☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel
5️⃣2️⃣A can gidan uncle Haiydar an samu wanda yaje har gida ya sanar da shi danyen aikin da cute ta shuka,
Dafarko yaso ya karyata, duk da yasan zata iya aikatawa.
Ganin qwaurafi bai kar6u ba, nan take wanda yakai masa rahoton ya fidda invitation card wanda sukayi na gayyatan friends,Jiki asayaye ya Haiydar yasa hannu ya kar6a yana girgiza kai lokaci daya ya birkice nan da nan idanunsa suka koma kamar garwashin wuta yayinda zuciyarsa ke tafarfasa dalilin ganin sunan dake jikin card din tare da cikakken address na hotel din da zasu gudanar da taron,
Iska ya busar ya sake kai dubansa ga card din, kallo yake yana kada kai azuciya yake kara karanto abinda idanunsa ke gane masa.
Ina gayyatar friends maza da mata don tayani farin cikin zagayowar ranar haihuwata. Address, seventeen hotel, no 6 tafawa balewa way, u/rimi GRA Kaduna. Time 4:00pm, gargadi bamu yarda da African tym ba, Allah yabaku ikon zuwa mungode..
Dasauri ya kalli agogan dake daure a tsintsiyar hannunsa yaga 2:30 zabura yayi ya mike kamar wanda wutar NEPA taja, a razane bakonsa ya fice daga palon saboda tsananin tsorata da yayi,
Uncle Haiydar baiyi wata wata ba ya afka mota ikon Allah shi kadai ya isar dashi gidan Momin su lfy, dan kuwa tukin kawai yake amma hankalinsa baya a jikinsa fatansa daya ya iske cute a gida,
Fitowanta daga wanka kenan sauri sauri tadan shafa mayukanta ta zira doguwar riga na atamfa, ta matsu tabar gida tin safe takejin gabanta na fadi, tana ji ajikinta kamar asirinta zai tonu.
"waiiii da kuwa na banu dasu yaya, inaga kasheni ne kadai ya Haiydar ba zeyi ba wannan tunanin shiya daddabi zuciyarta, sai tayi tunanin koma dai ta fasa ne?
Sai wata zuciyar tasage tinzirata da cewa,
Haba dai ai wlh da kinyi bala'in kwafsawa, toma ya zakiyi da mutanen da kika gayyato?
Karfa ki manta kin fada a whatsapp, fb, dasu instagram, babu inda ba'a sani ba mutane da dama sunyi shirin halartan taron kodan susha kallo.
"kaii ina bazan iya wannan abun kunyar ba garama ayi inyaso ko sunji daga baya nasan maganar dukane zafin zai wuce ya fiye min naji kunya.
Da wannan shawarar tayi naam, dan haka agurguje tagama shirin tafiya wajan da za ayi mata makeup, tuni daman ita suke jira harsun matsa mata da kira gudun kadda a makara kasancewar kwalliyar da za a tsara mata zai dauki lkc sosai, tinda safe ta tsarawa Momi karyan zata raka anty Haifah bikin kawarta Hancy Momi bata kawo komai aranta kasancewar tasan da maganar bikin, ta amince dataje amma sai data kira Haifah taji lallai itace ta bukaci taimata rakiyar..
Fitowa ta kenan tana shirin taje tayi sallama da Momi anan tayi kaci6ur da ya Haiydar, ganin irin kallon da yake mata jikinta yahau 6ari lokaci daya taji fitsari na shirin kufce mata, cikin matsanancin tsawa ya jeho mata tambayar...
"Zaki tafi wajan birthday party da kika shirya ko?
Bude baki tayi da nufin bashi amsa, taku daya yayi ya cafkota tare da sakar mata wani wawan duka a baki, wayyo abinka da jikin hutu nan da nan jini ya fara ambaliya,
Ihun da Momi taji yasata fitowa a rude, ganin haka yasa ya Haiydar yai saurin janta ya shige dakinta ya datse kofar,
Kururuwa su anty Humairah da Momi suke amma yaya yaki budewa saida yaga nunfashinta na neman daukewa saboda tsananin azaba sa'annan ya fito yana huci kamar wani zaki.
Kan Humairah yayo wacce musamman ya biya gidanta ya taho da ita acewarsa dasaninta ake komai itace shugaba, aifa tana ganinsa ta antaya aguje tashige dakin Momi dasauri ta datse kofa.
Tinda yafara dukan cute, asace Hameeda takira aunty Haifah ta sanar da ita ga halin da ake ciki,
wayyo zo kuga saurin sa6a goyo wajan Haifah tasan ba makawa sai yasa an taho da ita tinda har ya dauko anty Humairah, bata tsaya sawa ba, a dari ta fice tabar gidanta.😅
_Kindly Vote n Cmmnt pls_
*KING ASY KHALEEL...*✨

YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...