HUDAH Y'AR KARYA..63

752 70 4
                                    

☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻‍♀️)_*

     🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
     _*Wattpad@asykhaleel _*
        *_IG@asykhaleel_*

                  6️⃣3️⃣

Dole ya juya yana tattara kayan daya jibgo mata, haka ya fito yabar tarin kayan ciye ciyen daya tanada masu a hotel babu daya da suka sami damarci,

Sosai ya kashe kudi  wajan hada su duk wani  abinda yasan Hudah tafiso sai daya siya mata har dama wa'inda batasan su ba,

   Kwance ya tadda ita a bayan motar, ba bata lkc ya shiga ya tada motar suka dau hanya,
Sosai Hudah ke cike da fargaban abinda zata tarar a gida tasan tabbas sai Mamy ta tuhumeta inda taje,

Shi dai Abdallah sai aikin lallashinta yake, azuciyarsa yana kara tuni yanayin daya shiga lkcn da yake tare da Hudah, dukda yana tunanin  zai sameta a cikakkiyar budurwa, hakan kuwa ya kasance don harma ta zarce tunaninsa, don ko acikin yan matan Hudah daban take, hakuri yaketa bata har suka shiga layinsu, Hudah dai tana jinsa ko kallo be isheta ba,  numfashi kawai take saukewa alamar ta wahala, yanayin parking ta bude moton ta fito tayi cikin gida,

   Abdallah yana kiranta ta amshi kayan tayi kamar bada ita yake yi ba.

    Hamdala Hudah tayi lkcn data waiga taga qannen tane kadai a gidan, hakan na nufin Mamy bata dawo ba kenan.

  Huzaifah ne ya taso yana mata masifar danme an barta agida zata fice yawonta tabar musu gida abude, Hudah bata ko bi takansa ba ta shige daki dan yau ba tashi take ba.

Tana shiga daki bata zauna ba, saida ta jona ruwa  nan da nan ruwan ya tausa ta juye a baho tayi bandaki dan tadan gasa jikinta ko zataji saukin radadin da takeji a kasanta,

Sosai taji dadin zuwan zafin nan agurguje tasake sarkake jikin ta daganan ta dauro alwalla ta dawo daki danta gabatar da sallah.

Sai wajan goma saura Mamy ta shigo gida sakamakon biyawa gidan kawarta da tayi, nan hira yai masu dadi har batasan dare yayi haka ba,

Mafi yawan hirar tattaunawa  sukeyi a gameda shirye shiryen bikin Hudah, acewansu lkc baya jira sedai a jira shi.

Kusan duka yaran gidan ta iske sunyi bacci Huzaifah kadai ta riska  yana karanta Qur'an.    

Bayan Mamy ta kimtsa komai ta leka dakin Hudah nan ta hangeta kwance akan sallaya tana bacci, mamaki ne yasa Mamy shigowa cikin dakin tai saurin taba jikin Hudah,
Nan taji jikinta ya dauki zafi,

"Ai daman nasan a rina" Mamy ta fada a bayyane, dan tasan hakanan banza Hudah bata bacci da wuri haka, har fada Mamy take mata akan hakan, dan sai takai shabiyun dare tana latse latse a waya,

   Tashin ta Mamy tayi ta tambayeta meyake damun ta bayan ta barta lfy?

"Kaina yake mun ciwo ai dama seda nace miki banasan hayaki kika hadani da girkin ice, cikin shagwa6a Hudah tai mgnr. Mamy ta kada kai tana jinjina sangarta irinta Hudah, nan dai ta tambayeta.

"Kinsha magani?"
Hudah ta daga mata kai alamar eh,

"Toh Allah ya baki lfy tashi ki koma saman gado" Mamy na kaiwa nan tafice tare da janyo mata kofan,
Duk sai taji ranta ya baci daganin Hudah ba lfy.
 

    Bayan sati biyu da faruwan haka Hudah ta gaji da fushinta ta hakura sun cigaba da gudanar da soyayyan su kamar da,

A6angaran Abdallah burinsa ya gama cika yanzu abu biyu suka rage masa,
Nafarko dai yana matukar bukatar ya sake kasancewa da Hudah dan akullum sai yayi mafarki da ita,

Sosai sha'awarta ya dawo mishi sabo yanzu har yafi shan wuya fiye da kafin ya dandani zumarta, gashi ya rasa tayanda zeyi ya sake tinkarar ta dan ya lura tsoransa takeji.
Na biyun kuma ido bude hanyar guduwa yake nema  dan dama kaf a danginsa babu wanda yasan da wani maganar aure akansa,

  Musamman yasa aka nemo mai dattijan banza ya biyasu kudi masu yawa akan suje su nema masa auren Hudah a matsayin sune iyayen shi, don haka ya dinka masu manyan kaya sukayo shigan mutanen kirki sannan yasa aka kawo su a qatuwar moto ta alfarma. Kai Abdallah ya gwane wajan iya yaudarar yan mata,
   

     Bikin Muhibbah ne ya taso, duk da kasancewa yanzu  neman janye jiki  Abdallah yake yi, hakan bai hanashi kashe mata kudi kamar yanda yasaba mata ba, duk abinda ta tambayeshi yana bata, ahaka har tagama shirya komai na shagalin biki.

  Muhibbah kawar Hudah ce ta kusa a yanar gizo,
Yar wani babban dan kasuwa ne  a katsina, ta taso cikin gata da jin dadi domin tana ji da kanta ba kadan ba,
Shiyasa tasu tazo daya da Hudah har suka zama aminan juna.

Abangaran Mamy  karya aka gilla mata Hudah ta kwantar da murya tana cewa.
    "Mamy Abdallah ne yace in nemi izininki  yanaso in rakashi gaisheda kanwar Baban shi a katsina aiyi mata aiki ne, kinga daga nan sai inje wajan anti Sadeeya mu sada zumunta, 

Anti Sadeeya wata kanwar Mamy ce amma na yan uwa, da Mamy taso ta hana tafiyan daga baya dai ta barta tinda taji cewa da mijin da zata aura ne,

Mamy ta hakura akan kwana biyu za ayi a dawo aka aje lkc sati biyu masu zuwa......

*HUDAH 'YAR KARYA....*Donde viven las historias. Descúbrelo ahora