☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel5️⃣1️⃣
Tin tafiyar su Feedoh, Hudah ta zama silent sauqinta daya su Ablah suna yawan ziyartan ta dan sudan rage mata kewa, ga kuma Queen and star, sedai ta rage shige masu sosai a dalilin nunar da ita da Feedoh keyi, koda kasancewa yanzu basa kusa bata fasa aikinta ba akan Hudah kusan kullum sai sunyi waya.
*AFTER 6 MONTHS*
Akwana a tashi masu iya magana sukace mai hali baya fasa halinsa, tuni Hudah ta watsar da fadar Feedoh a halin yanzu sukanyi sati ko a waya basu gaisaba, daman Feedoh tafi kokarin kira, tinda ta koma skull itama tarage nemanta sedai lokaci lokaci.
Iyanzu kam baya da Queen and star, Hudah tana tare da ya'yan manya da kuma 'yan karya wan'inda sukace su Asy tai bani guri.
Awannan lokacin Hudah ta gama cika yanda ya kamata, ta hada duk wani abu da akeso 'ya mace ta kasance dasu, tayanda duk wani da namiji mai lafia in har zai daura idonsa akanta tofa sai yayi saurin neman tsari ga shedan, dan kuwa ko kai waye saika raya wani abu game da ita,
Haka dai rayuwa tacigaba da tafiya maganar dinki tuni Hudah ta yakicar yanzu samari suke daukar hidimanta duk abinda takeso da rawar jiki zata samu mai kawo mata, awannan lokacin ne Mamy take yawan matsa mata da maganar ta fitar da miji tayi aure, dan ta gaji da wannan layi da ake masu akofar gida, ace duk cikin masoyanta ba wanda ya mata ya takeso ayi da ita, daga karshe Mamy cewa tayi ta bata 2months ta fitar da miji in kuwa taki zata tattarata takaima can dangin ubanta dan bazata ja mata abun magana agari ba, a hakanma bata tsira ba sosai akeyi dasu a maqwafta wai ta saki yarinya ta lalace, kunsan duk abinda kake ciki idon mutane nanan akanka.
*** *** ****
A6oye Cute salheart ta shirya taron birthday party batare da sanin daya daga cikin yayunta ba, dayake sunyi mata gargani akan hakan, kasancewar gidansu mutanan qwaraine masu kokari wajan kiyaye dokokin Allah sunsha nunar da ita cewa,
Babu wani alfanu ga taron da zaka hada shi wanda babu makawa sai an sa6awa Allah, idan muka lura da yanda yan'mata da samari sukeyin yanda sukaso a wajan party musamman birthday party, sannan ga kuma yanda yan mata suke fitar da tsaraici suna karayyara qugu kowa yasan muslumci bai halatta hakan ba, duk lokacin dataje masu da bukatarta na birthday party sukance basu yarda tayi a hall ba, mafi sauki tayi farin cikinta a gida kuma banda tara gayyar banza. Hakan yasa ta shirya abinta a 6oye, datemakon saurayinta daya kama mata kasaitaccen hall na wa'inda suka isa, an kashe kudi masu tarin yawa su Asy da Hudah an gama tanadin fitinannun rigunan da za'a farfasa da ita awannan taro, ita uwar gaiyar kuwa wuhuhuuu abun ba'a magana musamman aka fita waje dan nemo rigar da zasa saka a wannan rana, ranar birthday tinsafe Asy da sauran friends keta kaikawo wajan ganin komai yatafi yanda suka tsara, misalin hudu na yammaci suka aje lokaci, dake sunata gargadin babu african time duk girman gurin nan ni danaje 4:15 bansamu shiga ba hall ya cika makil da haddadun yan'mata da samari isoyar cute da jaruminta kadai ake jira abunda basu sani ba shine...._Shine mai😳? Ina sauraran ra'ayoyinku kafin mu shiga next page_
*KING ASY KHALEEL...*✨

YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...