka doshi cikin hall din, har lokacin idanun jama'ar dake wajan  akansu yake, ba kamar Hudah da  tafi dauke masu hankali because yanda taci uban ado kai kayi zaton diyar  merusau ce lolz (gwamnar Kaduna kenan.)

***
         *TUNA BAYA*

HUDALLAH 'yace ga malam Yunus, dattijon kirki wanda yasan darajan dan Adam, suna zaune a (unguwan dosa Kaduna) matarsa daya sakeenah  suna kiran ta da Mamy, su biyar ne wajan iyayen su Hudallah itace babba kuma ita kadaice 'ya mace sai kannenta maza su hudu, hakan yasa take samun kulawa  akowani bangare awajan mahaifan ta, dukda mahaifinta ba wani mai karfi bane amma babu laifi suna cikin rufin asirin Allah domin,
     Gidan kansu suke zaune, sedai ba wani babban gida bane daki ukku ne sai kicin da bayi da dan filin tsakar gida, sun sami tarbiya dai-dai gwargwado kasancewar M. Yunus mutum ne mai kishin addini, dangane da karatun ya'yansa yana iya kokari a bangare biyun nan ba'a barsu a baya ba wato Arabi da boko.
   Lokacin da Hudah ta kare primary, gaba daya al'amuran suka wuyata wa Ma. Yunus, ahaka ya sama mata gurbin karatu a secondary skul don yana burin su sami ilmin zamani kodan halin rayuwa,
    Asannan ne   Mamy  taso daurama Hudah tallah, Sam Baba yaki amincewa acewarsa wannan ai cibaya ne, da dai yaga ta matsa masa akan yaa kamata surinka sana'a, ga kuma kasuwancin nasa abin sai hamdala don harya kaiga dakyar ake samun na abinci hakan yasanya yabata damar ta yiwa su Huzaifa kannan Hudah kenan, tinda su din mazane da dan sauki amma Hudah kam yayi doka ko bayan ransa idan ta daura mata tallah beyafe ba, sedai ya amince data sakata wajan koyan  sana'ar hannu, shi dinma awajan mace yar uwan ta ba shagon maza ba,
        Haka kuwa akayi Mamy tafara kasuwanci kala kala wasu ana shigowa asaya acikin gida, wasu kuma ya'yanta maza ke fita dashi, Hudah kam tuni an kaita koyon dinki. Kasancewar akusa dasu akwai wani Babban plaza na wata shahararriyar seamstress,  lokaci lokaci take  daukan yara masu koyo, sai kuma ga Mamy takai Hudah bayan ta rufe amsar  yara acewarta sai tayima wasu freedom don haka.
       Kudi masu yawa, Mamy ta biya kafin ta amshi Hudah aikuwa su Hudah an maida hankali sosai, hakan yasa karatunta ya durkushe makaranta ya zamana yau aje gobe aki zuwa,
     Ana cikin haka kwatsam M. Yunus ya tashi da amai da zawo yini guda yayi a hospital yace ga garinku nan.

*innanillahi'wainna' ilaihirrajiun*

Ku biyo *KING ASY KHALEEL* danjin ya rayuwar Hudah zai kasance.😘

*HUDAH 'YAR KARYA....*Where stories live. Discover now