☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel
4️⃣5️⃣Juye juye kawai take a saman gado sam bacci ya gagara daukan ta,
Kalaman Asy su suketa kaikawo a qwalwarta, ba abunda yafi d'aure mata kai sai cewan da Asy tayi,
Zaki daina daura atamfar kasa da 20k
Zaki daura lace harna sama da 50k
Zaki hau moto irin ta wa'inda suka isa!.
Anya kuwa?
Karfa San gayu yasa inkai kaina makasa, Anya yarinyar nan ba yar mafiya bace?
karfa ta hadani da yan shanjini in shiga uku!.
Nooo gskia Asy batayi kama da yar mafia ba, don naji tana cewa a kudin da basu taka kara sun karya ba, to kodai suna da masu siyar masu da kayan ne da sauqi?
Kai inaaa ba haka bane indai ba kayan sata suke siya ba, ina zasuga kudin siyan kayanda take lissafo min bare kuma ni, zan dai bari zuwa goben in naje naji yanda abun yake,
Da wannan tunanin bacci barawo yai nasarar sace Hudah sedai.Kiran sallan farko a kullum Hudah, don ta aje abin a ranta har mafarki seda tayi, dirowa tayi daga saman bed, take tafara harhada dad'add'un d'inkunan mutanen data aje batai ba, wasu an biyata wasu kuma ta raina kudin ne irin wanda take kunyan su, to saita amsa taita ajiya,
Aikuwa dik ta fito dasu kafin akira sallan asubahi harta yanka wasu.Yau kam ita ta tada Mamy yin sallah sa6anin da sai Mamy tasha fama da ita sannan ta tashi, wani sa'in ma sai gari yayi haske take tashi, Mamy batai mamaki ba tasan hakan nada nasaba da taso kudi, don haka takeyi da duku duku take tashi tahau keke kafin wayewan gari kuwa ta hada wasu.
Misalin shadaya na rana Hudah ta gama shirin tafiya U/rimi, tsaye take gaban Mamy tana mata magiyar ta ranta mata dubu biyar kafin anjima za a zo kar6an dinki, dayake a wayewan garin nan harta hada kala biyu ta kuma kira duk wasu datasan kayan su yana hannunta tace su kawo kudi zata hada musu.
Mamy dai cewa tayi "Allah ya tsareni d'an jarin da nake juyawa muna cin abinci shi zan tatara in baki ki watsa su, duka sai mu taru mu tsuguna, ke kuma naki dama ba amfani yake mana ba, dakin samu sedai kwashi banza kwashi hofi, to kima bar had'ani da Allah sisin kwabona bazan baki ba"Dole Hudah ta hakura ta fita dana hannunta daman 12k ne taso Mamy ta bata aran 5k sai taba Asy 15k yanda za'adan fara da tsoka, haka ta kama hanyar U/rimi batasha wuyan gane guri ba, har kofar gida mai nappep ya ajeta.
Wayarta ta fiddo a cikin jakar dake rataye a kafadarta, irin mai dogowar igiya ce wanda ake kira suwaga, d'and'asheshiyar bag ce milk colour wanda take kala daya da tsikareran takalmin dake makale a qafarta, shima me igiya ne wanda shi kansa abun kallone gashi yayi masifar dacewa da qafar , duka sunyi match da d'an siririn mayafin dake sagale a wuyata,
Jikinta kuwa tawa hadaddiyar gown ce purple colour, English wear ne ta kama jikinta dam, duk wani tudu da qwari babu abin data 6oye,
A idonta kuwa sanye take da dansiririn farin glass wanda ya qara fito da asalin kyawun face dinta, dogon hancin kawai kake gani.
Yayinda Zara zaran yatsun hannun ta ke sanye da wasu zobuna na azurfa, Wanda musamman taje museum aka qera mata masu harafin name enta,
Dayan hannun wani tsadadden agogo ne wanda saurayin ta ya siya mata, sai zube daya a yatsar ta na tsakiya Wanda shi akoda yaushe yananan a hannunta, tin ranar da suka hadu da Feedoh, daga tace zoben nan yamin kyau take Feedoh ta zare shi ta zurama Hudah shiyasa takemai laqabi da,
*TSANTSAR HALACCI* kai in takaice muku, mutum ko shine hasidin iza hasada, wajan iya kushe da hassada, lallai in har yaga Hudah a cikin wannan shiga to dolene yace ta hadu iyakar haduwa.Cikin takonta na isa da qwarewa wajan sarrafa kowace ga6ar jiki, ta isa jikin bishiyar flower wanda akaima bangon gidan su Asy ado dashi,
Jingina tadanyi jikin itaciyar sannan tayi dialling no din Asy, bugu daya ana biyu aka dauka,"Cikin muryan bacci Asy ta ambaci welcome my Hudah kin iso kenan?
Dayake Hudah ta sanar da ita gatanan a nappep."Murmushi Hudah tayi ta amsa da,
"Eh wlh gani a waje sarkin bacci har yanzu baccn ne be barki ba?Asy tadan dara gami da cewa,
"Ai *kece sila* jiya kin wahal dani dayawa, dani nan fitowa koma ki qaraso kawai!."A'a nidai futo kimin jagura idan nashigo in doshi ina?"
"Owk gani nan"
Nan dai Hudah ta tsaya tana jiran futowan ta, sai kuma ta fara kalle kalle, sosai tsarin uguwan ya burgeta, azuciyarta tace,
Gaskia G.R.A yayi yaushe zaka hada da getto erea, wanda hayaniyan yara kadai ya isa ya buwayeka, nan kuwa silent baka ganin d'an kowa awaje kai arziki da dadi, ya Allah ka azurtamu duniya wa lahira,
Ni da nake kusa da ita na amsa da ameen namesake don wlh ba wanda beson jin dadin rayuwa,
Sedai haushin rashi makaho yace ido da wari inji bahaushe.Hankalin ta tamaida ga gidajen alfarma dake unguwan kaf babu na kushewa, sedai wani ya daranma wani dama kuma Allah beraba dai-dai ba kome kake ganin kana da to wlh wani yafika, mai hakuri dai shiyake da riba awannan rayuwa. Ajerin 6angaran su Asy zamu iya cewa gidansu shine baya agurin, shidin ma babban gidane sedai daganin tsarin ginin bana zamani bane irin dai da anyi tashe yanzu kuma abun ya lafa,
To dama haka Allah ya fada mana, sauqi yana tare da qunci haka qunci yana tare da sauqi, shidai Allah yanaso dik yanda ka samu kanka to kayi godiya.
Tana tsaka da kallo nan kallo can Asy ta fito,
Tayi kusan 2mns idonta kyam akan Hudah, azuciyarta kuwa cewa tayi.
Woww gskia yarinyar nan tayi ba karya, yo wannan ai kwanan nan zatace mudin me?
Murmushi kawai Hudah take aika mata, ganin haka.
da gudu Asy ta nufota ta rungume tamkar ta dade da saninta, babu wani fargaba ko shakkun datake akan Hudah, don Asy tana da son jama a, bare kuma Hudah da take sakaran kofar samuce ta bude.Ganin irin tarban da Asy ta mata hakan yasa tasaki jikinta rai daya tabi Asy suka karasa cikin gidan..
*KING ASY KHALEEL...* ❣️

YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...