HUDAH Y'AR KARYA..74

764 93 10
                                    

☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻‍♀️)_*

     🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
     _*Wattpad@asykhaleel _*
        *_IG@asykhaleel_*

                  7️⃣4️⃣

Tashi Huzaifa yayi yaje ya rungume Baban khaleefah yana masa godiya harda hawayen farin ciki.

Mamy kam kuka take tana kwarara masa albarka, tana cewa,

"Hudah ki yafe mani komai ya sameki ni naja miki dana rabaki da gidan ubanki"

"Babu komai Mamy Allah ne ya jarabceni da hakan,

Kuma nice ya kamata in nemi yafiyar ki na musguna miki danayi,"

"Ai ni Hudah tuni nadade da yafe miki daman burina na karshe kenan Allah ya bayyana min ke ko yanzu na mutu alhmdllh,
Mamy ta daura da cewa,

"Ashe 6arin cikin nan kika yi, kai da ace wannan yaro yazo duniya lallai da yaga gata dan kakar nan tasa ta gwallafa rai akan shi kullum addu'an ta Allah yasa karki zubda cikin.

Hudah ta dubi mahaifiyar ta tace,

"Mamy wani gata ga d'an da baida  uba?"

Nanne Mamy ke labarta mata,
Kwanan ta biyu da barin gida,
Mahaifiyar Abdallah ta binciko gidan,

Da kukanta tazo tana ba Mamy hkr tare da yi mata alkawari tace,

"In dai nice mahaifiyar Abdallah in har nonona Abdallah  yasha ya rayu, sannan da sauran numfashina, nayi muku alkawarin insha Allah ranar da yarinyan nan ta haife cikin, aranar za'a daura aurenta da Abdallah.

Dan Allah kuyi hkr karkuce zaku zubar da cikin nan akwai laifi mai girma awajan ubangiji"

Mamy ta share hawaye tare da cewa,

"Nan nayi mata bayanin danyan hukuncin dana zartar miki,

Hajiya ta dafe kai tana takaicin kurarki da nayi.

Tin daga lkcn bata sati biyu batazo gurina ba wai taji ko an sami lbrn inda kike,

Duk idan zatazo saita riko mana abin arziki tin  bana karba harma na hkr nafara amsa.

Ahalin yanzu Abdallah yana nan ba lfy, sun sami hadarin jirgin sama ahanyarsu ta zuwa shakatawa  shida ubansa, acewan uban yaga mahaifiyarsa ba kaunarsa take ba gara subar mata gidan har sai ta nemesu takanta.

Take  uban nasa ya mutu, ance part part ya kasu wasu ga6o6in ma ba a gani ba,
Shiko Abdallah yananan daransa anata wahala dashi duk ya karairaye,  da ko zama baya iyayi komai zeyi sedai yayishi akwance,

Yanzu ne naji uwan  tana cewa, an fara jingina shi ya zauna ke abun fa babu kyau yanda ake fada duk ya shagide.

Rayuwa kenan kadanma yagani indai duniya ce,
Abinda Hudah ta fada kenan,
Takawar da zancen da cewa,

"Mamy ina lbrn kawata Feedoh?"

Mamy tace  "Feedoh tana nan lfy lau kullum cikin kukan rashinki take,

Kinsan lkcn da abun ya faru,
Tashin hankali ya mantar dani sanar dasu halin da muke ciki,
Bayan tafiyanki ne Hajiya ta kirani mugaisa nanne taji muryata wani iri ta tambayi ko lfy?

Ananne nake sanar da ita halin da ake ciki, aifa bakaramin tashin hankali suka shiga ba,
Hatta Alhj saida ya kirani cikin bacinrai,

Yana cewa,
"Meya hana in sanar dasu, aida  yazo ya tafi dake da bebarki kin shiga duniya ba"

*HUDAH 'YAR KARYA....*Where stories live. Discover now